HAUSA NOVELKADDARA Complete Hausa Novel

KADDARA Complete Hausa Novel

Ko da aka tashi tsayar da ita yayi ya ɗan mata tambayoyi bisa karatun da aka yi in da ba ta gane ba ya sake yi mata bayani har ta fahimta daga nan ya fara jan ta da hira har ya ke tambayar minene ya sameta jiya nan ta gaya mashi ta na fama da sikila ne cikin tausayi yace “miyasa ba ki je Likita ba?” “mun je mana har suka bani magani”
“Wace Likita kuka je?”ya tambaye ta “CSI Ali Shaibu”ta bashi amsa “ki rasa likitar da za ki je sai wannan?”ɗan kallon shi tayi a raunace sai kuma ta mayar da kanta ƙasa tana wasa da yatsun hannunta,wani gwabran numfashi ya sauke da ya tuna ba kowa ne ke da halin zuwa likita privé ba.
“Ina ne gidan ku?”ya tambaye ta yana mai tsare ta da idanu,ba tayi zaton haka ba amman har ƙasan ranta taji tambayar ” nan ne kusa ba nisa wajen gidan Alhaji mai tumaki”ta ba shi amsa “to daga nan ina za ayi aje?”
“Ai makwabtan mu ne daga gidan shi sai na mu”kai ya jinjina kafin yace “ok wuce ki tafi Samira na jiran ki Allah kauwo afuwa”da “Amen “ta amsa kafin su fito tare.

Turus suka yi ganin Samira da malam Jabeer sai hirar su suke cikin kwanciyar hankali,”ya dai kun gama karatun?”cewar Samira tana kallon su “a’a ba mu gama ba”Nazifa ta bata amsa tana hararenta.
Dariya malam Jabeer yayi yace “haba abun har da baƙar magana?”
“Eh ai ku kuka fara”malam Nur ya ba shi amsa nan dai suka yi sallama suka yo gida.

 

Tun daga wannan lokacin wata shaƙuwa mai game da ƙauna ta shiga tsakanin malam Nur da Nazifa,Samira kuma da malam Jabeer.Wannan alaƙa ita ta ƙara danƙon abotar Nazifa da Samira sai ya zamana ko a gida kullum suna tare ɗan Nazifa ba ta da waya da Samira ce take waya ita da malam Nur,babu yadda bai yi da ita ba akan ya saya mata waya amman fafur taƙi dan ta san Ɗalhat zai iya dukan ta.

 

Cikin canjin da ya samu na nishaɗi ya kalli mahaifiyar tashi yace “Maman ki shirya kin kusa samun ƴa “yayi maganai yana mai sunne kai alamun jin kunya,cike da murna Maman tace “kaiiii haba?Masha Allah yaushe za a kawo min ita na gan ta?”ƙeya ya ɗan sosai gabanin yace “nan ba da jimawa ba ke dai ki taya ni da addu’a”da sauri Maman tace “ai kullum cikin yin ta mu ke sai dai mu ƙara”.
Tsuki Sappa ta ja tana zumɓuro baki gaba tace “haba Maman sai kace dai an yi maki da albishirin kujerar Makka sai wani daɗi kike ji mtwsss”baki buɗe Maman ke kallonta kafin tace “yanzu Sappa wannan ba abun murna ba ne?tun yaushe ni ke jiran wannan ranai ta zo kuma shikenan ba zan yi murna ba?”ƙara turo baki Sappa tayi tace “to ai sai ki bari ki ga yarinyar wa ya sani ma ko ƴar tallakawa ce…”wata irin tsawa ya daka mata jin ta taɓa martaba ruhin shi,da sauri Sappa ta miƙe ta nufi ɗaki dan ta san ba ƙaramin aikin shi ba ne ya ƙara naɗa mata kashi dama har yanzu ba ta warke da bugun yayi masu ita da Balkis ba.

Haƙuri Maman ta shiga ba shi tana cewa “dan Allah ka barta ƙurciya ce “zaunawa yayi yace “ba wata ƙurciya iskanci ne kawai haka ranar nan tayi min wata banza lettre ko yaushe aka haife ta ma da har za ta fara zancen soyayya”
“Soyayya???ita da wa?”Maman ta tambaya shiru yayi jin yayi suɓutar baki dan ko kaɗan bai so Maman ta gane da Sappa na son shi,ganin ta ƙure shi da ido tana jiran amsa ya miƙe ya shiga wayar ƙarya.

Jikin Maman ne yayi sanyi “kar dai a ce Sappa son Ustaz ta ke?shine ta kasa gaya min taje ta faɗa mashi”Maman ke maganar zuciya kafin ta miƙe ta nufi ɗakin su Balkis,kwance ta tarar da ita tana kuka “ashhha!yanzu Sappa kuka ne kike dama?miyasa tun farko ba ki gaya min kina son shi ba shine zaki wani shige ɗaki ki na kuka?maza tashi ki goge hawayen ki gida ba ta ƙoshi ba ai ba za a baiwa dawa ba”cikin jin daɗi Sappa tayi saurin miƙewa tana murna ta shiga toilet.

