HAUSA NOVELKURUCIYAR JUMMAI Complete Hausa Novel

KURUCIYAR JUMMAI Complete Hausa Novel

A islamiyyah kuwa ta dade da sauke al-Qur’ani mai girma, yanzu karatun littafan addini take yi sai hadda da ta maida hankali akai sosai, yanzu bata fita gashin masara sabida shirye shiryen azumi.

Jummai ne zaune da allawiya bisan beanchi a kofar gidan su.

Tace allawiya mai zai hana MU shiga sabon makarantar islamiyyar nan na bayan layin mu.

Tace ai guda biu ne sabbi wane cikin?

Tace ke “”nurul Islam””din

Allawiya tace lalai jummai an fara hankali.

Tace ke cikin littafin nan da na karanta naga mijin yafi son amaryan sabida tana da ilimin addini kuma ga ibada.

Ita uwar gidan kullum office, ko karatun sallah bata iya ba.

Allawiya tace haka ne kinsan mutane vasu gane ba,gani suke littafan hausa bata tarbiya yake, kuma ai ba duka aka taru aka zama daya ba.

Wake daya ke bata iri, sai kaga mace ta zauna ta rubuta zallar batsa a littafi mutane ayita wawason karantawa, wasu yaran hadda cewa suke idan ba littafin wan ce ba, bana karatun na wan ce domin babu show a ciki.

Shi yasa mallamai kan ce rubutun da karatun littafan Hausa duk haramun ne.

Sabida masu rubuta batsan,sun bata tarbiyar yara da dama,dan yanzu har yar primary zaka ga tana karatun littafai, TAMA fi wata babban mace zaqe wa.

Masu rubutu akan kyawawan yan mata da samari,manyan masu kudi,yadda ake mugun tarairayar mace a gidan mijinta,many an motoci, yadda samari ke kashe ma mata million yin kudi da dai sauran su.

Sun bata tarbiyar yan mata da dama, sun kashe ma mata aure da dama.

Sai kaga budurwa tace, ita tafi son saurayi kyakyawa,mai mugun kudi, manyan motoci,babban gida sanan uban shi wani ne a gwamnati,Wanda kuwa cikin maza dari hardly ne ki samu Biyar masu irin abubuwan nan da kike so, daga nan ayita zaman jira har ki tsufe a gidan Ku, wasu kuma su shiga karuwanci dan su samu irin abinda wance keda acikin littafi.

Yanzu an var aduba Qualities da addini ya tanadar mana wurin Neman aure irin

Addini
Assali
Ilimi
Tarbiyar da makamantar su

Wurin mace kuma
.

Addini

Asalli

Illimi

Kyau

Dukiyaa da makamantar su

Sai jiran tsamani, ina kira ga yan mata da samari da MU kyara, MU mika lamuran MU ga ubangiji, sai yayi mana zavi mafi alkhairy.
Masu rubutan da basu fayace batsa ciki sai kuga baa damu da littafan su ba.amma inda za a natsu a karanta sai kuga an amfana da abubuwa da dama.

Wani mistake guda kuma da writers ke yawan yi
Sai kaga littafin Hausa ne fa, amma sai turanci yafi hausar yawa a ciki.

Bamu bin ka’idodin rubutu,idan Hausa zaki rubuta, ya zamana zallar hausar ce.
Idan turanci zaki rubuta, ki rubuta zallar turancin ki.

Domin wasu karatun hausan kawai suka iya, basu Iya na turanci ba.

Wash sun iya karatun turancin amma basu San ma’anar sa ba,wani lokaci marubuciya sai tayi amfani da manyan kalmomi ko jimloli na turanci.

*DON ALLAH MU GYARA*
*ina kira ga writer’s din MU da MU gyara,MU rinka rubutu akan abinda ke tafia da addinin MU,al’adun mu zamani,lokaci da kuma abinda ke yiwuwa*

Sun rubuta exams din cikin nasara, bayan sun gama ne aka basu Hutu sai bayan sallah da sati guda zasuyi resuming, kowa ya tafi gida cike da kewar juna.

Form suka amso, bayan sun ciki suka mayar.

An fara azumi cikin kwanciyar hankali, su jummai kuma sun fara zuwa islamiyya
Bayan sallar asuba;- hadda sai 7 am ake tashi.

10am aje islamiyya,zuwa 2pm bayan sunyi sallah a can, a fara tafsirin al-Qur’ani mai girma zuwa 4pm ake tashi, sai hadda na dare 8:0pm to 10:0pm.

Yanzu ta fara natsuwa tana gaida mutane,sabanin da,tana kama ma ummma aikin gida, idan kaga tayi fada janta akayi.

Wani mai kudi a unguwar su””alhaji na wudil””yayi sabuwar amarya nafisa.

