KADDARA Complete Hausa Novel

A ɓangaren malam Nur dakyal ya kawo kan shi gida dan baƙin ciki da tiririn da zuciyar shi ke yi ma shi,tun da ya ke ba’a taɓa yi mashi cin fuska ba sai yau.
Ya na isa gida direct part ɗin shi ya wuce ba tare da yayi la’akari da Baba wanda ya ke zaune a falo yana duba wasu littattafai.
Toilet ya shiga ya sakar ma kan shi ruwa,a ƙasan zuciyar shi kuwa “innalillahi wa’inna ileyhi raji’un”kawai ya ke nanatawa har ya fara jin sauƙin abun.
Cikin kayan ƴan balo (ƙwallo)ya shirya ya feshe jikin shi da turare sannan ya ɗauko system ɗin shi ya kunna, hotunan ta ne ya ke kallo wasu ta na dariya wasu ta shagwaɓe fuska .
Bai san lokacin da murmushi ya kubce ma shi ba da ya zo inda ta washe baki tana dariya kyawawan haƙoranta fari tas uwanda suka samu ƙawanyar wushirya,sai dimple (point beauté) ɗin ta mai ƙara mata kyau da ya lotsa.Ya shagala sosai da kallon hoton hakan yasa bai ji shigowar Baban na shi ba,sai jin ya dafa kafaɗar shi a razane ya ɗago ya sauke idon shi kan fuskar mahaifin shi wanda shi kuma ya ke kallon hoton Nazifa wanda ke bisa system.
Miƙewa yayi ya na ɗan sosa kai yace “um…Baba ina wuni?”murmushi Baba yayi ba tare da ya amsa gaisuwar da yayi ma shi ba yace “wacece wannan?”i’ina malam Nur ya fara “dama…dama ita ce wadda ni ke gaya ma Maman ina so”wani murmushin Baba ya sake yi yace “shine tace ba ta sonka wanda hakan yasa ka shigo gida rai ɓace ba tare da ka gaida ni ba ka wuce ɗaki sannan ina tayi ma sallama baka ji ba?”kai malam Nur ya sunne yace “ba wai cewa tayi ba ta sona ba” “to minene” “Baba magajinta ne yace min wai wani in dagaske ni ke in turo magabata na dan shi bai barin ƙaunar shi hira”
“To shine mi?ai hakan ne daidai ka bani address ɗin gidan za mu je in shaa Allah ai mu dama maganar auren mu ke so”tsabar jin daɗi Ustaz bai san lokacin da ya rungume Baba ba.
Ƙarfe goman dare Maman ce a ɗaki sai saffa da marwa take ,ta rasa sukuni tun lokacin da Sappa ta shaida mata tana son Nur.
Wani gwabron numfashi ta sauke kafin ta nufi part ɗin Baba,a zaune ta tarar da shi bisa tapis ya na tasbihi da yatsun hannun shi.Bayan ta gaishe shi ya amsa ya zuba mata ido ya na kallo duk wunin yau yanzu kawai ya ganta sam babu walwala a tare da ita a kwana biyun nan yana lura da ita.
Gyaran murya yayi hakan ya sa ta ɗago suka haɗa ido,kamar daga bisa taji yace “mi ke tafe da ke ?na ga da magana a bakin ki”gyara zama tayi tace “eh dama akan maganar auren yaran nan ce, Ustaz da Sappa shine nace bari na sameka na nemi alfarma ayi bikin ɗaya rana da na wacan ɗayar da ya zaɓa amman dan Allah kar kace ba ka yarda ba dan wlh Sappa na matuƙar son Ustaz wanda har son yayi mata mugun illa yanzu haka kullum sai an yi mata ƙarin ruwa”Maman ta ƙarashe maganar ta na sakin.
Sororo Baba yayi yana kallonta,sam abun ya zo ma shi banbaraƙwai, amman shi kan shi shaida ne yadda akan ciwon Sappa wanda kullum ƙaruwa ya ke.Nisawa yayi yace “ba damuwa zan yiwa shi Nur ɗin magana” cike da jin daɗi Maman ta shiga yi ma Baba godiya sai kace ba mijinta ba ne.
Washe gari zuwa 12 na rana sai ga valises (akwatina)kala biyun da Baba yasa akawo ana shigowa da su,a falo aka ajiye su.Cike da murna Maman ta shiga buɗa akwatinan,kaya ne na azo a gani a cicike “Maman valises ɗin wanene?”cewar Balkis wadda fitowar ta kenan daga ɗaki “na matan yayan ki ne ɗaya na Sappa Seat ɗayan kuma na ɗaya amaryai”cike da murna Balkis ta fara tsalle kafin kuma ta ruga zuwa ɗaki sai gaya sun fito ita da Sappa wacce duk ta rame,a bayyane ta nuna farin cikinta gabanin ta sunkuyar da kai jin Maman na cewa “wane kika ɗauka kalar zaiba koko jajayen?”ba ta ce komi ba sai Balkis da tace “Maman bari mu duba wanda kayan ciki suka fi kyau sai anty Sappa ta ɗauka”
“Duk kayan kala ɗaya ne ai”cewar Maman murmushi kan fuskarta.
