KADDARA Complete Hausa Novel

Shaƙe shi Kaka tayi tace sai ya fito mata da jika ai da shi aka gama baki,dakyal aka taɓe shi ga hannunta.Zaman ƴan bori tayi ta fasa ihu “wayooo ni Delu mi zan ce ma Haliru in na koma gida?ubangi ma’aikin Allah ya tsine ma Umaru Allah gama ka da bala’in duniya, innalillahi ileyhi raji’un jama’a ku cece ni ku karɓo min jikana”sosai Kaka ke kuka,ganin haka aka tsayar da mai taxi aka sakata tare da kayan sana’ar ta sai wata da ta shiga dan kaita.
A tsakar gida suka tarar da Anya hannunta dafe a saitin zuciya,Haleematu na kuka amman ta kasa ɗaukar ta saboda lugude da faɗuwa da gabanta ya ke.Tun kafin su shigo kukan Kaka yayi masu sallama,da azama ta miƙe ta nufi waje kiciɓis suka yi da Kaka wace ake kokawa saka ta gida amman fafur tace ba zata shiga ba doli sai da Tujani.
“Ina Tajdeen?”Anya ta tambaya murya na rawa zuciyarta na tsinkewa,”ya tafi da Tujanina ya tsere da shi”Kaka ta faɗa cikin kuka kafin su an kare sai ji suka Anya ta yanke jiki ta faɗi.
Kukan Kaka ne ya ƙaru tana mai kwance kwagirin ƙugunta ta fiddo wayata tana cewa “na shiga uku ungo kira min Haliru”mai taxi ya amsa ya shiga répertoire nan ya danna ma Baffa kira.Ba jimawa sai gashi cikin tashin hankali,ciciɓar Anya yayi ya saka a taxi suka nufi asibiti Kaka kuwa sai kuka ta ke har roƙon likita tayi ya bata gado yayi mata allura barci ko taji sanyi a ranta.
Sai da Anya ta sha ƙarin ruwa sosai kafin a samu ta farka,hawaye ne ke zuba kan fuskarta tana jin abun kamar cikin mafarki .Tun tafiyar su kasuwa take jin faɗuwar gaba ashe iftila’in da zai faɗa mata ne,a hankali ta fara motsa baki “innalillahi wa’inna ileyhi raji’un allahuma ajirni fee musibati wa’akhlifni khairun minha”sai ta rumtse ido tana mai cigaba da yi mashi addu’a a zuci ta na mai roƙon Allah kar ya ba shi ikon cutar da Tajdeen….
***Maradi
Kwance take bisa darduma hannunta riƙe da carbi tana ja,a zahiri tasbihi take amman a zuci tunanin malam Nur ne fal ranta.
Sallama wani yaro yayi yace “wani yace a kirawo mashi Nazifa”ras gabanta ya faɗi kafin tace wani abu Inna tace “je kace ga ta nan zuwa”kafin ta kalli Nazifa wadda ta taushi zaune “ki tashi mana ki ga ko wanene” “toh Inna “ta faɗa tana mai miƙewa ta saka takalmi.
A can ƙarƙashin wata itaciya ta hango shi,sanye ya ke da wani farin yadi ya taje sumar kan shi sai walƙiya ya ke baƙin gilashi ne a idon shi.Sai da tayi wata sanyayar ajiyar zuciya kafin ta ƙarasa gun shi bakinta ɗauke da sallama.
“Tare da sahibata abun alfaharina”shine malam Nur yace fuska ta rufe da hijab alamun jin kunya kafin tace “ya gida ina Maman da su Balkis”kwaɓe fuska malam Nur yayi yace “shine ni ba za a tambaye ni ya nike ba?toh duka lafiyar mu lau”dariya Nazifa tayi tace “laaa to kai ba ga ka a gaba na ba?hum to naji ya kake ?”bai bata amsa ba sai kallon ta da ya tsaya yi hakan yasa ta sunne kai ta fara wasa da yatsun hannunta, murmushi yayi dan kunyar ta na ɗaya da abinda yasa ya ke sonta “ya dai babyn Nur?”ba tare da ta ɗago ba tace “daidai” “ok shine kuma kika ƙyale ni”yadda yayi maganar a shagwaɓe yasa tayi saurin ɗagowa ta dube shi “kuma ni za’a ayi ma shagwaɓa?????”tsayuwar shi ya gyara tare da cewa “eh mana in ban yi maki ba wa zan yi ma?”tana shirin magana yaya Ɗalhat ya karyo kwana layin wanda ƙarar tsohon moton(Babur) shi ne ya shaida mata da zuwan shi yadda malam Nur ya ga ta firgita ne yasa shi kallon Ɗalhat wanda ya ajiye mota ƙofar gida ya doso inda su ke.
