HAUSA NOVELKADDARA Complete Hausa Novel

KADDARA Complete Hausa Novel

Inna na shiga ta tarar da Ɗalhat sai faman faɗa ya ke da wata nurs akan tace doli sai ya tafi ya karɓo takarda shi kuma yace ta dubata kafin ya dawo shine tace taƙi tayi ɗin.
Cikin alamun a tausaya masu Inna tace “ƴata ki taimaka ki duba ta dan haihuwar da iyayen ki suka yi maki,mai rubuta cahier ɗin kamar na ga ƙofar shi a rufe”a zafafe nurs ɗin tace “sai ku jira har ya dawo ko kuma ku canza likit….”Bashir ne yayi saurin katse ta wanda shi ma infirmier ne yace “haba Rakiya ba ki ganin halin da take ciki ne?kuma dan tsufan wannan ai kin taimaka”ya ƙarashe maganai yana mai juyawa inda Ɗalhat ke tsaye yace “mi ke damun ta?”cike da jin daɗin hallacin da yayi masu ya shiga yi mashi bayani “eh to duk in an yi ruwa ne ko kuma lokacin sanyi sai jikinta ya rinƙa ciwo tana jin sanyi”kai Bashir ke ɗagawa kafin ya ɗibi jininta ya kai Laboratoire cikin ɗan lokaci ya dawo da fara takarda,sai da ya naɗe lemar (parapluie) sannan yayi mata allura.

Inna da Ɗalhat na gefe sai godiya suke zuba shi, murmushi kawai Bashir yayi yace “ba komi ai yiwa kai ne”.
Barci mai nauyi ta samu sai fitar da gumu take tana sauke ajiyar zuciya,gefen gado Inna ta zauna yayinda Ɗalhat ya bi bayan Bashir dan karɓo magani.

Sai bayan sallah isha’i suka dawo gida,cike da mamaki Jamila ƙaunarta ke kallonta ganin ta warke lokaci guda cikin kasa ɓoye mamakinta tace “anty kamar ba ke ce aka fita da ke a duƙunƙune ba ya jikin naki ?”
“Da sauƙi na ma warke yunwa nike ji mi kika dafa?”
“Sirundu shinkafa”ta bata amsa ta na mai ɗaukar kwano ta zubo mata,ba wani ci tayi sosai ba ta tashi tayi alwala da ruwan zafi ta gabatar da sallah da ake binta.

Lamo tayi kan sallaya fuskar malam Nur nayi mata gizo, murmushi tayi tuna lokacin da ya lura da ba cikin hayyacinta take ba duk sai ya ruɗe “sai yaushe zaka furta ne?”ba ta san a bayyane tayi maganar ba sai jin Jamila tace “mi za’a furta?”yi tayi kamar ba ta ji ta ba ta tashi ta haye katifar da suke kwana ta cigaba da tunanin malam Nur har barci ya ɗauke ta.

 

Ƙarfe bakwai cicif a makaranta tayi ma malam Nur,tun kafin ya ƙaraso ajin ya ke jin sautin muryar ta sai karatu take cikin nutsuwa tare da ba ko wane harafi haƙin shi.
Bakin window ya tsaya yana ƙare mata kallo,sanye take da hijab da sket na uniforme ɗin makaranta hannunta riƙe da al’ƙur’ani amman ta rufe shi alamu harda ce take.Idonta a lumshe suke yayinda ɗan ƙaramin bakinta wanda ya sha janbaki sai motsawa yake yana fitar da dadaɗan amo na muryar ta.
Ido biyu suka yi a tare zukatansu su ka buga dam,cikin i’ina tace “as..salamu aleyka yaa mu’alim”sai da ya ƙarasa shigowa cikin ajin sannan ya amsa sallama yana mai tambayar ta “ba ki jin tsoro ne kullum ke kike fara zuwa makaranta ina ɗayar take?”wani daɗi Nazifa taji kamin tace “ta na gida sai zuwa ƙarfe takwas take zowa”
“Ke kuma ba ki iya jiranta ko?”ɗan ɗagowa tayi ta kalle shi tace “um..ai saboda nayi harda ne ni ke zowa da wuri”jinjina kai yayi ya amshi ƙur’anin hannunta ya fara yi mata questions,sai ya jawo Aya yace ta cigaba ko kuma ya tambaye ta cikin wace sura ce ita kuma ta na ba shi amsa.Sosai duka zukatan biyu su ke jin daɗin wannan kusancin a haka har mutane suka fara taruwa sai dai babu wanda ya shigo aji sai leƙen su da ake wasu na gulmar dama soyayya suke.

Lokacin shiga aji yayi kowa ya shiga,nan Nazifa ta ji ta a takure ganin rabin ɗalibain ajin sai harararta ake yawancin su duk masu son malam Nur ne.