Buzuwa ce bata iya komi ba, ko sanwa, dama jininta ya hadu da Aysha.

Aysha takan shiga ta koya mata abinci, gyaran gida, tana mata lalle da kiso,musamman ma da azumin nan da mijin kanyi shefanai mai yawa iri iri, gidan aysah kan yini ta na koya mata abubuwa tare da kama mata aiki.

Tunda umma ba wani abin azo a gani suke dafawa ba, iyaka kunu ne sai tuwo sai kwadon ganye.

Ranar da baba yasamu kasuwa kamar Friday,sai ayi ruwan tea ba bread, shinkafa,ko faten doya kona dankalin Hausa.

Nafisa na matukar tausaya masu, sabida haka duk abinda sukayi na bude baki tana dibar masu,taba Aysha hadda kwancen kayanta, dan kayan kwaliya,sabulai da sauran su..

Haka Allawiya idan sunyi abun marmari takan dibar wa jummai.

Hajia ta zayane ma nura duk rashin mutunci da rashin kunyar da jummai tai mata.
Ta umurce shi da ya fita hanyar jummai, dan ba maccen aure bace, duk da tasan yana matukar son jummai,bata hanashi gaisuwar mutunci da jummai da yan gidan su ba,amma maganar soyaya babu shi.

Yace insha Allah Hajia za nayi yadda kikace…

Yayai mayawa mayawa gidan su jummai, sai ace tana islamiyyah,Aysha kuma na gidan alhaji na wudil, haka ya hakura dan ko ya kira wayan daya ba jummai switch off,yana son jin inda takai wayan.

Sai da azumi ya kwana goma, jummai ta kwashi yara suje tashe gidan Hajia.

Sallama sukayi,suka fara wakar

Ke ina zaaki da kaya

Jummai da aka azama kunshin kaya tace.
Kishiya tak koro ni, ko gado ban dauko ba.

Da yake babu wutar NEPA, Hajia bata gane su ba, tace NURA ya dauki sauran kosai,da soyayyen dankalin Hausa,ga naira hamsin ya hada ya basu.

Yana mika masu, ya jaye jummai gefe, yace minti biyar.

Tace kada fa Ku canye kayan nan.

Yace nayi ta zuwa gida ban samun ki,ina wayar nan?

Tace kace wayarka ka biyo, dama ka bani ne dan kamin gori?

Yace bashi na tambaye ki ba.

Tace waya an amshe a makaranta.

Yace what! Dan me zaki schl da waya?

Tace abokai na naje nuna mawa.

Yace ki fadamin sunan mallamin daya amshe dan sai ya bani wayata

Kin San nawa wayar nan take kuwa?
Ko police ina Iya kai masu akan wayar nan,duk wani hoto da lamba mai muhimmanci na cikin wayar nan.

Ta hasala sai me,je ka kira police din mana,ka wani cika Mani kunne akan wata akwalar wayar ka.

Gashi nan cikin littafin Hausa hadda motor saurayi ke saya ma buduwarshi,kayan azumi ne, su kayan sallah da kudin kashewa.

Amma kai wata tsiyar ka taba tsinana min?

Yace ohh ta nan kika bullu kuma, waya sani ko sayar da wayar kikayi

Tace na sayar, nima a sayar dani,talakar banza.
Tace kuzo MU wuce dallah.

Yace ba shaka,daman dan talaka bai Iya samun wuri ba, kamar Shi jummai zata kira da dan talaka, bata dubi kanta ba, zai yi maganinta,ba dan ya dauko police abin ya shafe jummai dole a hada da ita,babu yadda ya iya,dole sai yayi hakuri da halin jummai..

Tana sauri zata Haddar dare, wani mutum yayi ta biyanta yana mallama sallamu alaikum.

Waalaiku musallam,lafia Mallam?

Yace ki bani dama na dade ina sonki, sunana alhaji KABIRU mai shadda, mata na uku.
Walahi duk abinda kika so ina zaka yi miki shiyya,ga babban gida gare ni, akwai motar hawa ta alfarma, umra,hajji dut dake za ana keji Yar diya.

Cikin zuciyarta tace, ga irin mijin novel, amma babu Khan fuska, babu tsari,gashi wani gaba,gara ga tsufa da dukan alamu ma jahili ne.

Tace alhaji KABIRU mai shadda yanzu hadda ZANi,kuma nayi latti,ka bani lokaci inyi shawara.

Yace konni Yar diya kamata aka shawara,walla hi diyata kada kiyi wa kanki tuwon tulo.

Ta kece da daria, lallai jummai zata wanki garra.

Tace sai kazo gida,ta wuce abinta.

Ya cije labba, Allah shi kai damu ga harawa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button