KADDARA Complete Hausa Novel

Washe gari ta kama Monday kuma rana ce ta komawa school,tun asubah farin Anya tayi ma Tajdeen wanka dan yau ne za a rubuta sunan shi cikin jerin ɗalibai.
Murna fal ran shi ganin an saka mashi sabbin kaya kuma za’a kai shi makaranta,duban mahaifiyar shi yayi wacce ita ma kallo guda za kayi mata ka gane tana farin cikin haka a zuciyarta kuma murna take Tajdeen zai rabu da talla zai fara karatu.
Kaka ce ta leƙo tana goge ƙwalla tace “dama ni tun tuni na san kin shanye Baffan yara,dan tsabar makirci shine kika saka shi ɗaki kika kitsa mashi a kai Tijani makaranta dan baƙin ciki yiiii”Kaka ta ƙarashe tana rusa kuka da sauri Baffa ya shigo kafin ya kai da magana Kaka tace “in dai na isa da kai kar ka saki ka kai Tijani makaranta a bari har wata shekara duka-duka nawa ya ke?”da “toh” Baffa ya amsa yana ficewa daga gidan rai jagule dan sam mahaifiyar shi ba ta gyara mashi kullum sai tayi mashi katsalandan cikin lamuran iyalan shi musamman.
Hannun Tajdeen Kaka ta ja suka nufi ɗakinta nan tayi ta kwantar mashi da hankali har da bashi kuɗi abu ga yaro dandanan ya manta da wani son zuwa makaranta.
Lokacin zuwa talla nayi Kaka ta ɗauki ƙwarya dawo Tajdeen seau nono kamar kullum suka nufi kasuwa.
Can nesa da inda Kaka ke saida fura Omar yayi parking ya fito waya maƙale da kunnen shi ya jingina da jikin mota,da hannu yayi ma Tajdeen alama ya zo wanda tun tsayawar motar shi ya ƙure shi da ido da sauri ya miƙe ya nufe shi da murna.
Kuɗin furar da zai sha ya bashi da gudu ya kai ma Kaka nan ta bashi kuɗi ya sawo madara.
Ganin ya tafi yasa Omar shigewa mota yabi bayan shi, Tajdeen na tsaka da tafiya yaji oder tsayawa yayi da nufin mai motar ya wuce sai ya ga Omar.Seat ɗin gaba ya buɗe mashi ya shige yana murna shi kuma Omar ya danna ma mota huta ya fara gudu babu ƙaƙautawa…………
Jikar Rabo ce????
[21/07 à 14:08] Matar Sadauki????: *LE DESTIN…*????
(ƘADDARA)
Story
and
Written by
“`Mrs Sadauki“`✍????
*MARUBUCIYAR:*
ƁOYAYYEN SIRRI
MAHAUKACIN SO
ƘAWAR MOMYNA
SADAM
☀️ *FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS*☀️
____________________________________________________________
“`MA’ABOTAN SAURAREN LITATTAFAIN HAUSA ZAKU IYA SAURAREN DADAƊEN LITTATTAFAI TA WANNAN SHENEL ƊIN“`????????
*SUBSCRIBE*
_DUNIYAR LITTAFAN HAUSA TV_
https://www.youtube.com/channel/UCcAjVQ74qod9_dL0e_AqkiQ
Page 5-6
Cikin gajiya da gudun da suke Tajdeen ya dube shi yace “Tonton wai ina ne za mu?ka ga fah mu na wuce shaguna(kanti)inda ake sayar da madara”murmushi Omar yayi yace “kar ka damu wannan tafi ko wace kyau kuma ina son sawowa dayawa ne ta yadda kai ma kullum za ka rinƙa shan guda biyar a wuni ko ba ka so?”baki Tajdeen ya washe cike da murna yace “ina so mana amman ita Kaka ba za ka saya mata ba?”
“Zan saya mata mana har da duk ƴan gidan ku”ya bashi amsa,shiru Tajdeen yayi yana kallon hanya yadda garin Niamey ya tsaru kai kace ƙasar waje ne.
Barci ne ya kwashe Tajdeen tun yana sa ran tsayawa har ya gaji yayi lamo,yafi minti talatin yana barci sannan ya farka amman abun mamaki sai ya ga har yanzu motar gudu take kuma sun baro cikin gari har sun shigo daji.
Cikin alamun tsoro ya kalli Omar yayi narai-narai da ido yace “ka mayar da ni wurin Kaka “wani banzan kallo Omar ya watsa mashi wanda ya sa shi fashewa da kuka.Bai hana shi ba hakan yasa ya cigaba da rera shi yana kiran sunan Kaka,wata uwar tsawa ya daka mashi yace “yi min shiru ko na jefar da kai waje Zaki ya canyen naman jikin ka”tsit Tajdeen yayi ya haɗiye sauran kukan sai hawaye kawai ke mashi zuba.
Ana kiran sallah la’asar suka shiga Dosso,a wani ɗan ƙaramin gida yayi horn aka buɗe mashi.Hannun Tajdeen ya ja suka nufi ciki bayan ya parker mota,a falo suka zauna bayan wani lokaci sai ga wani Alhaji ya fito.Gaishe shi yayi cikin ladabi ya amsa yana kallon Tajdeen wanda idon shi suka ɗan faɗa saboda doguwar tafiya da suka yi.
