HAUSA NOVELKADDARA Complete Hausa Novel

KADDARA Complete Hausa Novel

Washegari tun kafin bakwai na safe Yaseer ya tashi yayi wanka ya shirya tsaf cikin riga da wando na jeans uwanda suka karɓi farar watar shi kalar hutu,sai da ya gaishe da Ummu yayi mata sallama sannan ya nufi garejin su da ke ɗan nesa da su.
Da zuwan shi ya sauya kayan aiki sannan ya fara gyaran motocin da aka kawo mashi gyara,da sannu-sannu mutane suka fara zowa har garejin ta cika barjit da magyara da kuma masu karɓar abinda suka kawo gyara.
Wani Alhaji ne tsaye kusa da Yaseer ya na ƙirga kuɗi ya miƙa mashi ya na godiya,har zai tafi Yaseer yace “Alhaji ko ka bani na hau naji dan yanzu na gama gyarata ban kai ga hauwa dan jin in gyaran yayi”
“Ok babu damu ga key ɗin”cewar alhajin amsa key ɗin Yaseer yayi ya buɗe ƙatuwar motar Rav4 ya cilla hancinta bisa titi ,ya na bisa hanyar shi ta dawowa kamar an ce ya waige can ya hango Halimatu ita da ƙawayenta suna sauri za su je school.Horn yayi ya tsaya gaban su “Halimatuna”ya faɗa in cool voice ya na sauke glass ɗin mora da sauri ta ɗago kai tare waro ido tace “wai kai ne?”
“Eh ku shigo na kai ku na ga sai sauri kuke kuma lokaci ya ƙure”
“A’a ka bar shi mun kusa kaiwa ai”cewar Halimatu,ɗaya daga cikin ƙawayen tace “a’a kamar yaya?Malama ki shiga ya idasa da mu ko ba ki ga mun yi retard ba?”tana gama faɗin haka Yaseer ya buɗe masu gidan baya duka suka shige har da Halimatu da ya ke yi ma signe ta shigo gidan gaba amman tayi kamar ba ta gane ba.Sunne kai tayi tana tunanin mi za ta cewa ƙawayenta in sun fita,da wannan tunanin ya kawo su har ƙofar école ɗin su.Fita su kayi har sun fara tafiya yace “Halimatu”hakan yasa ta dawo 5000f ya miƙa mata dakyal ta karɓa tayi mashi godiya.

Tun kafin su kai da shiga classe suka samu labarin cewa Mr da zai masu cours bai da lafiya,cike da murnar haka su Halimatu su ka tafi restaurant a nan ne take shaida masu yadda aka yi suka gamu da Yaseer .
“Oh ƙawata kice mun huta mun samu saurayi mai mota kin ga duk inda za mu sai ya rinƙa kai mu wuuu”nan sauran suka kwashe da ihu suna masu cigaba da hira wacce rabin ta duk a kan burin auren mai kuɗi ne.

A jigace ta shigo gida,ko sallama babu ta nufi randa tare da ɗaukar moɗa ta kwankwaɗi ruwa tayi ajiyar zuciya “waiii Allah na gaji wlh,Anya ina Kaka ta ne?”kai Anya ta girgiza tace “yanzu Halimatu wannan wacce irin sara ce kika samu shigowa gida babu sallama sannan shan ruwa daga tsaye?”ƙeya ta sosa tace “ba zan sake ba Anya,am..ina Kaka?”
Anya tace “ta tafi kasuwa”cike da mamaki Halimatu tace “kasuwa wajen mi kuma?”sai da Anya ta kawar da kai tace “talla fura kin san yau ta koma bayan dogon zango”baki Halimatu ta ja tace “sabon kiciyi dai,sai yau ta ga damar komawa talla furai ”
“Kiciyi?”Anya ta tambaya tana kallonta “eh mana Anya ina ce tun bayan ɓacewa Tajdeen ba ta sake zuwa kasuwa ba sai yau”murmushin ƙarfin hali Anya tayi tace “kin san halin Maman cewa tayi fa jiya tayi mafarkin Omar ya maido Tajdeen kasuwa anata neman ta wajen ƴan fura-fura ba’a ganta ba to kinji dalilin”dariya Halimatu ta sheƙe da ita tace “oh Kaka ikon Allah shine sai aka ce mata Yau za’a kawo shi yaya Tajdeen ɗin?toh Allah sa mafarkin nata ya zama gaskiya da nafi kowa murna” “Amen”Anya ta amsa tana jin tsohon mikin ɓatan yaron nata na motsawa.