Malam Nur kuwa ya na can maƙale da waya shi da sahibar shi ya na shaida mata cikin satinan za’a kawo komi su yi aurensu su huta,kwaramniya da ihun Balkis ya fito da shi falo turus yayi jin zancen da ake wai har da Sappa zai aure.
Ran shi ne ya ɓace fuskar tayi kicin-kicin jijiyoyin kan shi duk suka fito,cikin furzar numfashi yace “wace Sappai???? ?”ba Sappa da ke kusan shi ba hatta Baba da shigowar shi kenan sai da ya razana,cikin tashin hankali ya ƙaraso tsakiyar falon ya durƙusa saman ƙafafun shi tare da game hannuwa yace “dan Allah Maman kar ki min haka wlh ni a matsayin ƙanwa na ɗauketa kuma ni banda tsarin zama da mata biyu Nazi ita ruhina,rayuwata da komi naw….”ƙara faɗuwar Sappa ne ya hana shi ƙarasawa da sauri duk suka nufi gun ta inda ta faɗi a sume……..
*In labarin ne bai yi maku sai ku faɗa min na bar ba kaina wahala na ajiye shi,ku karanta abu ku ƙi yin comments ko godiya babu???*
Please share
Jikar Rabo ce????
[23/07 à 11:53] Matar Sadauki????: *LE DESTIN…*????
(ƘADDARA)
Story
and
Writtenby
“`CHAMSIYA LAOUALI RABO“`✍????
*RUBUCIYAR*
ƁOYAYYEN SIRRI
MAHAUKACIN SO
ƘAWAR MOMYNA
SADAM
Dedicated to *Amana Writers Associations*????????
☀️ *FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS*☀️
____________________________________________________________
“`MA’ABOTAN SAURAREN LITATTAFAIN HAUSA ZAKU IYA SAURAREN DADAƊEN LITTATTAFAI TA WANNAN SHENEL ƊIN“`????????
*SUBSCRIBE*
_DUNIYAR LITTAFAN HAUSA TV_
https://www.youtube.com/channel/UCcAjVQ74qod9_dL0e_AqkiQ
Page 9-10
Ruwa masu sanyi Maman ta zuba ma Sappa nan ta shiga sauke ajiyar zuciya,bakinta ɗauke da sunan Nur.Baba, Maman da Balkis dukansu su ka juyo su na kallon shi yadda ya nuna halin ko a jikin shi,hawaye Maman ta goge tana kallon shi cikin ido hakan yasa ya ƙarasa cikin cool voice yace “Sappaaa…”ƙyalewa yayi ya ja dogon numfashi sannan ya cigaba da cewa “ki yi haƙuri kin ji?in shaa Allah ni da ke mutu ka raba” Sappa da ke kwance cikin ruwa da sauri ta buɗe idonta tarau kan kyakkyawar fuskar Ustaz wacce take tsanwa sharrr saboda ambaton Allah.Kai ya jinjina mata ganin tayi mashi ƙuri ta na son gasgatawa,ido ta lumshe tana jin wani sanyi na ratsa gangar jikinta ba ta san lokacin da murmushi ya suɓuce mata ba.
Kanta Maman ta shafa tace “Balkis ja ta ku tafi ɗaki ta canza kaya”da “toh Maman”ta amsa ta na mai taimaka ma Sappa ta miƙe a kunyace.
Ustaz kuwa gidan su malam Jabeer ya wuce ya na jin zuciyar shi babu daɗi ,a ƙofar gida ya zauna yana jiran fitowar shi.Seat ɗin mai zaman banza malam ya zauna yana mai gyara hullar shi yace “ya dai NazNur ka kira ni na zo kuma ka wani duƙe kai ko sallamar da nayi ba ka amsa min ba”ajiyar zuciya malam Nur ya sauke kafin ya ɗago fuskar shi ya kalli malam Jabeer “subahanallahi mi ya sami idon na ka suka yi ja haka?”cikin ɓacin rai ya ba shi amsa da “sun ƙaƙaba min auren Sappa Jabeer yanzu mi zan ce ma Nazi ?da wane ido zan kalleta na gaya mata su biyu zan aura?”zama malam Jabeer ya gyara yace “ban gane ba yi min dalla-dalla”nan malam Nur ya bashi labarin komi da ya faru ya ɗora da faɗin “ka san dama ta sha gayamin ta na sona to ban zata rashin kunyarta ta ba har ta kai haka shine tayi min gami da iyayena su kuma suka yanke hukunci ba tare da neman shawara ta ba”jinjina malam Jabeer yayi kafin yace “to shi aure lokaci ne kuma matar mutum kabarin ya,yanzu yadda za ayi ka bari har sai an sa date ɗin bikin ku sannan ka gaya ma Nazifa”
“Ka na ganin hakan shine mafita?” “Eh tabbas”nan dai malam Jabeer ya cigaba da kwantar ma abokin nashi da hankali tare da nuna mashi mahimmancin yiwa iyaye biyayya ba dan bai sani ba sai dan ƙara yi ma shi tuni su ma sunada haƙi kan shi.