“Mi sunan ka?”shine abinda alhajin ya tambaya,shiru yayi ya ƙi bashi amsa dan izuwa yanzu duk da ya ke yaro ya san ba sayan madara ba ne ya kawo su nan.
Wanka Omar ya shiga yayi kafin a gabatar ma shi da abinci,cikin plate ya zuba ma Tajdeen ya karɓa ya fara ci dan yunwa ya ke ji sosai.
Bayan sun gama ne ya karɓi saƙo gun alhajin sannan ya ja hannun Tajdeen suka nufi inda ya ajiye mota,titi ya hau nan ma ya shiga ba mota huta bai tsaya ba sai da dare yayi ya fiddo abinci suka ci suka kwana a cikin motar da gari ya waye kuma suka cigaba da tafiya.
Daidai maraba da baƙi ta maradi suka tsaya ya buga waya ba jimawa wani ya zo ya karɓi motar da suka tawo da ita,taxi ya tara aka ida shigowa da su cikin gari daga nan suka nufi tashar mota.
Motoci duk sun cika,har zai juya yaji wani mutum na waya yana cewa Jos zai tafi ai da sauri ya ƙarasa gun shi ya nemi alfarma in babu damuwa su tafi tare in ya so shi zai bada na mai,ba tare da wata matsala ba mutumen ya yarda.
Ƙatuwar mota ce irin wanda ake ma lodi,kujerar kusa da driver ya zauna tare da ɗora Tajdeen saman cinyar shi.
Sai da suka kwan suka wuni amman ko ƙamshi Jos ba su ji ba,ɓangare guda kuma har an saba tsakanin Omar da Jean wanda ya kasance bagwari.
Suna tsaka da tafiya Tajdeen ya aza kuka yunwa ya ke ji,Omar ne ya sauka nemo mashi abinci sai aka yi rashin sa’a a yayi hatsari bisa hanya.Tun Jean yana jira har ya fidda tsammani ,kuka Tajdeen ya fashe da shi yana cewa “dan Allah ka kai ni wurin Kaka ni ban son nan”cikin gurɓataciyar Hausar shi yace “wacece Kaka?ko wancan da ya tafi?”kai Tajdeen ya girgiza mashi ya shiga yi mashi bayani,zufa ce ta karye ma Jean dan ko babu shakka ya gano sato shi ne Omar yayi.
Cikin son kwantar mashi da hankali ya bashi biscuit da yi mashi alƙawarin zai kai shi wajen Kaka,cike da murna Tajdeen ya fara cin biscuit ɗin shi kuma Jean ya cigaba da tuƙi har suka isa Jos.
Wani tangamemen gida suka tsaya,tun shigowar shi mutanen gidan uwanda duk maza ne suka fito ko wane murmushi kan fuskar shi.
Tsaye Tajdeen yayi ya na kallon jama’ar uwanda duk kusan kamar su guda haka ma tsayi,hannun shi Jean ya kama suka ƙarasa.
Fuskar shi dattijon cikin su ya shafa yana mai ɗan rage tsayin shi yace “ina ka samo wannan kyakyawan?”ya faɗa yana kallon Jean a nan tsaye yayi masu bayani,cike da tausayin Tajdeen duk suka shiga taɓa kan shi suna mashi murmushi “mi sunan ka ?”dattijon ya tambaya lokacin da suke shigowa babban falon gidan “Tajdeen”ya ba shi amsa “to daga yau za mu dinga kiran ka da Deen kaji ɗan kyakyawan jikana”kai Tajdeen ya ɗaga yana murmushi wanda shi kan shi bai san na minene ba….
****Niamey
Wajen minti talatin Kaka na jiran Tajdeen shiru,inda Omar ya tsaya da mota ta kalla da niyyar yi mashi magana wayam babu shi babu motai maimakon hankalin Kaka ya tashi sai cewa tayi “ka ga ɗan albarka mai tunani ya ga Tijani ya daɗe shine ya bi min sawun shi”ta fada tana mai rufe furar da ta dama ma Omar murfi.Can wasu mitinan ta riƙe haɓa tace “yau ni na ga gantalale daga bin sawun yaro ba kai babu shi balle daɗa madarar”ta kusa da ita ce ta tambaya “ni kam Delu lafiya kike ta surutu ke ɗaya?”
“To ba doli nayi surutu ba tun ɗazu Tijani ya tafi sanye madara har yanzu bai dawo ba kuma shi ma Umarun haka”ido ta fiddo waje tace “kar dai kice mai motar da ya ke zuwa nan sayan fura?” “Eh shi fah,bari ki ga na tai na dubo su da kaina ƙila suna can shago(kanti)suna sayen kayan maƙulashe sun bar ni nan da tashi zuwan kan fura”cewar Kaka tana mai tashi ta tafi gun mai madarar da kullum Tajdeen ke sawowa,ba ta jima ba ta dawo hankali tashe tana gugar ƙwalla da haɓar zane “ka rufa min asiri Umaru ka dawo min da jikana,oh waini ni Delu”kafin wani lokaci wurin kancame kowa sai tofa albarkacin bakin shi ya ke dayawan mutane gani suke son banzar Kaka ne ya jawo haka yayinda Ɗan Ladi ke ta ƙara maimaitawa ya ga lokacin da Omar ya saka Tajdeen a mota ya wuce a guje.