HAUSA NOVELKADDARA Complete Hausa Novel

KADDARA Complete Hausa Novel

Washegari tun da safe Kaka tayi wanka ta shirya cikin sabin kaya,tsakar gida ta fito ta shiga kiran Baffa.Fitowa yayi cike da mamakin kiran, “ina shi Isuhun ya ke ko bai shirya ba”da mamaki Baffa yace “zuwa ina Mama?”
“Maraɗi mana ko ba can zai je ba?”dariya ta so baiwa Baffa amman ya gimtse yace “Maman sai fah wata shekara ne zai tafi”
“Auf!na zata yau ne ai zai tafi shiyasa nace bari na shirya mu tafi dan nayiwa ita mata Sa’idun kashedi game da jikana,ka san su mata ba iya masu ake ba kai da Ɗan ka amman a nuna an fika son shi da ikon ya”ta faɗa ta na mai komawa ɗaki,Leemat da ke alwala ta girgiza kai tana roƙon Allah kar ya gamata da uwar miji irin su Kaka.

Leemat na sallamace sallah ta waigo ta kalli Anya da ke saƙa rigar sanyi ta zare tace “wai dan Allah Anya mi kika yiwa Kaka ta tsane ki?kin ji fah wai tare za su tafi da Isma’il Maradi dan ta gargaɗi matar Tonton Sa’id”kamar ba za tayi magana ba sai kuma tace “saboda nayi nauyin ƙafa ne ban haihu ba har sai da aka kusa shekara goma da auren mu,babu kuma yadda ba tayi ba da Baffan ku ya ƙara aure ya ƙi to kin ji mafarin ƙiyayar” “Allah shirya ta”cewar Leemat kafin ta jawo waya ta aikawa Yaseer saƙon Barka da Safiya.

 

****Delhi

Wani kyakyawan saurayi ne chocolat color,zaune gaban system ya tsurawa allon ta ido sai murmushi ya ke sauke.
Cikin cool voice ɗin shi mai kama da ta ƴan Ethiopia yace “Momy in shaa Allah ina sa ran shigowa Niger kafin watan azumi,ke dai kawai ki shiryawa zuwa na dan ba zan faɗa maki ranar ba kawai sai kin ganni”murmushi latizuwar tayi mai sanyaya rai tace ” *Abraham* ka faɗan gaskiya kar fa ace duk dan ka kwantar min da hankali ne yasa kace haka “ta faɗa tana shafa jikin system daga can wurinta,dariya yayi wadda ta sa dimple ɗin shi lotsawa yace “Momy zan fah iya zuwa a ɗin nan ma”Momy tace “haƙurina ya kusa ƙarewa,wlh na kusa zuwa Delhi muddin ka wuce wannan month ɗin haba ina laifina ma wajen 5mois rabon da na gan ka a fili,shi kuma wannan likitan ya cika tsarabe-tsarabe ba dan ya hana ni yin balaguro ba ai da tuni na tsufa a Delhi”tagumi Abraham yayi ya zuba mahaifiyar shi ido yadda ta ke faɗa a system kawai dan tayi missing na shi.

Knowking aka yi ya waiwaya yace “Momy sai an jima nayi baƙi”da sauri Momy tace “No kar ka kashe ban gama ba,ya maganar auren na ka da fatan ka samu yarinyar”ɓata fuska yayi yace “Momy karatu fah ni ke banda lokacin kula ƴan mata,kuma ba ma wannan ba mi zan ce in na ga wacce ni ke so?ina nufin kalmar farko da zan faɗa mata”ƙit Momy ta yanke kiran ta na dariya shi ma dariya yayi ya tafi ya buɗe ƙofar da Friends ɗin shi ke tsaye su na jiran shi……

 

Please share

Jikar Rabo ce????
[11/08 à 13:48] Matar Sadauki????: *LE DESTIN…*????
(ƘADDARA)

Story
and
Writtenby
“`CHAMSIYA LAOUALI RABO“`✍????

*RUBUCIYAR*
ƁOYAYYEN SIRRI
MAHAUKACIN SO
ƘAWAR MOMYNA
SADAM

Dedicated to *Amana Writers Associations*????????

☀️ *FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS*☀️

____________________________________________________________

“`MA’ABOTAN SAURAREN LITATTAFAIN HAUSA ZAKU IYA SAURAREN DADAƊEN LITTATTAFAI TA WANNAN SHENEL ƊIN“`????????

