KADDARA Complete Hausa Novel

Sai bayan komi ya lafa an gama hirar yaushe gamo kaɗai Tajdeen ya samu kan shi,wanka yayi tare da alwala ya kulle ƙofa sannan ya fara gabatar sallah magrib da isha’i.Adu’o’in da ya iya ya karanta tare da roƙon Allah ya sa su Dad da duka familyn su gane musulunci shine mafificin Addini,daga nan barcin gajiya ya ɗauke shi…..
***Maradi
Duk fuskokin su ne suka yi jawur sakamakon wani mawuyacin halin da Maman ta ƙara shiga tun safiyar yau,suma take ta na dawowa ciwo duk ya rikice in banda neman gafara da yafiya babu abinda take sai fah wasiya kula da Laila da take ta nanatawa.
Wani likata ne ya fito a karo na barkatai yace “ku shigo ta na san ganin ku”da sauri malam Nur ya shiga Nazifa da Balkis suka take mashi baya.
A kwance suka tarar da Maman fatar nan ta jikinta tayi fari sol haka ma idonta, oxygène ɗin da aka sa mata a hanci ta cire tare da duban su tace “ku riƙe amanar da Allah ya baku kar ku cutar da baiwar Allah,Laila haske ce a gare ku dan Allah kar ku bari ta wulaƙanta.”da sauri duk suka shiga gyaɗawa Maman kai suna sharar hawaye “Allah yayi maku albarka Nuradeen ka kula da ƙanwarka ka zamo mata uwa da uba kar ka bari tayi kukan maraici, Nazifa ki riƙe amanar mijinki ki daɗa haƙuri kan wanda kike yi a ƙarshe zaki ci riba ku riƙe junan ku da amana.In kun je gida ku cewa Laila ina gaishetaaa….” nan ma ta fara tari tare da kalmar shahada tana yi numfashinta na ɗaukewa har rai yayi halin sa.
Nazifa da Balkis rungume juna suka yi suka fashe da kuka,malam Nur ya shafe idon Maman yana jin ruwan idon shi sun ƙafe.
Babu wani ɓata lokaci aka dawo da gawar Maman gida,aka suturtata aka wuce da ita makwancinta. Umma Sappa banda kuka babu abinda take dama su biyu kaɗai iyayen su suka haifa kuma suka bar su a duniya,yanzu ita ma tabi bayan su ta barta ita ɗaya.Sappa kuwa duk da mutuwa Maman ta kaɗata bai sa ta mance da kuɗin da ƴan fashi suka kwashe ba hasali ma cewa tayi “shikenan tayi mana baƙin cikin kuɗin mu,ta mutu ta bar mu da baƙin ciki na talauci”.
Jin duk gidan ya game da koke-koken mutane yasa Laila fashewa da kuka ta na kiran sunan Ammy ,Jasmine wacce ta zame mata wutsiya domin duk inda za suna tare saboda tayi mata jagora ta ruƙo hannunta suka fito falo.Cike da yarinta Jasmine ke cewa “Lailatu wai ashe Maman ce ta mutu shiyasa su ke kuka”ido Laila ta waro tace “wa ya gaya maki?”Jasmine tace “yanzu naji wata macce na faɗi,kin ga fah duka gidan mutane sun cika shi sam na kasa ganin inda Ammy ta ke”wasu hawaye ne suka shiga ambaliya a fuskar Laila rana maimaita kalmar “innalillahi wa’inna ileyhi raji’un.”…..
Please share
Jikar Rabo ce????
[03/08 à 12:15] Matar Sadauki????: *LE DESTIN…*????
(ƘADDARA)
Story
and
Writtenby
“`CHAMSIYA LAOUALI RABO“`✍????
*RUBUCIYAR*
ƁOYAYYEN SIRRI
MAHAUKACIN SO
ƘAWAR MOMYNA
SADAM
Dedicated to *Amana Writers Associations*????????
☀️ *FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS*☀️
____________________________________________________________
“`MA’ABOTAN SAURAREN LITATTAFAIN HAUSA ZAKU IYA SAURAREN DADAƊEN LITTATTAFAI TA WANNAN SHENEL ƊIN“`????????