An ce yawan zama tare shi ke sa shaƙuwa toh hakan ce ta kasance tsakanin Yaseer da Halimatu,wani irin so ne su ke ma juna mai wuyar fassarawa tun abun ya na tsakanin su har ya kai da manya sun shiga zance ta hanyar kawo kuɗin tambaya gidan su Halimatu inda aka aje magana da zarar ta samu BEPC za’a bashi dama ya kawo kuɗin aure.
Son da Halimatu ta ke yiwa Yaseer kusan yafi wanda shi ya ke yi mata,ba komi ya jawo hakan ba sai yawan kyautata mata da ya ke yi da kuma nuna damuwa a kanta,a rana sai ya kirata fiye da goma ya na tambayar ta lafiyarta da kuma abinda ta ke da buƙata.Sosai hakan ke yi mata daɗi wanda kuma yasa hutar gaba da hassada tsakaninta da ƙawarta soyuwa da kusanci mai suna Manira.A ko da yaushe Manira neman wani abun aibu take wanda zai sa Halimatu ta rabu da Yaseer amman ba ta samu ba sai yau kwatsam taje wucewa ta tsinkayi Yaseer cikin gareji ya na gyaran mota,har sai da ta ƙara matsawa ta ɗauki hoton shi dan samun ƙwaƙwarar shaida.

Zaune suke ƙarƙashin itaciyar bedi sai hira su ke cike da nishaɗi,ba su lura da ita ba sai jin muryata tayi tana cewa “ku tsayar da hirar da kuke na samo wani New mai ban dariya da kuma al’ajabi”cewar Manira tana murmushi tare da zaunawa tana mai fiddo wayar ta a sac,ba ta san dalili ba kawai sai taji gabanta ya faɗi hakan yasa ta maida hankalinta ga Manira daidai nan ta haska masu wayar wadda hoton Yaseer ke jikin allon yana tsaye da kayan gareji baƙin mai duk ya ɓata mashi hannuwa “yau dai dubun Yaseer ta cika na kama shi dumu-dumu yana gyaran mota ashe ɗan gareji ne ba mai sayar da motoci ba hhhh”Manira ta faɗa tana sheƙewa da dariyar ƙeta,duk tsayawa su kayi suna kallonta cike da mamaki ɗaya daga cikin su tace “haba Manira miye haka? wannan ai wulaƙanci ne miye abun ɗauko hoton shi da alamu ma bai san kin ɗauka ba”a zabure tace “miye na wulaƙanci?daga faɗin gaskiya ƙarya ce nayi ba ɗan garejin ba ne?”
“Aikin gareji ba sata ba ne neman halak kuma tunda ni ke da ku ban taɓa ce maku Yaseer na sayar da motoci ba ku dai ne ke hasashen haka ganin kullum cikin sake mota ya ke, sannan abu na ƙarshe abun alfahari ga duk mai neman halalin shi a kama shi dumu-dumu cikin sana’ar shi ko ba komi mutumen da ya kama shi ɗin zai gane dogaro da Kai yafi zaman jira”Halimatu ta faɗa tana mai miƙewa ta bar wurin ta nufi classe tana mai ganin buji-buji tsabar ɓacin rai,dakyal ta kai kanta ciki ta zauna bisa table tare da kifa kanta tana sauke ajiyar zuciya da furzar da numfashi.Ta ɗauki kamar 5mn sai ga ƙawayenta sun shigo amman banda Manira,haƙuri suka shiga bata ɗaya ta miƙa mata ruwa masu sanyi ta karɓa ta sha ta lumshe ido sai hawaye sun ziraro mata,cikin murya mai rauni tace “a tunani ko da kwasar kashi Manira ta ga Yaseer na yi ba za ta tozarta shi haka ba,tabbas ni ke da laifi da ban taɓa gaya maku sana’ar shi”jinjina kai su kayi Rabi’at tace “hakan ma bai zama doli sai mun san sana’ar da mijin da zaki aura ya ke yi ba,kawai dai tsiyar gumi ne irin na Manira ba tun yau ba na gano da ta na bin didigin haka ba kawai dai nayi shiru kar na haɗa faɗa,amman ke ma ya isa ki gane tunda ta na yawan tambayar ki”murmushin da yafi kuka ciwo Halimatu tayi tace “ba komi ai duk wanda yayi ta gari dan kansa, Allah na sama na gani duk da zuciya guda ni ke zaune da ku sai an jima bari na tafi gida kaina ke ciwo”dukan su da “toh” suka amsa mata.

