KADDARA Complete Hausa Novel

A zaune ya tarar da ita a man falo,sanye da kayen barci tana kallon tv ta saka tray fruits a gaba tana ci.Wani irin miƙewa tayi tana kallon sanyin idanunta wanda ke sheƙin amarci,ba tare da ta amsa sallamar da yayi mata ta faɗa a jikin ta saki kuka.Duk ƙoƙarin hanata da malam Nur yayi bai sa ta dakaga ba,da sauri ya ɗagota yana cewa “lafiyar ki kuwa Sappa?mi ya ke damun ki?yanzu a hakan ne kike zaune tsirara?”saurin sakin shi tayi ta zuba mashi ido cikin raunin murya tace “yaya Nur miyasa baka sona?minene wanda ake so ga ɗiya mace wanda ni ba ni da?ko ban cancanta ka so ni ba ne?”kawar da kai malam Nur yayi gafe yace “tafi ki suturta jikin ki sannan ki zo mu yi magana”yadda yayi magana sérieux yasa ta jawo wata doguwar rigar abaya ta hauda saman kayan barcin ta na mai zaunawa ƙasa kusan ƙafafun shi.
Huci ya furzar yace “Sappa ina son ki bani hankalin ki nan ki nutsu ki fahimce ni, muddin ki na son samun soyayya ta doli ne ki bi Naziii sau da ƙafa ban so kiyi wani abu wanda ranta zai ɓace, ki zauna da ita lafiya ki ɗauke ta matsayin yayar ki in kin yi haka ina mai tabbatar maki zaki samu soyayya Nuradeen akasin haka kuma hummm kin san sauran”tun da ya fara maganai ta buɗe ƙofofin kunnuwanta tana sauraren shi daki-daki,wasu hawayen takaici ne suka zubo mata amman ta danne zuciyata tace “in shaa Allah zan yi in dai ka so ni” dangwala mata yayi da yatsa yace “good girl????????”kafin ya ke miƙewa yace “na tafi sai na dawo ki kula da kan ki”amsa mashi tayi da “a dawo lafiya”tana jin daɗin kalmar ta kula da kanta da ya faɗa.
Nazifa kuwa sosai ta sha barci ba ta tashi ba sai da shabiyun rana ta gota shi ma kiran Inna ne ya tashe ta,bayan sun gaisa Inna tace ” ki bani hankalin ki nan Nazifa ina so ki saurare ni da kunnuwan basira”da “toh Inna”ta amsa ta na mai yin zauna.
Nasiha Inna ta fara yi mata ta ɗora da cewa “Nazifa ina so ki ɗauki *ƘADDARA* a duk yadda ta zo maki,wani abu ba zai taɓa samun bawa ba face dama ya na rubuce a cikin allon ƘADDARA sa,sau tari abubuwa su kan zo mana ba tare da mun shirya zuwan su ba ko kuma ba yadda mu ka tsara su ba,da haka ni ke cewa ki zama mai biyayya tare da duban uzirin mijin ki.Tun kafin auren ku Nuradeen ya same ni da maganar iyayen shi za su gama shi aure da ƴar uwar shi kuma bai da wani zaɓi sai nayi masu biyayya,ya faɗa min ne saboda ya kasa tunkarar ki dazancen gudun kar hankalin ki ya tashi ba dan ya na tsoron ki ba sai dan gudun ɓacin ran masoyi.Yanzu haka kishiyar ki na nan cikin gidan da kike kawai dai an raba ɓangarorin ne,ki riƙe ta amana ki zauna da ita da zuciya guda kar naji kar na gani kin yi wani abu na cutarwa”tunda Inna ta ambaci kalmar kishiya taji kamar an buga mata guduma amman kuma sauran kalaman sun ɗaure mata jijiyoyi,hawaye ta goge tace “toh Inna in shaa Allah zan kasance mace ta gari” “Allah maki albarka ya kuma baki ikon yin haka”cewar Inna sannan tayi mata sallama.
Jiki ba ƙwari Nazifa ta shiga tayi wanka tare da simple kwalliya ta saka riga da zane na atamfa,kitchen ta nufa ta haɗa tea ta sha sannan taci sauran kaza jiya.Tv ta kunna ta zauna ta na duba Chaine sai taji ana bubuga ƙofa,izinin shigowa ta bada aka turo ƙofar tare da yin sallama.
Amsawa tayi tana mai kallon Sappa wacce kallo guda za ka yi mata ka gane amarya ce,gaban Nazifa ne ya bada ras dan ko babu tantama wannan ce kishiyarta ta.Wurin zama ta bata,zaunawa Sappa tayi ta na cewa “ina kwana anty amarya”amsawa Nazifa tayi cikin sakin fuska kafin ta bata ruwa.
Tv su ke kallo lokaci zuwa lokaci suna ɗan taɓa hira kafin daga ƙarshe Sappa tayi mata sallama ta koma ɓangaren ta,Nazifa kuwa Samira ta kira suka sha hira daga ƙarshe Samira tace tana nan tafe….