*SUBSCRIBE*
_DUNIYAR LITTAFAN HAUSA TV_
https://www.youtube.com/channel/UCcAjVQ74qod9_dL0e_AqkiQ
Page 29-30
Laila na tsaye tana kuka taji an kama hannunta,da sauri murya na rawa tace “Ammy minene ake gidan?ko dai dagaske ne abinda Jasmine ta faɗa min”hannunta Nazifa ta ja suka nufi ɗakin Maman.
Jawota tayi zuwa jikinta tana ƙoƙarin danne kukan da taji ya na taso mata tace “Laila kulu nafsin zha’iƙatul maut,na san kin karanta haka cikin alƙur’ani mai girma dan haka kiyi amfani da wannan Aya ki yiwa Maman addu’a lokacin ta ne yayi.Mu ma wata rana zamu tafi kamar kowa,ƙila ma yanzu ko gobe dan mutuwa na kan kowa”girgiza Laila tayi tace “a’a Ammy ke ba zaki mutu ba yanzu dan Allah ki bar faɗin haka ita ma Maman Allah jiƙanta da rahama”da “Amen “Nazifa ta amsa tana kwantar da Laila bisa gado tace “ki kwanta ki huta kar ki fito ki na ga dai gidan da mutane,zan dawo na duba ki kin ji?”kai ta jinjinawa mahaifiyarta tana mai yin lamo ta luntsuma cikin duniya tunani.
Nazifa na shirin fita malam Nur ya turo ƙofar,ba tare da yace komi ba ya nufi gun Laila wacce shigowar shi yasa ta tashi zaune tana tsaka da yin tunani “Lailana…” “Na’am Abih”hawayen da suka zubo bisa kumatun ta ya goge yace “Maman tace a gaya maki tana gaishe kuma tana son ki” Laila tace “Abih dama ba ta rasu ba?ka kai ni gun ta” “kiyi mata addu’a” ya faɗa yana mai fita.
Matashin kai Laila ta jawo ta rungume a hankali sautin kukanta ya fara fitowa tana shasheka tana kiran sunan Maman,ganin zaman bai yi mata ba yasa ta sauko daga bed ta nufi ƙofa da lalube.Ture ta Twins suka yi uwanda suke ƙoƙarin shigowa,dafe goshi tayi tare da fidda sautin “washhh!”dariya suka shiga yi mata ta ƙyeta Anas ya ja hijab ɗinta ta gefen hagu yayinda Amar ya ja gefen dama.Tamkar wata majaujawa haka suka rinƙa yi mata ita kuma sai ƙoƙarin ƙwacewa ta ke amman ta gaza hakan ya sa tayi tsaye ta na ƙara sautin kuka,sakinta su kayi ta fara lalaben ƙofa sai ji tayi an kwashe ƙafafunta ta faɗi timmm.Wata ƙara ta ƙwala wadda ta jawo hankalin Nazifa da gudu ta nufo ɗakin,ba tare da ta tsaya tambaya mike faruwa ba ta kwashe Twins da mari nan suma suka fashe da kuka tare fita su ka nufi gun mahaifiyar su.
Nazifa na tsaka da rarrashin Laila Sappa ta banko ƙofa “saboda sun taɓa wannan banzar makauniyar ne zaki mara mani ɗiya?”biris Nazifa tayi kamar ba ta ji ta ba wanda hakan ya harzuƙa Sappa ta dungure mata kai tace “magana ni ke”miƙewa Nazifa tayi ta ɗauke ta da mari sannan ta nunata da yatsa tace “ki shiga hankalin ki shiru-shiru ba tsoro ba ne sai dai kawar da fitina,ita makauniya ba mutum ba ce? sai ke mai ɗiya ko?a’a ni ba haifarta nayi ba faɗowa tayi daga sama,banza sakara ballagaza wadda ba ta san ciwon kanta ba”tana gama faɗin haka ta ja hannun Laila suka fice ta bar Sappa dafe da kunci tare da mamaki.