“Keee!wuce maza gida,kai kuma wa ya baka izinin zuwa da har za ka wani parker mota kana wanke ƙaunata da ƙarya salon ka yaudare ta”shine abinda Ɗalhat ya faɗa cikin ɗaga murya tun kafin ya iso inda su ke.Cikin rawar murya Nazifa tace “yaya Ɗal…”wata uwar tsawa ya daka mata tare da nuna mata gida da gudu ta ruga ta na mai fashewa da kuka ………
No comments
No typing????????♀️
Please share
Jikar Rabo ce????
[22/07 à 09:38] Matar Sadauki????: *LE DESTIN…*????
(ƘADDARA)
Story
and
Writtenby
“`CHAMSIYA LAOUALI RABO“`✍????
*RUBUCIYAR*
ƁOYAYYEN SIRRI
MAHAUKACIN SO
ƘAWAR MOMYNA
SADAM
Dedicated to *Amana Writers Associations*????????
☀️ *FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS*☀️
____________________________________________________________
“`MA’ABOTAN SAURAREN LITATTAFAIN HAUSA ZAKU IYA SAURAREN DADAƊEN LITTATTAFAI TA WANNAN SHENEL ƊIN“`????????
*SUBSCRIBE*
_DUNIYAR LITTAFAN HAUSA TV_
https://www.youtube.com/channel/UCcAjVQ74qod9_dL0e_AqkiQ
Page 7-8
“Assalamu alaikum”malam NUR yace ma Ɗalhat yana mai miƙa hannu alamun suyi musabaha wani banzan kallo yayi mashi tare da ɗaga mashi hannu yace “bari abar ka abinda zan faɗa maka ka fita hanyar ƙaunata,kar na koma sake ganin ka nan”murmushi malam Nur yayi “babban yaya kar kayi min haka mana ai duk wanda yace ya na son naka ya gama maka komi a duniya”ya faɗa yana ɗan jan gemu,taɓe baki Ɗalhat yayi ya kuma cewa “Ni ba zaka yaudare ni da salon ustanzanci ba haka kuma ba zan bari ka yaudari ƙaunata ba in dagaske kake sonta ai sai ka turo magabatan ka”yana gama faɗar haka ya juya ya shige gida ba tare da ya tsaya jin ta bakin malam Nur ba.
Tsakar gida ya tarar da ita kwance tana kuka gefen ta kuma Inna na rarrashin ta,da sauri Inna ta miƙe tana kallon Ɗalhat wanda sai kumbura ya ke yana batsewa “Inna miyasa zaki barin ta hira?yanzu sabida Allah salon a rinƙa yi da ni ana cewa ba mu bata tarbiyya ba ido na ganin ido ta fita zance duk wanda ya wuce yana kallon ta kuma abun takaici wai Ɗan masu kuɗi…”saurin katse shi Inna tayi da “in ban barta hira ba kai zaka auren ta?nace kai za ta aura koko ba ka ga girma take ba?shi wanda ka kora ɗin ka san wanene? malamin su na makaranta ne wanda ta ke faɗa ma saboda karatun da ya ware ya ke koya mata na musamman sauran ɗaliban ke jin haushin ta,ina ce kai ma da kan ka har daɗi kaji ganin tana ta samun ilimi ko?”wani huci ya furzar yace “Inna ki yi haƙuri sam ban yi tunanin shi ne ba dan a yadda na gan shi bai yi kamata da malamin makaranta ba,amman in shaa Allah ba zan sake korar shi ba in ya zo”ɗagowa Nazifa tayi fuska shaɓe-shaɓe da hawaye ta kalli yayan na ta tace “dagaske ya Ɗalhat?”kai ya jinjina mata,cike da murna ta tashi ta wanke fuskarta ta nufi gidan su Samira.
