HAUSA NOVELKADDARA Complete Hausa Novel

KADDARA Complete Hausa Novel

 

Please share

Jikar Rabo ce????
[09/08 à 11:07] Matar Sadauki????: *LE DESTIN…*????
(ƘADDARA)

Story
and
Writtenby
“`CHAMSIYA LAOUALI RABO“`✍????

*RUBUCIYAR*
ƁOYAYYEN SIRRI
MAHAUKACIN SO
ƘAWAR MOMYNA
SADAM

Dedicated to *Amana Writers Associations*????????

☀️ *FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS*☀️

____________________________________________________________

“`MA’ABOTAN SAURAREN LITATTAFAIN HAUSA ZAKU IYA SAURAREN DADAƊEN LITTATTAFAI TA WANNAN SHENEL ƊIN“`????????

*SUBSCRIBE*
_DUNIYAR LITTAFAN HAUSA TV_

https://www.youtube.com/channel/UCcAjVQ74qod9_dL0e_AqkiQ

Page 33-34

Ganin ta saki ranta yasa Yaseer cewa “bari na ɗauko makuli na kai ki gida My baby”ido ta rufe tana dariya ƙasa-ƙasa,ya girgiza yace “hum!kunya ko?sai na cire maki ita dan ba zan bari a ƙware ni”fuskar ta buɗe tare da turo baki ta turo tace “a’a ni dai a bar ni kunyata”kafaɗa ya maƙe alamar ya ƙi sannan ya koma can cikin garejin bai jima ba ya fito riƙe da key.

A hankali ya ke tuƙin,su na tafe suna ƴar hirar su ta masoya har ya kawo ƙofar gidan su.Kashe motar yayi yana dubanta,bai kai ga yi mata magana ba yaji tsinkayo Kaka ta nufo wurin su.Murmushin fuskar shi ya fafaɗa a zuci ya ke cewa “tau!ga ƴar dramer na ta zo ,ko yau da mi aka zo mana”glass ɗin motar ta bubuga,da sauri Leemat ta juya kasancewa ta wajen Seat ɗin da ta ke ne Kaka ta ƙwanƙwasa,buɗe portière ɗin tayi ta ɓata fuska tana kallon Kaka “ke ni ba wajen ki na zo ba kika wani kafe ni da ido kamar mujiya kin wani matse baki sai kace tsohuwa za ta kira sunan Ya’u”Kaka ta faɗa tana ɗan zuro kanta cikin motar,dariyar ta baiwa Yaseer ya shiga ƙyarƙyatawa sake da baki Kaka ke kallon shi tace “to bari ni na gaishe ka tunda yau da dariya aka tarbe ni”dakatawa Yaseer yayi yace “no ba haka ba ne Kakus kawai ke ɗin ce kin fiya ban dariya yanzu amaryar tau ce ta tsuke baki kamar za ta kira Ya’u”caraf Kaka tayi tace “Allah kuwa dan ba ka ga yadda ta cinno shi ba kamar macen kare da shafa jan baki”ɓata fuska Yaseer yayi yace “a’a ni dai amarya ta ba tayi kama da duk abinda kika ambata ba dan ita ɗin kyakyawa ce”baki Kaka ta ja tace “sai a gayawa wanda bai da kyawun dan ni kam ko rabin kyauna ba ta kamo ba dan ma yanzu tsufa yasa ya rage inda lokacin da ina budurwa ne har sai kayi tuntuɓe in ka kalle ni”kallonta Yaseer yayi sai ya ga tabass da kyawunta irin na Fulanin asali sai dai yanayin talauci da wahala yasa farar fatar dishashewa.

Ƙafa Leemat ta zura waje tana mai cewa “sai an jima tunda yau da Kaka za kayi hirar ni na haƙura sai mun yi waya”tana gama faɗin haka ta fita daga mota ta nufi ƙofar shiga gida,haɓa Kaka ta riƙe tace “auf yo kishi ne kike?lalle ga wofi kenan wai harare cikin duhu dan kam hira yanzu mu ka fara tunda shi zai kai ni kasuwa kuɗin taxi na sun huta”Kaka na gama faɗin haka ba ta jira cewar Yaseer ba ta shige mota.