Ƙwafa tayi tana tunanin irin baƙaken cutarwa tare da muguntar da take shirya mata,Twins da su ke kallonta ta harara tare da yi masu tsawa a guje suka bar ɗakin.Bincike Sappa ta fara yi,duk abinda ta san zai yi kuɗi ta mille a haɓar zane kama daga ƴan kunnai,zobe,sarƙa.
Wunin ranai Sappa da baƙin cikin Nazifa a ranta ta yi shi sai dai da ta tuna nan da ɗan lokaci mulkin gidan zai koma hannun ta sai tayi dariya mugunta.
Zaman makoki na kwana uku aka yi kowa ya kama gaban shi,sai a sannan ne mutuwar ta dawo sabuwa dal gun malam Nur Nazifa kullum tana ƙoƙarin tunatar da shi da hakan har ya saba da rashin Maman.
Sappa na zaune tana yankan farce kwatsam sai wayarta ta ɗau ruri,sai da ta kusa tsinkewa sannan ta ɗaga tare da ƙyalewa dan numéro inconnu ne.
“Assalamu alaikum Sappa ce?”amsawa tayi”eh ita ce wacece?”murmushi mai sauti tayi wanda har sai da Sappai taji tace “alhamdullah ashe dai number ce,Mama Latif ce “cike da jin daɗi Sappa ta sake suna ta hira da ya ke sokuwa ce har da baiwa Maman Latif ƴan fashi sun kwashe kuɗin da za’a yiwa makauniya aiki “innalillahi wa’inna ileyhi raji’un dan Allah kar ki ce dagaske kike,yo an kama ƴan fashin?”
“Ina fa aka kama su,ai intaƙaice maki hawayen jini ya kama Maman daga nan ya aikata lahira”cewar Sappa “assha ban ji daɗin haka ba in Allah ya yarda zan zo in yi maki gaisuwa har gida” “Tom na gode sai kin zo”sallama su kayi Mama Latif ta aje waya cike da tunanin wani zagon ƙasa da za tayi mata.
Sappa kuwa kitchen ta shiga ta ɗora girkin rana dan lokacin tasowar Twins ya kusa,jalof ɗin taliya tayi shaf-shaf tana gamawa ta shiga wanka.
Ko da ta fito ta tarar da Twins har sun zuba abincin suna ci,Anas ne ya kwaɓe fuska yace “Momy miyasa yanzu baki sa nama cikin girki? Allah sam abincin bai yi daɗi ba”saurin karɓe zancen Amar yayi da “eh wlh jiya ma almajiri mu ka baiwa abincin”kallon su kawai Sappa take zuwa can tace “to ai sai ku kawo kuɗin naman,dan wancan matsiyacin uban naku in banda talauci babu abinda ke ciciyar shi kullum bai da kuɗi wannan ma da kuɗi na nayi cefane na dafa ”
Duk da Sappa uwar su kuma ta sakantar da su ta hanyar nuna masu komi su kayi daidai to amman ba su ji daɗin zagin mahaifin su da tayi ba,ƙiri-ƙiri Anas yace “Allah kiyaye Abih ɗin mu ya zama banza,kawai tunanin mutuwar Maman ya sa shi ƙin fita ya nemo kuɗi”dundu Sappa ta kai mashi a baya ta shiga zagin su a ƙarshe ta ce su tashi su bata wuri.
Direct part ɗin Nazifa su ka wuce ,a zaune suka isko su suna cin abinci cikin plate guda.Tsayawa su kayi suna kallon yadda su ke komi cikin ƙaunar juna,shinkafa fara ce da mai da yaji su ke ci amman kai kace wani kayan daɗi ne a gaban su yadda fuskokin su suke fitar da annuri.
“Amar duba cikin plate guda su ke cin abinci har da Ammy amman mu kowa da plate ɗin shi”cewar Anas,tsuki Amar yayi yace “to shine mi ai duk ɗaya ba wani banbanci” “akwai banbanci mana ka taɓa ganin Momy ta ci abinci da mu ?kullum cewa take kar muyi ƙazamta kowa ya ci daban”hannun shi Amar ya ja suka bar gun.