Abun hawa ta samu ya kaita garejin,fitowa yayi daga ƙarƙashin mota ya goge hannun shi sannan ya ɗaga kiran “ina ƙofa ka fito”tana gama faɗi ta kashe appel ɗin.
Tun daga nesa ya ga tana goge hawaye,bai tambaye ta ba sai tsayawa yayi kallonta.Sunne kai tayi tana wasa da zoben hannunta lokaci-lokaci sai ta goge ƙwalla,”kukan na minene?dan ƙawar ki ta ɗauki hoto na halan?”da sauri ta ɗago ta kalle shi cike da mamaki,gira ya ɗaga mata yace “Yes na ga lokacin da ta ke ɗaukata ni kuma nayi semblant kamar ban gani ba dan na san ko minene za tayi da shi,ke kike tare da Manira amman na fi ki sanin halin ta a ko da yaushe in naje wajen ki tana yawan yaba kyawun motar da naje da ita tare da tambayata kuɗinta ni kuma ban bata amsa dan ban son yin ƙarya.
Ki na yawan faɗa min yadda ƙawayen ki su ke murna in nayi masu kyauta wanda hakan yasa suke tambayar ki aikin mi ni ke?ko ɗan mai kuɗi ne ni ? wannan dalilin yasa ke kuma kika tambaye ni aikina bayan na shaida maki sai kika ce ko kin faɗawa ƙawayen ki ba za su yarda ni bakanike ne ba”Yaseer ya faɗa yana murmushin da ke ƙara mashi kyau yana kallonta, cigaba yayi da cewa “ko kunya kike ji ace zaki auri bakanike?”kai ta girgiza tare da fashewa da kuka “to kukan minene kike dan Allah kin san ban son zubar hawayen ki”
“Ba za ka gane ba ne Yaseer a gaban mutane fah ta nuna hoton ka tana cewa Allah ya toni asirin ka yanzu hakan da tayi minene in ba tozarci ba?kuma shine kake son kar nayi kuka bayan an zagi mijina?”Halimatu ta faɗa tana kallon Yaseer da idonta da suka fara yin ja tsabar kuka.
Tako biyu ya ƙara hakan yasa suka samu kusanci yace “Leemat kalli cikin idona”ɗagowa tayi ta kalle shi idon su suka sarƙe cikin na juna na tsawon ƴan sakanni kafin tayi ƙasa da nata,nisawa yayi yace”Leemat mi kika gani cikin idona in banda tsabar soyayyar ki da tayi ma zuciyata ƙawayyen da ƙaunar ki? billahil’azim Leemat zan iya yin ko wane irin aiki dan faranta maki tare kare darajar ki,dan haka ki fidda ƙwanƙwanto ko shakka daga duk harin maƙiya na ganin sun raba mu ki sanya a ran ki Yaseer mai son ki kuma zaki zauna da shi a duk yadda ya ke ba wai yadda mutane ke son kasancewar shi ba”murmushi ne ya suɓucewa Halimatu wanda yasa ta biɗi rungume Yaseer dan daɗin kalaman shi……

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button