HAUSA NOVELKADDARA Complete Hausa Novel

KADDARA Complete Hausa Novel

Ƙwalla farin ciki Mom ta goge ta kamo hannun Tajdeen tana sakar mashi murmushi,Dad ma kan shi ya shafa yace “tu es libre m1na zaka iya yin duk abinda kake so my son”ajiyar zuciya ya sauke ya rungume iyayen nashi duka kafin yayi masu sallama ya koma compagnie.

Tafe ya ke ya na murmushin jin daɗin zai cigaba da yin addini cikin kwanciyar hankali ba tare da takura ko tsangwama ma kawai sai ya ga Feedy gaban shi,kafin yayi magana ta fesa mashi wani turare mai taken SAI ABINDA NA CE.”Biyo baya na”ta faɗa tare da yin gaba,bin ta yayi har suka isa ɗakin Amrita kamar ko yaushe ɗakin sai tashin ƙamshi ya ke.Shi kaɗai ya shiga Feedy ta tsaya daga baya ta rufe ƙofar da key ta baya kamar yadda suka haɗa plain.

Abun mamaki Tajdeen na shiga turaren ya saki jikin shi dama quelque minute ne ya ke aiki,cike da takaici ya kalleta yadda ta hakimce cikin riga da wando na jeans kamar wata baturiya.Dariyar ƙeta tayi tace “T.Deen yau dai babu inda za ka je domin nan za ka kwana,kar ka kawo gardama domin na sa Feedy ta rufe mu ta baya”maimakon Tajdeen ya razana da abinda tace sai yayi wani ƙayatacen murmushi ya fara takowa inda ta ke a zaune yace “in tafi in je ina wai?humm ai ina nan,ina ne toilet ina son watsa ruwa”ya faɗa yana ɗan dube-dube cike da jin daɗi Amrita ta kai shi can bedroom inda a nan ne ke da toilet ɗin.
Murmushi yayi mata yace “jira ni na fito”kai da ɗaga mashi ta zauna bakin bed tana shillo da ƙafafunta.

 

***Niamey

Aéroport Diori Hamani shahararren filin jirgi ne da yayi fice wajen ƙayutuwa da kuma tsari,duk ko ta ina mutane birjit wasu akan kujeru wasu kuma a tsaye.Lokaci zuwa lokaci Momy ke duba ɗanƙareriyar agogon da ke ɗaure akan tsintsiyar hannunta,tsuki ta ja ta fara zagaye kamar mai ciwon naƙuda cikin masifa ta ke cewa “kun ce ƙarfe biyar jirgin zai sauka amman ga shi har da rabi ta gota mtsw”ba ta ida rufe bakinta ba ƙarar rawar sanarwa ta fara shaidawa ga jirgin nan zai sauka.

Jirgin na sauka mutane suka fara fita,ƙuri Momy tayiwa steep ɗin jirgin ko ƙyaftawa ba tayi har lokacin da Abraham ya zuro ƙafar shi ya fara saukowa murmushi kan fuskar shi.
Fararen idanun shi ya fara buɗewa yana dubawa ko ina zai ga Momy ,”Abrahammm”yaji an faɗa daga bayan shi da sauri ya juya tare da rugawa ya rungume Momy kamar wani ƙaramin yaro.

Sumar kan shi ta shafa suka ɗago suna dariya,kafin su nufi motar Momy hannun shi riƙe da sac ɗin kayan shi.
Momy ke dreving suna tafe suna hira har suka kawo gidan su mai gadi ya buɗe masu porte.
Su na tsaya Momy ta kama hannun shi suka shiga ciki,ajiyar zuciya ya sauke yace “nayi missing ɗin gida sosai Momy”murmushi tayi tace “zo ka ci abinci dai dan yau ba zan barka tsayawa yin wani wanka ba”zaunawa yayi bisa lafiyayar moquette ɗin da ta ke da taushi tamkar jikin Zomo.Drinks yafi kala biyar ta dire a gaban shi tace “sai ka zaɓa duk yau nayi su da kaina”murmushi yayi ya ɗauki na peine de singe ya tsiyaya a kofi ya shanye.
Naman rago wanda ya sha albasa da tafarnuwa da kayan yaji Momy ta zuba mashi akan plate dan yafi son farar dafuwa,yawu na tsinkewa yayi Bismillah ya fara ci……..

 

[ad_2]

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button