HAUSA NOVELKADDARA Complete Hausa Novel

KADDARA Complete Hausa Novel

Cikin satin da bai wuce biyu ba Maman suka fara shirye-shiryen fita ƙasar waje bayan ta sa malam Nur ya je Bank ya ciri ke duka kuɗin account ɗin da suka yi saura dan tun auren Balkis aka bata gadonta cikin su aka yi mata sayayya sauran ta baiwa mijinta kasancewar shi tallaka.

Cike da mamaki malam Nur ke kallon Maman yace “yanzu Maman saboda kawai a buɗe ma Laila ido zaki sa na kwashike kuɗin account duka?”zaro ido Sappa tayi jin wani za’a yi ma Laila magani a take wani kishi da baƙin ciki ya turnuƙeta ta shiga tari.
“Eh tabbas kuma babu wanda isa ya hana dan haka ka fara shiri dan tare za mu tafi”wasu hawayen farin ciki ne suka shiga ambaliya a fuskar Nazifa ita sam ba ta zaci gaskiya Laila ke faɗa mata ba lokacin da ta shaida mata Maman tayi mata alƙawarin kaita asibitin waje.
Jasmine ce ta shiga tsale tana cewa “waiiii antyna za ta buɗe ido nima Maman sai a sayo min hannu”dariya Maman tayi tana mai jawo ta zuwa jikinta.

Tsananin baƙin ciki da hassada ya haifar ma da Sappa ciwon mara,a ƙarshe dai cikin jikinta ya fara zuba.
Tun da safe ta tafi asibiti,su na nan zaune jiran Dr ɗin abun ka da taron mata nan fa suka shiga hira kowa na faɗin abinda ke damun shi har aka zo kan Sappa wacce ke basu labarin za’a kashe maƙudan kuɗi saboda gyaran idon ɗiyar kishiyar ta,ai kam suka shiga zuga ta kar ta yarda.Baki ta ja tayi ƙyaci tace “ina fah zan yarda ina nan ina tunanin matakin da zan ɗauka,ki na ga fah tashin hankalin da ni ke ciki ne ya haifar min da zubar jini”wata ɗaya daga cikin wadda tafi nuna damuwa akan abun tace “nima ciki ya taɓa min zuba amman ina shan wani maganin gargajiya ya ɗauke har sai da na haife ɗan cikina”Sappa tace “a ina kika same shi ni inda ki na da shi da kin bani dan dama ba kasau ni ke son namiji ya duba ni ba”
“No babu matsala in ki na so sai ki tashi mu tafi na kai ki har gun da ake saidawa” “ok tashi mu tafi”cewar Sappa.
Adaidaita suka samu suka nufi bakin likita ƙarama,wani gayen matar ta saye ta baiwa Sappa lokacin da suka ƙara tarar adaidaita da za ta mayar da su.”Ka fara sauketa sai na ga gidan ki,in ya so daga baya sai na kawo maki ziyara” “babu damuwa Maman Latif”cewar Sappa.
Hira suka tayi har aka kawo Sappa ƙofar gida ta biya duka kuɗin harda na Maman Latif,”nagode sosai Allah bar zumunci ki ban number dan in naje gida na kira naji maganin in ya so jikin ki” Sappa tace “ba damuwa”ta zaro number ta da ke jikin wata ƴar takarda ta baiwa Maman Latif.

Da zuwanta ta tafasa ganyen maganin ta tace ta fara sha,tun Sappa na jiran cikin ya bar zuba har ta fidda rai.
Shirin barci tayi ta tana tunanin ƙila maganin bai so jininta ba ne.
Sappa ba ta jima da kwanciya ba taji kamar ana dirowa cikin gidan,ji kake dif-dif-dif ƙatti na dirowa.Ta window ta leƙa nan ta ga zabga-zabga mazaje fiye da goma ko wane fuskar shi rufe da masque,ga manyan bindigogi a hannun su.Da sauri Sappa ta saki labulen tana jin fitsari da ragowa cikin sun fara zuba.

Part ɗin Maman suka nufa,ba su wani ɗauki lokaci ba suka ɓalle ƙofar.Duka suka shigo aka bar biyu a bakin ƙofa,kamar a mafarki Maman ta ga mutane da baƙaken kaya sun yi ma gadonta ƙawanya.Wani gigitacen ihu ta ƙurma wanda ya sauka har cikin kunnen malam Nur da ke tsaye kan sallaya yana sallah.Ƙirjin shi ne ya buga da sauri-sauri ya sallamce ya nufi ƙofa.
“Ina kuɗin da kika ciro daga Bank?kar kiyi garma dan zan iya harbe ki”ɗaya daga ciki ya faɗa yana bugawa Maman kan bindiga ga hanci a take jini ya ɓarƙe,ta dafe wurin tana kuka wani ya kai mata naushi da ƙafa yace “ba tambayar ki ba a ke?”azabar da Maman taji ne yasa ta nuna masu drower,ba ɓata lokaci wani ya buɗe sai ga ƙatuwar bag.Zip ɗin ya buɗe ya ga ƴan goma-goma rasss kwance ciki da hannu yayi masu alama suka fice daga gidan…….

Please share

 

Jikar Rabo ce????
[31/07 à 10:13] Matar Sadauki????: *LE DESTIN…*????
(ƘADDARA)

Story
and
Writtenby
“`CHAMSIYA LAOUALI RABO“`✍????

*RUBUCIYAR*
ƁOYAYYEN SIRRI
MAHAUKACIN SO
ƘAWAR MOMYNA
SADAM

Dedicated to *Amana Writers Associations*????????