*SUBSCRIBE*
_DUNIYAR LITTAFAN HAUSA TV_

https://www.youtube.com/channel/UCcAjVQ74qod9_dL0e_AqkiQ

Page 35-36

Tajdeen ne zaune kan sallaya yana tasbihi da hannun shi,gefen shi kuma Mari ce tsaye tana kallon shi tun farkon fara sallar shi ta shigo.Ta na ganin ya shafa Fatiha ta nufo shi tana mai zaunawa kusa da shi ƙafafuwan su na gugar na juna, saurin janyewa yayi yana mai sakar mata murmushi yace “ya ne ƴar babyta?”baki ta turo tace “yaya Deen shine kake guduna?”kai ya girgiza yace “ni na isa in guji rayuwata,tun da na tafi na matsu in dawo kawai dan na gan ki”cike da murna ta kamo hannun shi tace “dagaske?dagaske ya Deen?”kai ya jinjina mata,kiss ta kai mashi a kumatu yayi saurin rumtse ido ya na jin tsanar haka amman ya zai yi?ɗabi’ar ƴan garin ce ita da ta turawa duk ɗaya,da rana ƙiri-ƙiri za ka ga saurayi ya goya budurwa shi ko da kuwa gaban iyayensu ne za su iya rungumar juna.
Kallon shi tayi cikin ido ta sauke ajiyar zuciya tace “sai yaushe za muyi aure?”da mamaki ya kalleta yace “aure fah?ke ɗin ce za a yiwa aure?haba baby duka nawa kike 12 or 13years ne fah”a shagwaɓe tace “Père yace bai komi ana iya yi mana aure tun yanzu dan suma a zamanin su an sha yin haka”tashi Tajdeen yayi ya na ɗaukar zancen ta shirme,duk ba ma wannan ba shi sam bai ra’ayin auren zobe ya fi son na Musulunci.

“Ki fita zan sauya kaya”Tajdeen ya faɗa ya na mai fiddo wasu riga da wando na jeans ya aza bisa gado,baya ta juya mashi tace “ka saka kayan ka kawai ni ba zan kalle ka ba,in ka gama ka faɗan sai na juyo”shiru yayi ya na sauraren ta har ta gama,kayan ya ɗauka ya shiga toilet ya canza sannan ya fito.
Murmushi yayi ganin Mari tayi tafiyarta alamun fushi tayi, parfumé jikin shi yayi kafin ya ke fitowa main falo.
“Oh!Ni Deen tun ɗazu na aiki Mari ta kiranyo ka amman sai yanzu ka tashi?ko duk gajiyar ce?”Mom ke faɗar haka ta na zuzuba abinci cikin plate gefenta kuma Avani ce zaune tana kallon shi tana yaba kyawun surukin ta a zuci.
Murmushi ya ɗan yi “oh kenan wannan yarinya cewa tayi barci ni ke?amman gwara haka inda tace sallah ni ke ƙila da yanzu an fara haɗa meeting a kaina”Tajdeen ya faɗa a zuci a zahiri kuma kai ya sosa yace “uhm Mom gajiya kam akwai ta kuma ina ga fah yau zan koma dan ba’a ma san da fitowata ba”ɓata rai Mom tayi tace “to ba za ka koma ɗin ba ka bari har gobe”da sauri yace “Please Mom…”hannu ta ɗaga mashi tare da yi mashi nuni da abinci.

Bai da wani zaɓi ya zauna ya fara cin abincin can kuma ya ɗago yace “Mom wai ina ake samun nama (viande,meat)ɗin da kuke girki?na ga ba’a taɓa yankawa a gabana ba”murmushi Mom tayi tace “ai nan nahiyar ba sa yanka bisa/dabba sai dai a kawo mana daga makwabta kamar Kano ,Abuja da dai sauran garuruwa”
“To amman miyasa haka Mom?”
Mom tace “nima ban sani ba mun taso a haka ne,ba ma yin yanka da kan mu sai da mu sawo mu saka a frigo”cigaba yayi da cin abincin shi yace “alhamdullah ko ba komi Musulmai ne ke yin yanka,naman ya hallita a gare ni “duk wannan maganar a zuci ya ke yin ta.

Sai da suka ci suka ƙoshi sannan aka kunna kallo,télé Sahel ta Niger Tajdeen ya kamo bai san ko miyasa ba ya na son ƙasar har cikin ran shi kullum addu’a ya ke Allah sa aiki ya kai su can.

