KADDARA Complete Hausa Novel

Washegari bayan su Maman sun dawo daga asibiti nan fah mutane suka fara shigowa jaje,Laila na jikin Maman kamar wata mage Nazifa na daga gefe rungume da Jasmine yayinda malam Nur ya tafi kai Sappa asibiti.
Duk binciken da ƴan sanda suka yi sun kasa gane komi,an fi alaƙanta abun da ƴan daba ne suka biyo malam Nur lokacin da ya ciro kuɗin.Haka aka yi ta yin maganai kafin daga bisani abun ya lafa suka rungumi *ƘADDARA*
Tun bayan da abun ya faru Maman ta ɗauki sarkawa duniya ta ɗorawa kanta,kullum cikin tunani da zubda hawaye take wannan ya jawo mata muguwar tension.Ta na fitowa daga wanka ta faɗi,da taimakon matan shi suka ciciɓi Maman zuwa asibiti.Tsawon lokaci Dr ya fito da sauri malam Nur ya tare shi ya na cewa “ya ake ciki likita?”ɗan jim yayi kafin yace “toh da sauƙi alhamdullah ta farfaɗo sai dai ta samu shanyewa ɓare guda,hannu da ƙafa sun shanye”
“Innalillahi wa’inna ileyhi raji’un”ita kaɗai malam Nur ke maimaitawa yayinda matan shi suka fashe da kuka babu ma kamar Sappa.
Cikin ɗakin da aka kwantar da ita suka shiga,barci take amman kallo guda za kayi mata ka gane hallitarta ta canza yadda bakin ya ɗan juye ƙafa da hannun kuma suka yi kumburi.Su na nan zaune cikin jimami sai ga Balkis ita da yaren da aka kai mata ɗazu da safe,kuka ta fashe ta nufi Maman ta faɗa jikin ta.
Twins kallon Maman su ke nan suka fara dariya yayinda Jasmine ta kama hannun Laila zuwa wurin Maman wacce ta buɗe ido.
Hawaye suka ziraro kan kumcinta tace “shikenan zan tafi ba tare da na ga buɗewar idon ki ba Laila,ina takaicin haka”da sauri Laila ta lalubo hannunta jin murya kamar ta Maman amman ita wannan a rarrabe take fita irin ta ƴan tension “Maman..ina ne zaki tafi?to miyasa ba zamu tafi tare ba?minene ya samu muryar ki?”Laila ta jero mata wannan tambayoyin dan ita a tunaninta gida ne su ke.
Ido Maman ta rumtse tana jin wani raɗaɗi a zuciya,dandanan numfashinta ya fara kokowa ya na fita da sauri-sauri sai wani gurnani ta ke.Da gudu Sappa ta kirawo likita suka shigo tare,fita duk suka yi waje kamar yadda ya buƙata bayan ya dubata ya fito yace “please ku bar barin ta na tuna abinda zai ɓata mata rai dan zuciyarta tayi rauni ba ta iya ɗauka”
“Toh in shaa Allah”malam Nur ya faɗa ya na mai cewa Nazifa ta koma da yara gida tayi sanwa ita da Balkis sai shi su tsaya da Sappa da “toh”kawai suka amsa mashi ba dan sun so ba.
Abun kunya abun takaicin da ya faru bayan su Nazifa sun dawo asibiti shi ne tarar da Maman cikin kashi da fitsari dan Sappa tace ba za ta iya taɓawa ba.Balkis da Nazifa suka yi mata wanka suka canza mata kaya tare da wanke kayan da ta ɓata,turaren huta da na feshe Nazifa ta saka nan ɗakin ya ɗauki ƙamshi.
Bayan sallah isha’i sai ga Umma Sappa sai faɗa ta ke dan mi ba’a gaya mata ba tun lokacin da aka kawo Maman asibiti “Ni nace kar a gaya maki ɗan ke ma ba lafiyar ce da ke ba”cewar malam Nur.
Ummu ba ta koma gida ba nan ta kwana ta cigaba da jinyar ƴar uwarta har lokacin da aka sallami Maman.Duk wanda ya ga Maman sai ya tausaya mata ta rame ta koma kamar ƙwarangwal,godiya tayi ma Umma na jinyar da tayi mata dan yanzu ba ko wane ɗan uwa ba ne zai yin abinda Umma ta yiwa Maman ba.
Cikin rashin jin daɗi malam Nur ke magana yana cewa “kin kyauta Sappa yanzu duk irin karamci da kulawar da Maman tayi maki kin manta har kika kasa wanke kayan fitsarin da ta ɓata?ashe dama butulcin ɗan Adam har ya kai haka?ke yanzu ba ki jin kunya ace Nazi ke kula da Maman ke ki na gefe ki na kallo?a tunanin ki hakan bai yiwa Maman ciwo kawai ta zira Mali ido ne?ba komi kin kyauta”baki Sappa ta turo tace “ni fah wlh ba wai ban iyawa ba ne,kawai ka san yadda ni ke tsoron ɗan malati”bai tanka ta ya cigaba da karatun da ya ke.
