HAUSA NOVELKADDARA Complete Hausa Novel

KADDARA Complete Hausa Novel

 

***Niamey

Wata ƴar matashiyar yarinya ce wacce ba za ta wuce 13years ba,tafe ta ke tana karatun Alkur’ani wanda in kana kusa da ita za ka iya jiyo sautin.Ta na daf da shiga gida taji muryar mai motar da tun ɗazu ya ke biyar ta a baya yace “ƴan mata”cak ta tsaya ba tare ta juyo ba,tattaki yayi ya ƙaraso gunta yace “dan Allah in ba zaki damu ba ki faɗa min sunan ki”ƙare mashi kallo tayi ɗan saurayi ne kyakyawa wanda ba zai wuce 27years ba,baki ta taɓe tace “a kan mi kake son sanin sunana?”murmushi yayi wanda ya fito da zallar kyawun shi yace “wato tunda kika fito daga makaranta idona ya sauka kan ki sai naji a raina Allah ya kawo min matar aure” “aure dai?ina matar ta ke”kallonta yayi da mamaki nufinta ba ta gane ba komi amman sai yace “ke mana,wlh tun kallon farko da nayi maki naji zuciyata ta kamu da sonki,so ina son ki kuma da aure”dariya ta sheƙe da shi tace “tunda auren an ce maka har yara ake yiwa shi ba,to a ƙara gaba ƙorafi bai karɓu ba”ta na gama faɗa ta shige gida.

Buguzun-buguzun ta nufi ɗaki ba tare da ta kula Kaka da masifar ta shigo gida ba sallama kamar gidan arna.Turus tayi ta na kallon mahaifiyarta ta wacce tun tasowar ta take ganinta cikin ƙunci da damuwa,a hankali tace “Anya?hallo kukan ne kike?da zan tafi na barki ki na kuka kuma na dawo ki na kuka,dan Allah Anya ya kamata ki daraye ki ɗauki *ƘADDARA* duk son da kike yiwa yaya Tajdeen bai kai wanda Ubangijin shi ke yi masa ba”ɗagowa Anya tayi ta kalleta da idonta da suka rine suka yi ja tace “Halimatu ba ki san raɗaɗin da ni ke ji ba in lokacin tashin ku daga makaranta yayi kuka hauda minti guda a bisa lokacin da kuke dawowa gida ba,to kiyi tunanin ina ga ɓacewa ?”cikin tausayi tace “na sani Anya baki ga wasu ƴaƴan su rasuwa su ke yi ba amman kuma su yi haƙuri?”murmushin da yayi kuka ciwo Anya tayi tace “da mutuwa Tajdeen yayi da hankalina yafi kwanciya akan ɓata ƙila yana can cikin mawuyacin haliiii.”ta ƙarashe maganar tana mai fashewa da kuka,jikin mahaifiyarta ta kwanta ta shiga tayata aikin kukan da ya zame masu sabo kusan kullum sai sun yi shi.

Tsaye Isma’il yayi wanda shigowar shi kenan ya na kallon su,ko bai tambaya ba ya san kukan da su ke domin ɓacewar Tajdeen ta zame masu kamar wata bauta kullum sai an yi hirar shi,tun suna yara suka koyi lesson ɗin ɓatan shi da yadda aka yi ya ɓata wajen Kaka.Cireta Anya tayi daga jikinta tace “tashi ki cire uniforme kiyi wanka kafin sallah magrib ta gabato”miƙewa tsaye tayi sai yanzu suka lura da Isma’il,saurin goge ƙwalla da ta cika mashi ido yayi tare da ƙyarƙyaro murmushin doli.

Bokiti Halimatu ta ɗauka ta nufi randa dan ɗibar ruwa,murya Kaka ta tsayar da ita “to wankan ne na ba gaira babu dalili an taɓa mutum kamar kwaɗo kullum cikin ruwa, Allah kawo miji a maki amre mu huta da wannan ɓarna ruwa ah toh ɓarna mana kin san ba wampo gare mu ba miye na wanka fiye da ɗaya a rana”cewar Kaka ta na nufota za ta ƙwace bokitin,baya tayi da shi ta ɓoye tace “haba Kaka wai ina ruwan ki da ni ?”
“Da ruwana mana tunda ba ke kike ɗauko min ruwan ba,dama can Isuhu ne ɗan ƙwarai ya ke ɗaukan yanzu kuma tunda ya fara ƴan mata ya zama….”ƙyalewa Kaka tayi ganin Isma’il ya fito fuskar nan tamau yace “Kaka yanzu mi na zama?”caraf ta ce “mi fa zan ce in banda ɗan albarka”murmushi Isma’il yayi yace “Kaka…Kakata ta kaina”baki ta taɓe tace “bayan ka cire min zane a kasuwa,ta baya ga wasa kenan”bai kulata ba ya fice.
Dakyal Kaka ta bari Halimatu ta ɗibi ruwa tayi wanka.

Bayan sallah isha’i suna zaune suna cin gujiya Kaka nayi masu labarun lokacin suna ƴan mata???? Halimatu sai dariya take yayinda Isma’il ke zolayar Kaka.
Wani yaro ne yayi sallama yace wani mutum na kiran Halimatu a ƙofar gida fuska ta haɗe tace “ce ma shi ban zuwa”yaron ya amsa da “toh”ya juya da sauri Kaka tace “kace mashi ga ta nan zuwa”inda Halimatu ke zaune tana gunguni Kaka ta kalla tace “maza tashi kije ƴar jakka uba ,in samrayin bai zai ba ta yaya zan amrar da ke”cikin jin haushi Halimatu ta miƙe tana cewa “sai in ke za ayi ma auren amman ni ba ya gaba na”taɓa hannuwa Kaka ta shiga tana salalami “Ni za’a yiwa amren Halimatu?duk wanda nayi a baya bai isa ba”Halimatu dai ba ta kula ta ba ta nufi ƙofar fita……

 

Please share

 

Jikar Rabo ce????
[05/08 à 16:58] Matar Sadauki????: *LE DESTIN…*????
(ƘADDARA)

Story
and
Writtenby
“`CHAMSIYA LAOUALI RABO“`✍????

