HAUSA NOVELKADDARA Complete Hausa Novel

KADDARA Complete Hausa Novel

 

Cikin sati guda kacal Baba yasa aka yi bincike dangane da tarbiyya Nazifa inda ta samu kyakyawa shaida hakan yasa ba ayi ƙasa da gwiwa ba aka kai lefe tare da tsayar da rana aure nan da wata biyu.

Mahaifiyar Sappa ba ƙaramin daɗi taji ba ganin zumuncin su zai ƙara ƙarko ita da ƴar uwarta,Sappa kuwa tun da aka kawo lefen ta ƙara ɗaukar son duniya ta ɗorawa Ustaz dan yanzu abokan ta SapNur su ke kiranta.

 

Tun wayewar safiya yau take yawan jin faɗuwar gaba,ko dan za ta je gaishe da iyayen Nur ne oho.A haka dai Samira ta tsantsara mata lalle tayi wanka sannan ta shafa mata hoda,za tayi mata kwalliya yayi ta meakup tace ba ta so.
Wani rantsantsen lèche coton ta saka mai ratsin ja,hijabi da kalmi da sac ta fitar jajaye hakan ba ƙaramin fiddo ta kayan su kayi ba.
“Masha Allah”shine abinda Inna ta faɗa Rakiya da Samira kuwa sai kallonta su ke yadda ta fito sak amarya.Hotuna Samira ta fara ɗaukar ta a wayar da malam Nur ya saya mata kafin ta fito waje inda Ustaz ke jiran ta.
Sai da suka gaisa da Samira kafin su wuce gidan Maman,a falo duk suka tarar da ƴan gidan ana zaman jiran Nazifa.Malam Nur ne yayi sallama yana gaba ta na biye da shi a baya,a ƙasa ta zube tana mai kwasar gaisuwa cikin sakin fuska Maman ke amsawa kafin Balkis tace “ina wuni anty amarya”ɗagowa Nazifa tayi ta kalli inda taji murya ta sakar mata murmushi sannan ta amsa akan idonta Balkis ke zungurar Sappa wacce sai cika ta ke ta na batsewa,dakyal tace “sannu”shi ma ɗan ta ga irin kallon da Ustaz ke jifarta da shi ne,gaban Nazifa ne ya faɗi cikin sanyi da taji duk jikinta ya ɗauka ta amsa ma Sappa kafin su tsaya ƴar kallon-kallon.Wata irin muguwar tsana ce Nazifa ta hango cikin idon Sappa,cikin zuciyata kuma take tambayar kanta “to ita kuma wannan wacece?mi nayi mata ne daga gani na take hararena? …”ba ta tsinke da lamarin Sappa ba sai da taji ta ja tsuki ƙasa-ƙasa tare da cewa “baƙauya kawai”kallon Sappa Maman tayi dan ta ji sarai abinda tace.

 

“Sappa tashi ki ɗauko ma antyn ki ruwa mana,kun wani sa ta a gaba ku na kallo haka ake tarban baƙi?”Maman ta faɗa cikin bada umarni,gunguni Sappa ta tafi ta na yi ta shiga kitchen Balkis ta bi bayanta.
“Anty Sappa mi za ki yi da ruwan pampo ?ba dai amayar ce za ki kai ma ba?”Balkis ta faɗa lokacin da ta shigo ta tarar da Sappa na zuba ruwan pampo cikin moɗar ƙarfe,yatsina fuska tayi tace “eh mana ai su ta saba sha a gidan su ko ba ki ga ƴar tallakawa ba ce”cikin jin daɗin zancen ta Balkis tace “a haka kuma Ustaz ke son abar shi”ta na gama faɗi ta ɗauki jus ɗin citron ɗin ta haɗa ta fita,ƙanƙara ta zuba cikin verre sannan ta tsiyaya lemun ta miƙa ma Nazifa sannan ta ajiye sauran kusa da ita ko da buƙatar in ta ƙara.

“Merci”Nazifa ta faɗa tana mai yin Bismillah ta ɗan kurɓi lemun cike da kunya, Ustaz na kallonta ya na jin son ta na ƙara ratsa shi ya lura a takure take hakan yasa ta kasa cin fruits ɗin da Balkis ta kawo.

Zamewa yayi daga bisa salon ya zauna ƙasan capet,trayn ya jawo gaban shi ya ɗauki ayaba ya ɓare tare da nufar bakinta “buɗe bakin ki na ciyar da ke tunda kunya kike ji”ɗagowa tayi ta kalle shi ta sannan ta juya inda Balkis ke zauna Maman kuwa tuni ta bar gun, ɗan turo baki za tayi magana kawai ya tura mata ayabar a baki ba ta da wani zaɓi hakan yasa ta ɗan guntsira tana murmushi.Taratsee kofin glas ɗin da ke hannun Sappa ya sulɓe,dukan su kallonta suka yi banda Nazifa da ta sunne kai zuciyarta na bugawa das-das.

