KURUCIYAR JUMMAI Complete Hausa Novel
*HALIMATU SADIYA MUHAMMAD*
*L££MA*????
*@AM££NCI WRITER’S ASSOCIATION*????✍????
*domin samun kayatatun littafan mu a shafukan fcbk Ku tuntube mu a:-AM££NCI WRITERS NOVEL GROUP*????
*25-26*
Ba jummai ba,ba Alawiyyah ba duk sai da hanjin cikin su ya kada.
Tattako wa yake zuwa inda jummai take tsaye,tana ja da baya, yana isa daf da ita ya kasheta mari guda biu masu lfy,ya shake ta,yana fadin azzaluma,muguwa,baqar ashana mai kike yi a gidan nan, ko wata bala’in kika zo hadda sa masu?
Nura dai mamaki ya cika shi,sai BELLO ne yayi karfin halin cewa, haba raji idan rai ya baci bai kama ta hankali ya gushe ba,me wanan karamar yarinyar tai ma da zafi haka, kake bugunta kamar ka samu namiji dan uwanka,pls ka kyaleta.
Ya kalle shi da mamaki,in kyaleta fa kace, akan wani dalili,kasan abinda ta aikata min ne ita da wanan munafukar kawar nata.
Nura yace look,duk abinda tai maka bai dace da zub da girmanka kana irin hakan ba, sanan duk fa abinda ya samu yarinyar nan ni za a kama tunda a dakina suke, kuma ni aka sani.
Yace nura itace yarinyar da nike baka lbr tai min kazafi har aka koreni a wurin aiki
Nura da BELLO salatti sukai, a lokacin Alawiyyah ta bude kofar da Sauri ta sheka ta kira hajia
Hajia tace lfy?
Alawiyyah tace m.raji zai kashe jummai hajia.
Da Sauri suka isa dakin, Hajia tace kai raji sake diyar mutane, duk Ku sameni a palour.
Duk sun zauna a palour hajia.
Tace raji menene ke faruwa?
Lbr yaba hajia tir yan,tir yan yadda jummai ta mai kazafa,da transfer da aka mashi.
Duk mamaki su kai yadda karamar yarinya kamar jummai ta Iya hada makirci haka.
Hajia ta ce jummai haka akayi?
Tace eh hajia
Nura yace kenan kin yi amfani da wayar dana baki Wanda akwai hotunan shi da number shi kika shammace shi?
Tace eh.
Raji yace “no Wonder””har bisa ga yau ina kan tunanen inda ta samu wayan nan abubuwa.
Hajia tace wai ke jummai wace irin shai’daniyar yarinya ce mai hadda sa fitina cikin al’umma,baki da aiki sai tadda zaune tsaye?
Raji da kike gani dan uwana ne uwarmu guda ubanmu guda dashi,kawun nura ne,mahaifin NURA ya riqe shi har ya kare karatun shi, koda mahaifin NURA ya Rasu raji ya CI gaba da daukar nauyin karatun NURA,cin mu, shanmu da duk wani lalurar mu da wanan shagon na dunki da kika gani, shagon dunkin nan na raji ne daya samu aiki yabar ma nura shagon dunki,abinda yasa bakya ganin shi gidan nan makarantar Ku ta bashi wurin zama, nura bai da uba,dan uwa da aboki kamar raji.
Jummai baki kyau tawa rayuwar kiba, bakyi ma nura adalci ba da kika shaga rayuwar shi, domin keba Matar aure bace.
Raji,nura banda abin cewa daya wuce wanan,yanzu hukunci na hannun ku, duk abinda kuka yanke akan ta dai dai ne, amma zan nemi alfarma akan a sasauta mata duk hukuncin da za a yanke.
Jummai kuka take yi wiwi, allawiya na gefe.
Gyaran murya raji yayi, yace hajia na gode da damar da kika bani, tabbas jummai yarinyace,QURUCIYA ke damunta,amma abin lura shine ai akwai yara wayan Dama basu kai shekarun taba amma basu aikata makamancin abinda take aikata wa ba.
QURUCIYAR JUMMAI hauka take gaya mata,tana azza mata girman kai,wauta, kafiya da sauran su.
Nura idan na isa da kai daga yau babu kai babu jummai, dan Baku dace ba at all, ba macen aure bace, nidai na yafe mata da duk wasu ma biyan ta,duk abin da suka aikata a kai na, na yafe masu duniya da lahira, Allah kuma ya yafe mana.
Duk aka amsa amin,banda jummai.
Nura yace insha Allah duk yadda kace haka zanyi,, jummai kiyi hakuri Allah hada ki da miji na gari, amin.
Jummai tace nura,hajia,M.raji Ku yafe min sharin shaidan ne.
Bello yace kuje gida yamma ttayi, an yafe maku.
Allawiya tace mun gode.