*RUBUCIYAR*
ƁOYAYYEN SIRRI
MAHAUKACIN SO
ƘAWAR MOMYNA
SADAM

Dedicated to *Amana Writers Associations*????????

☀️ *FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS*☀️

____________________________________________________________

“`MA’ABOTAN SAURAREN LITATTAFAIN HAUSA ZAKU IYA SAURAREN DADAƊEN LITTATTAFAI TA WANNAN SHENEL ƊIN“`????????

*SUBSCRIBE*
_DUNIYAR LITTAFAN HAUSA TV_

https://www.youtube.com/channel/UCcAjVQ74qod9_dL0e_AqkiQ

Page 31-32

 

Jingine ya ke jikin motar shi ya zubawa ƙofar gidan ido, ajiyar zuciya ya sauke ganin ta fito kafeta yayi da ido ita kuma ta harare shi lokacin da taƙaraso.Baya ta juya mashi kafin tace “ina jin ka mi ya sake dawowa da kai?”murmushi mai sauti yayi yace “ai kya bari mu gaisa daga nan sai ki ɗora da tambayata” kallon shi tayi sheƙeƙe tace “ko?ita gaisuwar humm”a yadda take maganar za ka tsinkayo zallar ƙurciya a tattare da ita hakan yasa Yaseer cewa “kiyi haƙuri ki saurari abinda na zo da shi yaa ke kyakyawa” wani daɗi ne ya luluɓeta jin an ce mata mai kyawu “um to ina jin ka”ta faɗa tana kallon shi,tsayuwar shi ya gyara ya fuskanceta da kyau yace “a gaskiya ba zan ɓoye maki ba kin yi min kuma ina son ki shiyasa ma har na biyo ki,da fatan zaki karɓe ni a matsayin masoyi kuma mai ƙaunar ki”jin kalaman shi yasa ta ɗan murmusa tace “na gode da kulawa sai dai ni banda ra’ayin soyayya saboda karatu ne yanzu a gabana”da sauri ya tari numfashinta yace “babu matsala zan jira ki har lokacin da zaki gamawa”dariya tayi a zuci tace “zakwaɗi”a fili kuma tace “ba ka ganewa ne yanzu ta yaya zan gama karatu da soyayya?” marairaicewa yayi yace “please ki amince in shaa Allah ba zan kawowa karatun ki cikas ba sai dai ƙarfafawa”
“Allah ya sa”ta bashi amsa tana kallon ƙofa “komawa za ki yi ko?”kai ta ɗaga mashi yace “to masoyiyya ba ki faɗan sunan ki ba,ni sunana Yaseer”
“Ni kuma Halimatu”ta bashi amsa tana mai yin gaba dan ba ta saba tsayuwar zance ba,kai ya girgiza ganin ko sallama babu ta tafiyar ta.

Key yayiwa motar bai zarce ko ina ba sai gareji,motar ya aje sannan ya zo bakin titi ya nemi taxi ta kai shi pays bas inda a can gidan su ya ke.Ya na shigowa ya ci karo ummar shi bakin ƙofa,hannu ta tara mashi ba tare ɓata lokaci ba ya lalubo duka kuɗin da ke aljihun shi ya miƙa mata.Ƙirga su tayi wajen jikka goma har da wasu ƴan canji,1000f ta miƙa mashi tace “amshi sai ka ƙara da uwanda ka mallaƙe” cikin rashin jin dadi yace “wlh Ummu ban rage ko dala ba duka ne na kawo maki”ya faɗa yana kallon 1000f ɗin da ta bashi alamun tayi mashi kaɗan “oho dai can ta matse ma kuɗin da na baka sune rabon ka,in banda shashanci ai ko ban ce ka kawo na ajiye ma ba ya kamata ka bayar dan wasu abubuwan su kan zo uwanda doli ayi buƙatar kuɗi”Ummu ta faɗa tana mai shigewa ɗan ƙaramin ɗakin ta mai kama da rudun tantabaru.
Cike da baƙin ciki Yaseer ya nufi ɗakinsu na samari,sabbin kayan ya cire ya saka na zaman gida sannan ya jawo kwanon da ake saka mashi abinci ya buɗe tuwon hatsi ne wanda ya sha miyar ɗanyar kuɓewa sai ƙamshi ke tashi.Wanke hannun shi yayi ya fara cin tuwon,sai da yaci kusan rabi sannan ya sha ruwa tare da wanke hannun ya kwanta.
Murmushi yayi ya dafe saitin zuciyar shi da ke bugawa sakamakon tunowa da yayi da abar ƙaunar shi “Allah sa zaki so ni a yadda ni ke, Allah ka gani ni talaka ne amman mutane dayawa na min kallon mai kuɗi wanda sam ban san dalilin haka ba, Allah ina roƙon ka kasa Halimatu ta yarda da ni sannan ta so ni a yadda ni ke ba dan wani abu ba can”Yaseer ya faɗa a fili har da shafa Fatiha.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button