Sai da ya fara tuƙi sannan yace “Kaka yau kuma ziyara za’a kai kasuwa?”
“Wace irin ziyara kamar gantalala na rasa inda zan je ziyara sai kasuwa?haba Ɗan nan “dariya Yaseer yayi yace “toh Kaka na ga ke ɗaya kika fito babu kayan talla koko sayayya ce za ki?”sai da ta kalle shi tace “kayan sana’ar suna can kasuwa na dawo gida ne ganin ko Tujani ya dawo ai ka san shi ko?jikana wanda Umaru ya sace to kullum sai nayi mafarkin zai dawo amman yace min sai in na tafi talla fura zai zo”cike da tausayi ya kalli Kaka da ke share ƙwalla yace “Allah sa ya dawo ɗin,Leemat na yawan bani labarin ɓatan na shi “baki sake Kaka tace “uwar mi ta sani dangane da Tujani da har za ta bada labari?a lokacin fa ta na cikin tsumman goyo,fitsari da kashi duk a wando ta ke humm ta dai ji ana faɗa”daidai nan ya iso cikin kasuwa nan ta fara yi mashi kwatance har ya kawo ta gaban kayanta godiya tayi mashi ta fita,a hanya shi ta dawowa ya kira Leemat ya bata labarin yadda su kayi da Kaka sai dariya ya ke yi mata ita kuma taji haushi ta kashe kiran.

Cike da takaici ta dubi Anya tace “wlh Kaka ba tayi ba!”kallon ta Anya tayi tace “mi tayi kuma yanzu?”Leemat tace “kin ji fa duk dizganin da tayi a gaban Yaseer bai ishe ta ba wai sai da ta ƙara bashi labarin lokacin yarinta ta” “to shi ne mi ?”cewar Anya,baki ta turo tace “wai fah lokacin da ni ke fitsari a wando yanzu wannan magana ta dace?”kai Anya ta girgiza tace “ta shi ki ɗora min waken miya da wannan sakarcin halin Kaka ne a baki sani ba da za ta baki wahala”miƙewa tayi tana gunguni ta nufi madafa.

 

Da dare bayan Kaka ta sharɓi tuwon masara da miyar kuka ta kalli Leemat tace “halan ke kika yi wannan girkin?”da “eh”ta amsa mata tana jiran abinda za Kaka za tace,”haba shiyasa naji uban yaji sai duk ya kashe ma tuwon galmi ina amfanin wannan girkin ko kaɗan bai ƙayatar ba”a hasale Leemat tace “shiyasa na ga kin zubda tare da wanke hannun ki ashe?”salalami Kaka ta shiga yi tare da dakatawa da siɗar yatsun da take tace “magana zaki gayamin Halima?dan kin yi girki na ci?au so kika yi na zubar dan albazaranci da ya ke ba uwar ki ce ta nemo ba”Leemat tace “ai ubana ya nemo”dundu Kaka ta kai mata ga baya tace “eh babu shakka ai ke kika haifar min Haliru ɗin maras kunya”dariya Isma’il yayi wanda ke ta fafutukar duba takardu,duban shi Kaka tayi tace “kai ma har da kai shegantakar za ka yi min?”
“Wane ni Kaka?ni fah cikin jimamin tafiyar da zan yi na bar ki ma ni ke”
“Ina kuma za ka tafi?” Kaka ta tambaya da sauri “Maradi”ya bata amsa kicin-kicin tayi da rai tace “uwar mi za kayi a can?to ko ma dai minene ba da yawu na ba”ta na gama faɗa ta shige ɗakinta ta bar Isma’il da sakaken baki.

“Anya ki na ji wai ba da yawunta ba sai kace uwata,so ta ke na zauna na dafe mu dawwama a talauci” “ba tafiyar ka ba ce matsala garin da za ka tafi ne ta tsana”cewar Anya ,Leemat da ke kusan ta tace “mi garin Maraɗin yayi mata?” “Ku bari in Baffan ku ya zo ku tambaye shi”Isma’il yace “Please Anya ki faɗa mana” miƙewa Anya tayi tace “in ba ka manta ba ranar da kayi mashi maganar za ka tafi Maradi fita yayi ran shi a jagule,to wani babban dalili ne yasa haka”kai Isma’il ya jinjina dan kau tabbas haka aka yi.