Da suka dawo gida, umma tace Allawiya ina kuka tsaya?
Allawiya ta zayane mata abinda ya faru.
Umma tace alhamdulilah,Alllah na gode maka da ka nuna min wanan rana da liqin jummai ya balle, maganin Mara jin Magana kenan, yanzu hankalin ki ya kwanta ai, ni rajin bai cimin goro ba,da bai laqada maki kashin tsiya ba,gashi kin yi rashin masoyi na gaskia,yanzu sai ki auri alhaji KABIRU mai shadda ai.
Ta shige daki abinta.
A kwana a tashi ba wuya har sunyi resuming makaranta.
Yanzu jummai ta mai da hankali a islamiyya har tayi nisa.
Alhaji KABIRU kulum sai hidima yake masu jummai, amma har yanzu ko kallo bai isheta ba.
Su Aysha sun fara zana junior waec, yayin dasu jummai ke jss2 yanzu.
Yau alhaji kabiru yazo hira da kyat jummai ta fita.
Yace yan mata ya kwanan gida.
Tace lfy.
Yace mi’an bayani.
Tace gobe zan kai abinci makaranta na walimar hadda izo biu Dana kamala.
Yace madalla, yanzu mutai kkasuu asamu abinda anka bako ki.
Tace tau, motar shi suka shiga, ya dau bypass na unguwan daji.
Tace naga nan ba hanyar kasuwa bane, ina zaka kai ni.
Yayi banza
Tace ka tsaya nace ko in maka ihun barawo.
Bai tanka taba
Kiciniyar bude motar ta fara yi……….
*L££MA*????
[01/02, 17:01] +234 816 432 1306: ????????????????????????
????????????????????????
*QURUCIYAR JUMMAI*
????????????????????????
????????????????????????
*HALIMATU SADIYA MUHAMMAD*
*L££MA*✍????
*27-28*
Sa’a Allah ya bata ta bude kofar motar, ai gangara wa tai cikin rami,saura kadan tayar motarr ta take mata kafa.
Jan murfin motar shi yayi,yace ko mutuwa kika yi Yar banza banda hasara, ya kara gaba.
Cikin tulin bola ta fadi Tim,duk ta kukuje, tayi ma alhaji KABIRU Allah ya isa yafi a kirga, haka ta rarafa har ta haura saman titi, gashi bypass ne akwai qarancin abin haka.
Ta jima wurin sosai gashi magrib ya gabato, can ta hango mai adaidaita tun daga nesa ta fara daga mashi hannu, tana zaune gefen titi.
Yana isowa ya taka burki tare da fadin,wainnahu,sulaimanu wainnahu,bismillahir rahmanir rahim,Ku kuke ganin mu bamu ke ganin kuba.
Tace dallah malam mutum ce ba aljan ba, taimako na za kai ka kaini gidanmu.
Yace inane gidanku?
Ta mashi kwatance,yace muje.
Da kyar ta Iya shiga napep din.
Har kofar gida ya kaita, godia tai mashi ta shige gida.
Baba ya wuce masallaci,umma ce zaune saman tabarma tana tankaden garin alkama da zata yi tuwo.
Tace ke ke ke!
Daga ina?
Ta fashe da kuka, tare da zayane ma umma duk abinda ya faru.
Umma tace Allah ya qara,ke mai son banza ko,kinga kamar bai San abunda yake yiba bara ki wanki garra,ai gashi nan ya nuna maki halinsa.
Tace haba ummata,yanzu laifina kike gani,ko tausayina bakya Ji,yanzu da mutuwa nai fa?
Dama BABA na kawai ke sona, ta shige daki.
Umma tace Allah shirye ki,mazza fito ki Debi ruwan zafi kiyi wanka ki gassa jikinki kiyi sallah.
Dole ta fito ta hada ruwan wankan ta shige toilet wanka sosai tai tare da kakasa inda ta kuje, sanan tai alwala.
Sallah ta gabatar, tana idar wa ta dauko Qur’ani tai tilawar hadda kafin lokacin isha’i tayi.
Umma ta gama tuwon alkamarta da miyar danyar kubewa,wanka tayi ta gabatar da sallah,tana zaune tana lazimi Aysha tai sallama.
Tace sannu umma,ya gida,nabarki da aiki,har yanzu jummai bata dawo bane?
Tace ai na gama aikin tun dazu,ya kika baro nafisar?
Tace lfy lau,taji dama sosai.
Umma tace kinji abinda alhaji KABIRU mai shadda yayi ma jummai?
Aysha tace ikon Allah,Ashe datijon banza ne,Allah ya fishi dama nasan duk hidimar nan da yake yi Ashe da wata a kasa,inna jumman?
Tana daki
Shiga dakin Aysha tai tace jummai Ashe abunda ya faru kenan?
Allah tsare gaba.