Gidan babu kowa sai Samira zaune kan kujera ta na wankin kaya gefe guda kuma portable ɗin ta na fidda sautin waƙa.Sallama Nazifa tayi kafin Samira ta kai ga amsa mata ta kuma cewa “Allah ya shirye ki ke yanzu waƙa ce kike sauraro ko kunya baki ji matar malam guda?”sheƙeƙe Samira ta ɗago tana kallonta tace “to sannu ustaziya miye na jin kunya daga sauraren waƙa sai kace wata ta gamtsi wadda ba ta kamata ba ” “waƙa dai sunan ta waƙa malama dama bege kika saurara da ya fi wannan shirmen”ruwan wankin ta watsa mata a fuska tace “wlh ke ce shirme ba ni ba”dariya Nazifa tayi “kan ki dai ake ji”ta faɗa tana ɗaukar waya tayi composé lambar malam Nur amman a kashe.
Cikin sanyi jiki ta labarta ma Samira abinda ya faru “to miye na damu tunda yanzu ya Ɗalhat ɗin ya amince ya rinƙa zuwa?”
“Samira ba zaki gane ba ne ta yaya kamilin mutum kamar malam Nur a jefe shi da muggayen kalamai?ni wlh in da na san gidan su da na tafi na bashi haƙuri”cike da mamaki Samira ke dubanta tace “haƙuri?eh lalle yanzu na yarda da maganar ɗalibai da su ke cewa kin fi son shi fiye da yadda shi ya ke son ki,wannan rawar kai har ina?yanzu ke sabida sai ki tai gidan na su dagaske?”kai ta ɗaga mata alamun eh, baki Samira ta ja tace “to ADS ne gidan su kuma dukɗan ɗan adaidaita sawun da kika ce ma ya kai ki gidan Ali Ɗan Masani zai kai ki”dafe ƙirji Nazifa tayi tace “ki na nufin ɗan Alhaji Ali Ɗan Masani ne?”tsuki Samira tayi tace “sai ki yi,nima jiya naji malam Jabeer nayi mashi kirari”jikin Nazifa ne yayi sanyi dan duk yadda take zaton malam Nur na da kuɗi ba ta zata jinin Alhaji Ali ba ne “gaskiya yaya Ɗalhat,ni yanzu mi ma zai yi da ni ƴar tallakawa uwanda abincin da za su ci ma ya na yi masu wuya wata rana?”
“To shine mi dan ya na Ɗan masu kuɗi ke kina ƴar tallakawa?ina ce dai akwai ƴaƴan masu kuɗin dayawa a makaranta amman ya nace sai ke ko?”
“Samira ina jin tsoron kar dangin shi su ki karɓata,na san malam Nur ba dan wani abu ya ke sona ba in ma akwai bai wuce ilimi shi ma Allah ne ya bani” “hum!su kuma su suka ba kan su kuɗin ko?Nazifa ya kamata fah ki nutsu ki gane da tallaka da mai kuɗi duk Allah yayi su kuma shi kaɗai ya san manufar yin haka,dan Allah ya baka arziki ba ya na nufin ya fi son ka da kowa ba ne in kuma yayi ka tallaka ba wai dan bai sonka ba ne a’a hakan dai ya ga yafi dacewa da rayuwar ka”wani lumfashi Nazifa ta sauke tace “na sani amman abinda ni ke nufi ni ba classe ɗin shi ba ce ya fi ƙarfina”cikin jin haushi Samira tace “kawai kice dama baki son shi tun farko amman zancen wani ba ajin ki ba ne bai ma taso ba,kyawu ma na banza kin fi shi kuɗi kawai zai gwada maki su kuma ba komi ba ne fa ce dauɗar duniya in baka kashe su ba ka mutu ka bar su”
“Tabbas haka ne Allah sa dai mu dace”cewar Nazifa ta na mai shiga galerie inda hotunan malam Nur su ke,da “Amen”Samira ta amsa mata kafin ta miƙe ta fara shanya kayanta…