Wata uwar tsawa Ustaz ya daka mata “keee!wane irin hauka ne wannan?so kike ki firgita min mata ko miye ?maza ɗauko tsintsiya ki kwashe shi sannan ki goge wurin”wasu zafafan hawaye suka karyi ke ma Sappa ta ɗauko salade de fruits ne dan ta nuna ma Nazifa isa da su sun san yadda ake shan shi kuma sun saba sai ga shi kogo ya juye da mujiya.Sanin halin shi ya sa tayi saurin tattare glas ɗin da ya fafashe ta kwashe sannan ta goge wajen tsaf,cikin kuka ta nufi part ɗin su.

Ajiyar zuciya Balkis ta sauke kafin tace “Allah yaye maki wannan baƙin halin”kusa da Nazifa ta zauna tace “antyn mu dan Allah kiyi haƙuri ki ci duk wannan abun saboda ke fah nayi shi”ta faɗa tana mai sake jawo wani tray mai ɗauke da abinci,saving na ta yi amman fafur Nazifa tace sai dai Balkis ta sa hannu su ci tare.
Kallon malam Nur Balkis tayi sai ya jinjina mata kai hakan ya sa suka fara cin abinci shi kuma ya nufi ɗakin baba,bai fito ba sai da ya kwatanci sun kamalla sannan suka fito shi da Baba.Gaishe shi tayi tamkar uban da ya haife ta cikin kulawa Baba ke amsawa ya na tambayar ta ƴan gida da kuma karatu.

Har Nazifa ta tashi tafiya amman Sappa ba ta sake fitowa ba,goma ta arziki Maman da Baba su kayi mata Ita kuwa sai zuba godiya take.Kafin Nur ya sauke gida sai da ya biya Kalla Transa Mall yayi mata sayayya ƴan abubuwan da ba za a rasa ba.

Ganin irin hidimar da aka yiwa Nazifa ya sa Inna jin sanyi a ranta da tunanin ko ba ta da rai Nazifa ba za tayi kukan maraici ba dan a yadda Nazifa ta tsaya ta na yabon Maman da Balkis abun sai Masha Allah.
Samira da Rakiya sai buɗa kayan su ke suna fesa turarurukan,bayan sun gama gani ne ta ba kowa rabon shi Inna dai sabulu kawai ta amsa ta ajiye ma Ɗalhat.
“Tashi ki raka ni gida zan wuce”Samira ta faɗa ta na mai ɗaukar ledar kayanta,hijab Nazifa ta saka suka kamo hanya a nan ne Nazifa ta shiga ba Samira almara Sappa ta ƙare da cewa “wlh har cikin raina ni ke jin tsoron ta dan da irin mugun kallon da take min ba ƙaramar tsanata take ji ba”numfashi Samira ta ja tace “to Allah kyauta sauƙin ta dai ba ƙaunar malam Nur ba ce da kin shiga uku kin san ƴan uwan miji in ba su son ka akwai matsala”
“Eh haka ne sosai, amman dai su na da alaƙa dan da alamu a gidan take zaune inda ma naji sauƙin abun da yake tana tsoron Noori”cewar Nazifa ta na mai tsayawa dan sun ɗan yi nisa da gidan su alamu kuma sun nuna daga nan za su rabuwa,sallama su kayi kowa ya tafi gida.

 

Da dadare bayan sallah isha’i malam Nur ya kirata a waya suka sha hira su ta soyayya wacce rabin ta duk akan yadda bikin su zai kasance ne da irin rayuwa da za suyi bayan aure.
Har sun yi sallama Nazifa tayi saurin tsayar da shi tace “um..Ni kam Noori wannan wacece wadda na gani gidan ku?”duk da ya gane wadda take nufi amman ya basar yace “wace fah daga ciki?”fuska ta ɓata kamar ya na ganinta tace “ba Balkis ba ɗayar”
“Wai Sappa kike nufi?” “Um ita”ta bashi amsa “kishiyar ki ce”ya samu bakin shi da furtawa,shiru tayi kamar ba taji ba sai da ya sake maimaita mata daga ƙarshe yace zai ƙara yi mata bayani daga baya ya kashe wayar.A daren ranar nan juyi Nazifa ta aniya yi ba ta rumtsa ba,kalmar kishiyarta ce ta tsaya mata a rai.

Washe gari ta kama asabar ranar zuwa makaranta tun bayan kawo kuɗin aurenta ba ta sake zuwa ba sai yau da malam Nur ya bata umarnin zuwa.
Lati tayi yau kasancewar tayi ranar tashi,tun da ta shigo ƴan ajin ake kallonta ana ƙus-ƙus-ƙus ita dai ba ta kula su ba gefen Samira ta zauna ba jimawa malam ya shigo.
Har zai fara karatu wata tace “malam yau ba’a bulalar lati ne ?”duk ɗaliban kallonta su kayi,malam ya so yayi kamar bai ji ta ba amman kar ace yayi son kai saboda Nazifa ta zo late kuma ya san saboda a ga yadda zai yi ne suka kitsa haka.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button