☀️ *FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS*☀️

____________________________________________________________

“`MA’ABOTAN SAURAREN LITATTAFAIN HAUSA ZAKU IYA SAURAREN DADAƊEN LITTATTAFAI TA WANNAN SHENEL ƊIN“`????????

*SUBSCRIBE*
_DUNIYAR LITTAFAN HAUSA TV_

https://www.youtube.com/channel/UCcAjVQ74qod9_dL0e_AqkiQ

Page 25-26

A gudane malam Nur ya nufi part ɗin Maman,tsakiyar gado ya hango ta dafe da hanci jini na zuba sai kuka ta ke kamar wata ƴar yarinya.”Maman…”ya faɗa in cool voice ɗagowa tayi ta kalle shi sai kuma ta ƙara fashewa da kuka tace “shikenan sun ƙwace kuɗin maadina ba zai cika ba”wani tsalle malam Nur yayi yace “wane kuɗin?” “Uwan da ka ɗauko Bank”wani irin bugawa ƙirjin malam Nur yayi a haka ya daure ya taimakawa Maman jinin ya tsaya.
Tagumi ya rabka ya na kallon mahaifiyar shi wacce ta fita hankalinta lokaci guda sai surutu ta ke,maganin kwana da na ɗauke zafin ciwo ya ɓalla ya bata ba jimawa tayi tsit ta na sauke ajiyar zuciya.Falo malam Nur kwanta bayan ya rufe porte,duniyar tunani ya tsunduma “tabbas Allah ke gwada min ishara da ace na yarda da *ƘADDARA* da ƙila wannan ba ta faru ba,da yanzu kuɗina su na cikin account.
Astagfirullah Allah na tuba ka yafe min, Nuradeen ka zama butulu duk da ni’imar da Allah yayi maka ba ka gani ba sai jarabtar ka da yayi?miyasa ma na aikata haka alhalin na san Allah shi ke yin yadda ya so ga bawan shi?”malam Nur ke wannan maganar zucin kafin ya miƙe ya koma part ɗin shi.

Wata alwalar ya kuma yi ya shimfiɗa tafi yana mai cigaba da Sallah da ya fara.Ya na tsaka da karatu cikin Suratul Ibrahim sai ya tsaya daidai Aya ta biyar yana ta nanata ta,daga bayan shi ya tsinkayo murya Laila na cewa *WA’IZ TA’AZHANA RABUKUL LA’IN SHAKARTUM LA’AZI DANNAKUM,WALA’IN KAFARTUM INNA AZABI LASHADID* cikin kuka malam Nur ya maimata kamar yadda tace kamin ya cigaba da sauran karatun.Sai da ya sallamce sannan ya juyo ya kalli inda take zauna “Lailaaa…”ya faɗa cikin sanyin murya “na’am Abih”ta faɗa tana takawa zuwa wajen shi dan a yadda taji ya kira sunanta ba ta tunanin cewa masifa zai yi mata kamar kullum.
Face ɗin shi ta zauna tana laluben hannun shi,riƙe ta yayi yace “miyasa kika tayar da ni a Aya ta shidda?ko a tunanin ki ɓacewa ce nayi?”cikin sanyin murya tace “eh naji sai maimaita Aya guda kake alamun ka laƙe ne shine na faɗa ma ta gaba”murmushi da hawaye ne suka zubowa malam Nur lokaci guda “ba laƙewa ba ne nayi ku san kullum ma ina karanta Surat,kawai tsoro da kunyar ubangijina ce naji”duk da bata gani bai hanata hango tashin hankali da Abbanta ke ciki ba “tsoron mi Abih?”gaɓar ta ya ɗago yace ” ko kin san abinda Aya ta shidda ta cikin Suratul Ibrahim ta ke cewa?”kai ta girgiza ma shi alamun ba ta sani ba,sunkuyar da kai malam Nur yayi yace “Ubangiji ta’alah ne ya ke cewa “`Azabar mi Allah zai yi maku in ya baku ni’ima kuka gode ma shi? IN KUN GODE ZAN ƘARA MA KU,AMMAN IN KUKA BUTULCE MIN LALLE AZABATA MAI RAƊAƊI CE“`” da sauri ta jimƙe hannun Abih ta ce “ya kai Abihna mai zuciyar imani ba zan hanaka kuka ba dan alamu ne na tsarkakun bayi masu raunin zuciya a duk lokacin da suka ji Ayar Ubangijin su mai kaifi,su kan jin tsoro ne dan kauce ma fushin Ubangijin su.Abih kayi shiru ya isa haka ka gode ma Allah da ya baka zuciyar imani kake kiyaye haƙoƙin shi da na jama’a ba tare da ka cutar da kowa ba”tunda ta fara magana malam Nur ke kallon ta yana jin bugun zuciyar na dokawa da ƙarfi,wani irin cirota yayi ya rungume cikin kuka yace “astagfirullah Allah na tuba ka yi min kyautar Lu’ulu’u amman na banzatar,My Laila ki yafe min ko zan samu salamar ruhi na cutar da ke nayi watsi da ke a lokacin da kike buƙata na”ajiyar zuciya farin ciki Laila ta shiga saukewa tana jin son Abih har cikin ɓargon zuciyarta “Ni ai dama ban riƙe ka a zuci ba,na yafe ma Abih Allah kare ka da duk wani abun cutarwa” “Amen “Nazifa da ke bakin ƙofa ta furta da ɗan ƙarfi ta yadda har sai da suka ji.Wata sallah malam Nur ya ƙara jan su,su ka yiwa Allah godiya tare da neman tsari.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button