 

 

 

***Niamey

Wata tsohuwa ce zaune bisa tabarma sai mulmula dawo (fura) gefe guda kuma wani ɗan yaro ne da ba zai wuce shekara shidda zuwa bakwai ba sai tankaɗa gari ya ke yana barbaɗa ma dawon da take dunƙulewa ƴan mili-mili daidai na ƙadago.
Cikin gajiya da aikin yace “Kaka ki tashi mu tafi in mun je can sai ki ƙarasa mulmulewa”cike da kulawa ƴar tsohuwar tace “ah Tujani saurin mi kake haka ne kayi kowa sanin duk lokacin da za mu kaiwa gida doli a jira mu da fura ta tafi ta kowa duk kasuwar garin nan,ungo je ka karɓo ƙnƙara “ta bashi ƙaton tarmus amsa yayi ya fice da gudu ba jimawa ya dawo ya tarar har ta jera kayan tallar.

Ɗan seau(bokiti)da nonon shanu ya ɗauka yayinda Kaka ta ɗauki ƙatuwar ƙwarya dawon ta aza a kai,tarmus ɗin ƙanƙara kuma suka yi kama-kama.
Har sai da suka kai bakin ƙofa Kaka tace “mun tafi sai mun dawo”ƴar ƙwalla baƙin ciki Saude ta goge sannan tace “Allah ya tsare ya bada kasuwa, *Tajdeen* ka kula da kan ka banda yawo”tana gama faɗi ta ɗauki *Haleematu* ta ja hannun *Ismaël* suka shige ɗaki.

Wata uwar ashar Kaka ta aika mata tace “yau na ga ƴar baƙin ciki ni da jikina ba ni da ikon tafiya talla da shi,to ta Allah ba taki ba mai farar ƙafa tun da Haliru ya auro ki ya tsiyace abincin da zaku ci ma sai naje na nemo maku dan talauci amman da ya ke butulu ce ke shine kike jin haushi dan Tijani na taya ni talla…”cikin gajiya Tajdeen yace “Kaka mu tafi kika tsaya sai surutu kike sai Clients ɗin mu sun yi fushi sun fasa saye”dariya Kaka tayi tace “mu je ɗan jikalle na ai uwar taku ce ta fiya mugunta”cikin jin haushi yace “ban so kar ki sake zagin Anya kin ga ba tayi maki komi ba”
“To ni mi nayi mata da ta ke hassadata?”
“Ita ba hassadar ki take ba kawai ba ta so ina zuwa talla so take nayi karatu na zama likita”ƙyaci Kaka tayi suka cigaba da tafiya har suka iso kasuwa dama babu wani nisa.

Tun kafin su zauna costomer suka fara zowa,cikin ɗan ƙanƙanen lokaci Kaka ta fara ciniki dan har ta kusa sayarwa sai habaici take yi ma sauran ƴan fura-furai sanin hali yasa babu wace ta tankata.

Wani mai mota ne ya parker kusan kullum sai ya zo sayen fura wani bi anan ake dama mashi ya sha wata rana kuma ya tafi da kayar shi.
Washe baki Kaka tayi tana amsa sallamar da yayi dan ba ƙaramin burge ta mutumen ya ke ba saboda in ya sayi fura sai yace ta riƙe canji ta sayawa jikanta wani abu.Shi kan shi Tajdeen sosai ya ke son mutumen wanda yace sunan shi Omar.

2000f ya bada yace a dama mashi fura a ba asa madara da suga,fura Kaka ta shiga damawa yayinda Tajdeen ya tafi sawo madara da suga.Bayan ta gama ta miƙa ma Tajdeen ya kai mashi cikin mota,ɗaya gefen ya buɗe mashi sannan ya karɓi roba da aka zuba furai.
Ƙatuwar wayar shi ya ba Tajdeen yana game sai dariya ya ke,sai da ya sha ya ƙoshi ya bashi sauran ya shanye.

 

Yamma lis su Kaka suka shigo,sannu da zuwa Baffa yayi mata ta amsa tana mai cewa “yauwa ga cefanen gobe nan shinkafa da wake za ayi mana da rana da dare kuma ayi tuwon laushi, tunda ni ke kawo cefa ne ai sai abinda nike so”Baffa dai bai ce komi ba sai ƙwala ma Saude kira da yayi,”sannu da zuwa”Saude ta faɗa tana mai sunkuyar da kai “riƙe abar ki bayan kin gama ci min mutumci ɗazu shine yanzu kike wani duƙe kai dan munafurci to ban so” kallon Kaka Baffa yayi yace “haba mama gaishe ki ne fah tayi ai sai ki amsa kafin ki ɗora da faɗan”
“Na ƙi na amsa ɗin ina ce saboda Tijani tayi min rashin kunya “cewar Kaka tana hararen Saude,gefen Tajdeen ta zauna ta shiga duba kayan wasar da Omar ya saya mashi “Tijani wannan karin dai babu wanda zaka baiwa kayan ka dan ba zan bari ka rarraba su ga uwanda uwar su sam ba ta da mutumci”ɓata rai Tajdeen yayi yace “ai dai ƙannai na ne kuma nace maki ki bar zagin Anya (uwa) ban so”yadda yayi kicin-kicin da fuska yasa Kaka dungure mashi kai tace “naji dan gaban goshi uwar ta ka ce sai da haka”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button