“Ke miye haka?dan Allah ki saki jikin ki duk kin wani takure kawai dan surutun mutane ba komi ba ne ke cin su sai baƙin cikin ganin kin samu abinda suke so shekara da shekaru”cewar Samira murmushi kawai Nazifa tayi ba tare da tace komi ba domin tun ba yau ba tayi remarque ɗin suna son junan su ba tare da su sun sani ba,tun ba ta yarda da zancen Samira har ta yarda da lalle tana son Malam Nur.

Duk karatun da ake masu na yau sam ba ta fahimta ba dan rabin hankalinta yana can duniyar tunani,ƴar ƙarar rawar da aka kaɗa alamun lokacin récréation yayi ne yasa ɗaliban fara fita dan karyawa,”Malama ki tashi mu tafi ko yau ba ki cin komi?”ta tsinkayo murya Samira cikin masifa, murmushin da ya zame mata jiki tayi tana mai miƙewa har sun kai bakin ƙofa suka ji malam Nur yace “Naziiii”cak ta tsaya zuciyarta ta shiga lugude kallon Samira tayi da ido tayi mata alama da ta tafi tare da ɗaga mata gira kafin take ficewa.

A hankali ta dawo kamar wacce ƙwai ya fashe ma a ciki har ta zo gaban bureau ɗin shi inda ya ke zaune a kujera ya ɗora hannuwan shi akan table.

“Ga ni mu’alim”ta faɗa kamar za tayi kuka,bai ce mata komi ba sai ma ƙoƙarin ciro wani littafi ya ke.
Turo baki tayi gaba tana jin haushin shanyata da yayi har ta fara tunanin ko dai ba kiranta ba ne yayi sai kuma taji yana cewa “ya kamata ki ƙara da karatun wasu littattafai dan ilimi yawa ne da shi ga uwannan kije da su gida kiyi nazari gobe za mu fara su”amsa tayi ta juya za ta tafi yace “am…ban gama ba”tsayawa tayi jin bai ce komi yasa ta ɗago kanta karaf suka haɗa ido wani irin masse mai game da shock suka ji a tare da sauri ta mayar da kanta ƙasa.Murmushi yayi yace “ki na iya tafiya”kamar mai jira ta juya da sauri ta fara tafiya kamar wadda aka yi ma dabaibayi……….

*Da sannu zaku fahimta wannan duk shimfiɗa ce domin tushen labarin ne*

Please share

More comments
More typing

 

Jikar Rabo ce????
[20/07 à 17:03] Matar Sadauki????: *LE DESTIN…*????
(ƘADDARA)

True Life Story

Story
and
Written by
“`Mrs Sadauki“`✍????

*MARUBUCIYAR:*
ƁOYAYYEN SIRRI
MAHAUKACIN SO
ƘAWAR MOMYNA
SADAM

Dedicated to *AMANA WRITERS ASSOCIATIONS*????????

BISMILLAHI RAHMANI RAHIM.

Page 3-4

Tun daga nesa Samira ke ƙare mata kallo har ta ƙaraso,dungure mata kai tayi tace “ƴar sa ido kallo miye kike min?”dariya tayi tace “to Naziiii ni kam mi zan kalla a nan,kawai na ga yau duk a takure kike kamar wata kaza da ƙwai ya fashe ma a ciki haka kike tafiya tsaya ki ga na gwada maku ma ki yadda kike tafiya”Samira ta faɗa tana kwaikwayon tafiyar Nazifa “ke dai kika sani uwar sa ido”
“Babu wani sa ido sai gaskiya,wai miye yace mi ki?”ajiyar zuciya ta sauke ta gwada mata litattafain da ya bata “na miye ?”
“Karatu za mu rinƙa yi”jan baki Samira tayi tace “sabon kiciyi…”wani dundu Nazifa ta kai mata a baya cikin jin haushin furucin tace “Noori ɗin ne kike ce ma kiciyi?”amsa ta bata da “eh ɗin in ba kiciyi ba miye na wani kame-kame ai sai ya fito fili yace maki ya na son ki ba ya fake da koyar da ke ba”kamar daga sama suka tsinkayo murya malam Nur yana cewa “in kun gama gulma ta sai ku shiga aji”da mugun tsoro duk suka juyo sai dai tuni ya wuce sai bayan shi suka hango.
Sai da Nazifa ta sayi taiba suka wuce aji,a gagauce ta shanye taibai ta ɗauki ruwa tana sha ita kuma Samira sai aukin kallonta ta ke “lafiya ko na sauya maki ne?”Nazifa ta tambaya “a’a ko ɗaya kawai na ga ki na shirin zautar da malamin mu ne,har fah zai shigo ko da ya ga ki na cin abinci ya koma na san jira ya ke har ki ma”waro ido Nazifa tayi sai kuma ta ƙyale ganin malam Jabeer ya shigo aji da alamu kuma shi zai masu karatu.

Rubutu ya fara a tableau sannan ya juyo ya fara tambayoyin akan karatun da ya gabata su kuma ɗaliban na ba shi amsa,cike da ƙwarewa ya shiga yi masu bayani muhimmancin amana da gaskiya suna tsaka da karatu malam Nur ya shigo ya zauna shi ma ya na sauraren jawabin malam Jabeer.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button