***JOS
Wanka Vani tayi ma Tajdeen ta saka mashi kayan da mijinta Jean ya sawo,sosai Tajdeen yayi kyau ya fito asalin bafulatanin shi.Cikin jin daɗin sabin kayan da ta saka ma shi yace “na gode tantie”da sauri Vani tace “no daga yau da Mom za ka rinƙa kira na kaji ko?”kai Tajdeen ya ɗaga yace “toh Mom”kan shi ta shafa ta na jin son ɗan har ƙasan ran ta,Jean da ke gefe ya na kallon su yace “toh ni kuma da mi za’a kira ni ?”kallon Vani Tajdeen yayi alamun ya na son jin amsa daga gareta “Dad ɗin ka ne dan haka shi ma daga yau Dad za ka kira shi kaji ko?”kai Tajdeen ya jinjina alamun toh.
Hotuna Mom ta fara ɗaukar shi wasu ya na tsaye wasu kuma zaune kafin ta jawo shi su fara selfie suna dariya inda a ƙarshe Dad ya shigo suka rinƙa ɗauka tare gwanin sha’awa.
Wasap Mom ta shiga ta saka hoton da suka saka Tajdeen a tsakiya kan profil (dp)sauran kuma ta zaɓi masu kyau ta saka a status,inda ya ke shi ɗaya ta rubuta “`My son Deen“` a sama.
Cikin zumuɗi irin na wanda bai taɓa samun haihuwa ba suka kamo hannun Tajdeen zuwa babban falon gidan,a zaune suka tarar da Raj,Ranvir,Rahul da kuma Père wato dattijon.
Dukan su da murmushi su ke kallon Denn in ka fidda Raj wanda tun zuwan Tajdeen ya ji ya tsane shi har ƙasan ran shi.
Hannuwa Père ya buɗe yace ma Deen ya tawo,cikin rashin sabon haka Tajdeen ya shige jikin tsohon.Kan shi Père ya rinƙa shafawa yana sa mashi albarka kafin yace “ya kamata ku tashi mu ɗan zaga gari ta yadda jikalle na zai saki jikin shi”dariya dukan su suka yi dan sun san halin Père da son yara dan dai ma Allah ya jarabi babban yayan nasu Jean da rashin haihuwa kuma shi kaɗai ne mai mata sai Raj wanda ake shirin auren shi.
Cikin gari suka shiga suna zagawa Tajdeen kuwa ya ware ido sai kallon abubuwan mamaki ya ke yadda mutanen garin ke rayuwa irin ta turawa,mata na saka sutura wacce ita da babu kusan ɗaya yayinda mazan garin su ka ɗauki shan giya da sauran kayan maye kamar ado.
Sai da Père ya ga alamun kamar Deen ya gaji sannan suka koma gida,Mom kuwa ta ja hannun Ɗan ta suka wuce part ɗinta ta sake yi mashi wanka tana cikin shafa mashi mai Dad ya shigo dariya yayi mata yace “abun nema ya samu ko?to a rage yi mashi wanka kar mura ta kama shi”dariya tayi tare da rufe ido alamun jin kunya kafin ta buɗe akwati ta zaɓo mashi wasu kayan……
Please share
Jikar Rabo ce????
[25/07 à 11:47] Matar Sadauki????: *LE DESTIN…*????
(ƘADDARA)
Story
and
Writtenby
“`CHAMSIYA LAOUALI RABO“`✍????
*RUBUCIYAR*
ƁOYAYYEN SIRRI
MAHAUKACIN SO
ƘAWAR MOMYNA
SADAM
Dedicated to *Amana Writers Associations*????????
☀️ *FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS*☀️
____________________________________________________________
“`MA’ABOTAN SAURAREN LITATTAFAIN HAUSA ZAKU IYA SAURAREN DADAƊEN LITTATTAFAI TA WANNAN SHENEL ƊIN“`????????
*SUBSCRIBE*
_DUNIYAR LITTAFAN HAUSA TV_
https://www.youtube.com/channel/UCcAjVQ74qod9_dL0e_AqkiQ
Page 13-14
Rayuwa mai daɗi Tajdeen ke fuskanta,ya ci abinda ya ke so ya kwanta wuri lafiyaye babu abinda ya fi yi mashi daɗi irin kayan jikin da ake saya mashi tsadadi.
Soyayya da Vani da mijinta su ke nuna mashi ko ɗan cikin su sai haka amman duk da hakan Tajdeen bai sa ya mance Anya da Kaka ba dan kusan kullum sai yayi ma Mom hira su,ita kuwa tayi ta dariya jin shirmen da Kaka ke yi.
Cike da kulawa take shirya Tajdeen cikin uniforme ɗin makarantar da zai fara zuwa yau, murmushi tayi bayan ta gama shirya shi tace “iyeee ɗan Mom ka ga yadda uniforme ɗin nan tayi maka kyau kuwa?zo muje ka duba madubi ka gani”kusan ƙaton madubin suka isa nan kyakyawar fuskar shi siriri irin ta Fulani ta bayyana,sai sumar kanshi wadda ta ɗan toho ita ma sai ƙyali take.