“Ya Deen miye wannan kuma ?za ka tsaya a gun almajirai”cewar Mari kallonta yayi kafin ya maida idon shi kan tv inda ake magana kan yawan almajirai da suka tsananta yawa a cikin babbar jahar ta Niamey.
Zuciyar tausayi ce ta motsa,wani irin suya ran shi ya fara ganin ƙananun yara na bara kan titi.Tunani ya fara to miyasa su ke yin bara?rashin aikin yi ne ko kuwa doli ce ta saka haka?miyasa ba za su bar ƴaƴan su suje makaranta ba dan samun gobe mai kyau?hawaye suka cika idon Tajdeen,kamar daga sama yaji Mom na cewa “tun da ni ke ban taɓa ganin soja mai raunin zuciya ba sai kai,miye wannan Deen?daga kallon tv sai kuka akan mutanen da ba ka sani ba ƙila ma ba journal ɗin yanzu ba ne na dogon lokaci ne da ya wuce”kai Tajdeen ya sunkuyar yana ƙoƙarin mayar da ƙwallar sai dai ya makara tuni ta silalo daga idon shi ta fara ɗiga kan wando shi.Murya na ɗan rawa yace “Mom ina jin ciwo a duk lokacin da na ga yara bisa titi suna ko da talla ce yanzu ya goben wannan yaran zai kasance ba Arabi ba Boko?shin iyayen su ke aika su Bara ko su suka sa kan su?a kullum wannan tambayoyin ni ke yi ma kaina”ya ƙarashe maganar ya na mai ɗagowo ya kalli Mom wacce ita ma shi ta ke kallo.
“Ɗana Deen ya kamata fah ka cire wannan a ranka su fa ba ma ƴan ƙasar mu ba ne kuma ba ma wannan ba kai dai ba mun kula da kai ba to su suka sani tunda har suka kasa ɗaukar ɗawainiyar ƴaƴan su”Mom ta faɗa tana mai miƙa mashi salade fruits,kai ya girgiza yace “Mom Ɗa na kowa kuma addinin mu yace “`Almusulimu haƙun Musulim“` musulmi ɗan uwan musulmi ne,ya kamata ka rinƙa jin ɗacin halin da ɗan uwan ka ya ke ciki dan ba’a san inda rana za ta faɗi ba zai iya yiyuwa gobe kai ka shiga fiye da halin da ya ke ciki”ya na gama faɗa ya miƙe ya nufi ɗakin shi.Jiki a saɓule Mom ta zauna kusan Avani wacce kalmar Musuluncin da Tajdeen ya ambata ke tayi mata yawo a kai,kasa haƙuri tayi tace “Vani ni kam mi Musulunci ya ke nufi” ɗan kallota Mom tayi kafin tace “nima ban sani komi dangane da shi ba,abinda dai na sani addini ne kamar yadda mu ke bautar gumki Ganash to su ma sunada Allahn da suke bauta ma”shiru Avani tayi tana sauraren ta kuma cewa “to su miye sunan gumkin da su ke bauta ɗin?”miƙewa Mom tayi tace “an ce maki ba gumki ba ne abun bautar su Allah shine suke bautawa?”riƙe hannun Mom Avani tayi tace “Please kar ki tafi ina son sanin wanene Allah”murya Tajdeen suka ji yana cewa “Allah shine Ubangiji abun bautawa da gaskiya,bai haifa ba kuma ba a haife shi ba haka kuma bai da abokin tarayya shi shi kaɗai ne,Allah shine Ubangijin rahama mai saukar da cuta ko magani,mai bayarwa ga wanda ya so ya kuma hana ma wanda ya gadama, Allah shi kaɗai ke yin Abinda Ya so,A sanda ya so,Ga wanda ya so.
Allah shine ke bayar da ƴaƴa,wasu ya basu maza duka wasu mata wasu kuma ya haɗa masu duka biyun,wasu kuma ya hana masu.Duk wata ni’ima da huƙuba ta duniya daga gare shi suke,in ka samu shi yayi niyya ya baka ba wai dabarar ka hakan in ka rasa shi ya hana maka ba kasawar ka ba ce,in kuma ya baka ba ya na nufin yafi sonka da kowa ba ne haka in ya hana maka ba ya na nufin bai sonka ba ne a’a wannan ya na ɗaya daga cikin hikimar shi da buyar shi”shiru Tajdeen yayi ganin Dad da Raj sun yi tsaye daga bakin ƙofa suna sauraren bayanin shi,kai ya sunkuyar ganin irin kallon da Raj ke watsa mashi “to sannu tsintatar mage wadda tafi ƴan gida,duk wannan abun da ka zayyano kai a tunanin ka mi?mu yarda da tatsuniyar ka ko mi?to bari kaji na faɗa maka daga yau kar na kuma jin ka ambaci sunan wani abun bauta in ba Ganash ba, entendu ?”Raj ya faɗa yana mai ƙarasowa inda Tajdeen ya ke a tsaye rataye da ƙatuwa sac ɗin shi ta sojoji,rigar shi ya cakumo ya shaƙe shi har sai da idon shi suka fito sannan ya shiga jijiga shi ya daka mashi tsawa yace “ko baka ji ba ne?”.
Père ne ya shigo yace “Raj miye haka kake?sake shi laifin mi yayi maka?”sakin shi yayi ya na huci yace “ka tambayi uban shi ya gaya ma,tsabar ya raina mutane yasa ya sake maimaita kuskuren shi na yin maganar abun bauta wanda ba GANASH ba”Père yace “ya isa haka!daga yau a matsayina na shugaban duka family na ba kowa dama ya zaɓi addinin da ya ke so,dan haka Deen ka cigaba da bauta abun bautar ka babu mai hanaka kuma in akwai mai sha’awa zai iya shiga”da sauri Avani tace “Père ni ina s…”kafin ta ƙarasa Raj ya wanke ta da mari tare da fizgar hannun ta ya nufi part ɗin su.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button