Su na nan zaune har Baffa ya shigo gida,bayan sun mashi sannu da zuwa Anya ta gabatar mashi da abinci.
Cikin hankali kwance ya ke cin abincin,can ya dakata ya kalli ƴaƴan na shi yace “ya dai?na ga kun tsare ni ku na kallo ko ba ku ƙoshi ba ne?”kai suka girgiza Anya kuma ta harare su ,wanke hannu Baffa yayi yace “ku gaya min abinda ke faruwa dan duk wunin yau da faɗuwa gaba nayi shi”Isma’il ya zunguri Leemat alamun ta faɗa,kai ta ɗan sosa tace “Baffa dama mu na son sanin minene dalilin da yasa kai da Kaka ba ku son ayi maku maganar Maraɗi?”daram gaban Baffa ya faɗi ya ɗago kai ya kalli Anya,shiru yayi yana tunani sai jin murya Kaka su kayi tana cewa “Allah ya isa in ka faɗa ma su ban yafe ba,miye ke cikin garin Maradi da zai ce can zai tafi?duk garuruwan Niger ba su yi ma shi ba sai can salon ya jajiɓo mana baƙin iri yace ya na so ko?to ba zan lamunci rasa shi ba kamar yadda Sa’idu ya nisanta da mu ba”

“Wanene Sa’idu Kaka”Leemat da Isma’il su ka tambaya a tare suna mai ƙarasawa inda ta ke a tsaye,ƙyafƙyaf tayi da ido sai yanzu ta tuna da tayi suɓutar baki.Baya ta juya masu ba tare da tace masu komi ba,”Please Kaka”suka ƙara cewa ,”yayan mahaifin ku ne”Kaka ta faɗa tana sake rushewa da kuka.
Baffa ne ya cigaba da cewa “mu ƴan asalin Timiya ne da ke can cikin garin Agadez ,mu biyu iyayen mu suka haifa,tun tasowar mu ba mu ga mahaifin mu ba ya rasu tun muna yara.Mama(wato Kaka)ita ta ɗauki ɗawainiya mu tun daga cin mu, sutura,karatun mu duk ita ɗaya tayi ta fama ba tare da dangin uban mu sun tausaya mata ba.A haka har mu ka girma,ni daga collège na tsaya dan ban sha’awar dogon karatu yayinda yaya Sa’id ya tafi lycée,da ya samu BAC ne ya tafi Université de Maradi inda ya cigaba da karatu a can ni kuma na fara koyarwa,sai in sun samu hutu ya ke zuwa ganin gida.A shekarar da ya kusa gama karatu nayi aure inda a lokacin da ya zo bikin ya ke shaidawa Mama shi ma ya samu matar aure ya na gamawa za’a yi magana.”jin Baffa ya tsaya ne yasa Leemat cewa “har yanzu ba’a yi auren ba ne Baffa?”gumin da ya keto mashi ya goge yace “an yi auren mana to tun daga lokacin wata ɓaƙar *ƘADDARA* ta gifta tsakanin mu da shi”a mugun hasale Kaka ta juyo tace “babu wata ƘADDARA shi yayi niyya kuma shi ya zaɓi mace akan dangin shi”
“Mace Kaka ta yaya hakan ta faru”cewar Isma’il,Baffa yace “iyayen yarinya suka ce su ba za su bada ƴar su a tafi da ita wani gari ba sai dai in ya yarda ya aureta su zauna can Maraɗi, kasancewar shi kuma ya na mugun sonta ya amince da haka duk da Mama ta gindiya mashi sharaɗin sai dai ya zaɓa ko ita ko kuma matar da zai aura”
“Yanzu ya na ina Baffa?”cewar Leemat,”ban sani ba Halimatu domin tun bayan da abun ya faru aka fara tsangwamar mu a gari dan wasu cewa su ke ma sayar da Sa’id Mama tayi dan sama ba’a fiya son Ɗan fari be shiyasa mu ka baro garin mu ka dawo nan Niamey”Isma’il ne ya nisa yace “Baffa toh yanzu a ina za mu same shi?ya kamata mu nemo shi dan hannun ka bai ruɓewa ka yanke”kallon Kaka Baffa yayi sai kuma ya sunkuyar da kai yace “ku tashi ku kwanta dare yayi”.Haka ahalin gidan suka kwana kowanensu da abinda ke ran shi game da Sa’id.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button