***Nigeria
Wasu matasan sojawa ne barjit a wani fontaine su na alwala,Ifan ne ya kalli Tajdeen yace “miye haka Deen alwala ma sai kayi mata kuri?ka wani tsaya ka na sanyin jiki kamar ba soja ba mtsw…”banza Tajdeen yayi da shi ya cigaba da yin alwala cikin nutsuwa.Ko da ya gama ya nufi wurin da aka shimfiɗa tabarmi ya fara sallah cikin nutsuwa har da yin dogon karatu kai kace ba jiran shi ake ba.Lokacin da ya gama dayawan mutane har sun shiga Bus,ɗan dudubawa yayi can ya hangi ta su motai ya na shigowa Irfan ya ja tsuki tare da yiwa Faruk ƙus-ƙus a kunne murmushi Tajdeen yayi yace “to ko da aka haifa cikin musuluncin miyasa ba ku tsayawa kuyi komi cikin nutsuwa kamar yadda aka ce?”shiru su kayi dan sun san ba su da gaskiya.
A kujera tsakiya ya zauna sai ya zamana Irfan na daga gefen hagun shi yayinda Faruk ke dama,nasiha ya fara yi masu duk da ba wani ilimi ne da shi ba wanda ya ke da ɗin ma su suka koya mashi shi amman sam su na négligeant abinda musulunci ya gindiya duka shekarun su 23 ko 24 amman idon su sun buɗe ga mata.
“Ya isa haka malam in wa’azi mu ke so ai ga shi nan a wayoyin mu sai mu saurara ko kuma muje masallaci”cewar Irfan ya na hararen Tajdeen, murmushi Tajdeen yayi wanda ya zame masha tabi’a domin shi ya banbanta da sauran sojawa sam bai da halayya irin ta soja shi ya kasance mai sauƙin kai, haƙuri da fara’a.”Ba komi Allah shirya ku”da “Amen”suka amsa daga nan babu wanda ya sake magana har aka zo garin JOS inda za su yi wani aiki.
Masaukin su na sojawa aka kai su nan suka fara fita,ko wane fuska a murtiƙe sai kace uwanda aka aiko ma da saƙon mutuwa.Chambre guda suka ɗauka su uku,Irfan da Faruk ke ƴar rigai-rigai na shiga toilet a ƙarshe dai a tare suka shiga suka yi wanka wanda yin haka ba wani abu ba ne cikin rayuwar soja,kai Tajdeen ya girgiza ya na mamakin halayyar abokan shi.Sai da suka fito shi ya shiga yayi wanka,ko da ya fito ya tarar da har sun karɓo abinci ko wane ya na ci a cikin ɗan plate.
Shiryawa yayi cikin Kayan shan iska ya haye gado,wayar shi ya ɗauko yayi dealing number Mom bugu biyu ta ɗauka “hello my Deen””Assalamu alaikum Momyna kin wuni lafiya?” “Lafiya lau Deen ya kake?kenan har yanzu ba ka bar wannan Addinin ba ko?”murmushi yayi yace “Mom ai wannan Addinin haske ne ku ma ina maku sha’awar shiga ciki”numfashi Mom ta furzar tace “ba zan hana ka ba Deen amman ka kula sosai dan har yanzu Dadyn ka da Père fushi su ke da kai tun wancan zuwan da ka yi”ido ya lumshe ya na jin yadda Mom ta firgice saboda kawai yayi mata sallama,bai manta ba lokacin da ya tafi ganin gida su ka ga ya na sallah ranar nan yanka shi kawai a ba su yi ba.
“Toh Mom zan kiyaye,ina Mari ?”Mom tace “hum!ina sarkin rigima za ka ce tun ranar da ka tafi har yau ba ta bar bada labarin yaya soja ba”dariya Tajdeen ya tuntsire har da ƙyalƙyatawa yace “kaiiii Mari ta ji rigima,wai ta fa yarda da tare za mu tafi” Mom tace “to ai laifin ka ne kai kayi mata alƙawari”
“Mom sai an jima zan sake kiran ki Chef na son ganin mu”.
Ɗagowa Tajdeen yayi ya na kallon ƴan matan da suka shigo,su ma sojawa ne sai dai kallo guda za kayi masu ka gane ba yara ba ne.Fuska Tajdeen ya tamke tamau ya kalle su yace “ya?wa kuke nema?”sheƙeƙeee su kayi su na kallon shi jin wani rainin hankali.
Feedy ce ta fara takowa gaban shi tana girgiza jiki har ta zo inda ya ke a tsaye,kewayar shi ta fara can kuma ta juyo ta kalli sauran tace “shi ne dai” Irfan da Faruk da suke zaune suna kallon ikon Allah suka kalli juna.
Tsuki Tajdeen ya ja yace “aikin banza kin wani zo kin min tsaye a kai,wuce ki ban waje”ya faɗa ya na ɗan ture ta gefe ya ɗauki plate ɗin abincin shi ya fara ci…….