HAUSA NOVELKURUCIYAR JUMMAI Complete Hausa Novel

KURUCIYAR JUMMAI Complete Hausa Novel

Tace tau munafuka,ina ruwanki,Allah ya tsare abinda yafi haka ai, dan tsabar GULMA da iyayi ki wani jawo gwanjan jikin ki kizo wai wai Allah kyauta,walahi duk naji maganan nan ya fito cikin UNGUWA walahi keshe kuma ban yafe ba.

Tace yanzu ni kike fadawa haka,shekara 6fa na baki jummai,Allah shirye ki.

Tace sannu sarkin son girma,CI goro cikon benci tabarman kada chacha.

Tace jummai muje muci abinci.

Tace tare muka saba ci, wanan wanan sai anyi kini babban mace,tau da baba na zan ci.

Bayan sallar isha’i baba ya dawo masallaci,umma tamai shimfuda,ta gabatar da abinci.

Zama jummai tai suka fara cin abinci, bayan sun gamane,ta kwashe kwanan.

Umma tace babansu KAJI KAJI abinda alhaji KABIRU yai ma jummai.

Yace subhanallah,wanan ai rashin sanin darajar dan Adam ne,yanzu dama haka yake?

Umma tace waya sani, Allah dai ya qara tsare gaba. Amin

Ranar asabar da misalin karfe 9am aka gabatar da walimar saukar al-Qur’ani mai girma a harabar madarasatul nurul Islam,Wanda ya samu halartan dunbin jama’a ciki hadda Hajia,nura, bello,Muhammad tare da M.raji.

Dalibai ashirin da biu sukai sauka,mata goma,maza goma sha biu.
Cikin matan hadda jummai da allawayi.

Ko wane dalibi yayi karatu cikin natsuwa,bayan sun gamane akai rabon kyaututuka.

Wa’azi da nasiha sosai babban malamin su yayi akan suji tsoron Allah tare dayin aiki da abinda suka karanta.
Su hajia suma sun isko su jummai har wurin zaman su tare da bada tasu gudun mawar kunya sosai jummai taji,m.raji yace Allah yasa anyi na tsoron Allah,suka wuce

Haka taro ya watse kowa sai Sam barka.

Anyi resuming schl yanzu su jummai an shiga jss2
Aysha result na junior waec ya fita, boarding schl taci”government girls secondary schl kontagora”(GGSS)

UMMA bata so haka ba, baba yace tai adu’a Allah yasa haka shiyafi alheri.

Ta amsa da amin.
Dan abinda baba yake da,dashi akayi sayayan zuwa schl na Aysha, akai ma jummai Sabin uniform itama.

Komi ya kamala da izinin Allah,ana gobe zata wuce nafisa tashigo ban kwana,kayan tea da hadaden dakan yaci ta kawo ma Aysha.

Sosai umma taji dadi tare da saka mata albarka.

Tace babu komi umma yiwa kai ne, cikin wasa tace dama jummai aka kai makarantar kwana.

Daga cikin daki jummai ta daga murya,tau mazuga maqongwara masu zuwa lahira da qoqon danbu a hannu,ba a kaini ba ke sai ki daukeni ki kai ni, karamar yarinya dake kin Iya munafunci,ko da take naga ba laifin ki banne, na iyayenki ne da suka maki aure da wurin, meke cikin buzaye banda zallar yunwa da warin dirty, wai har ke, kike kawo ma wasu kyautar abinci.

Umma tace wanan wanan Allah ubangiji ya aiko maki da mala’ikar shiriya.amin
Tace dan Allah nafisa kyi hakuri fa.

Tace babu komi umma sai da safe,Aysha Allah bada sa’a yasa aje cikin nasara.

Tace amin nafee,nagode sai da safe.

Da safe Aysha tai sallama da yan unguwar su,baba da kanshi ya kai ta har schl, bayan an gama komi har an bata hostel.

Nasiha sosai baba yayi mata,tana kuka suka rabu.
[01/02, 17:09] ‪+234 816 432 1306‬: ????????????????????????
????????????????????????
*QURUCIYAR JUMMAI*
????????????????????????
????????????????????????

*HALIMATU SADIYA MUHAMMAD*
*L££MA*✍????

*nagode sosai da adu’ar Ku masoya,masu kira a waya, masu massege dama wayanda suka kawo min ziyara da wayanda basu ma samu dama ba,baba yaji sauki sosai insha Allah yanzu komi normal*

 

*29-30*

 

Suna tafia suna hira har suka kai karkashin gada,tun suna ganin mutane har suka fara shiga gona ki ta titin jirgi suna faman ratsa gona ki,sunyi nisa sosai,allawiya tace qishin ruwa Nike jifa,jummai tace mun kusa kai wa rafi ai sai musha.

Allawiya tace nidai bazan sha ruwan rafi ba cholera ya kama ni.

Har rana ta fito sosai suna abu daya, da kyar suka tsalaka rafin da zai sada su da unguwar padukway.

Da tambaya suka gane gidan,koda suka shiga dakuna duk a kulle sukai ta gwada sallama shiru, wani yaro suka gani zai gilma ta wurin gidan jummai tace kai ina masu gidan nan?

Yace ai sun tashi a gidan sun koma tudun fulani.

Jummai tace amma Allah ya mana baqar isa ga diyar shegiyar nan hadiza, dama sun bar unguwar nan bata taba gaya ma kowa ba yayi, Allah hada MU a makaranta.

Allawiya tace ni bama wanan ba qishin ruwa ke mugun damu na,yanzu ina zamu samu ruwan sha?

Tace oho.
Duk sunyi butum butum da qura.

Allawiya tace inada naira ashirin cikin Jakata ko ruwa masha.

Jummai tace amma anyi muguwar diya,yanzu dama kina da kudi kikai mirtsitsi aka sha rake da nawa,dan tsabar maqo kika qi fitar da naki ko?

Wallahi ba’a sayan ruwa bus zamu shiga zuwa Mobil Ku qarasa gida qasa.

Tace ke jummai nifa man cewa nai inada kudi.

Tace koma dai menene bus za MU shiga.

Kuda suka isa bus stop,bus ta cika dole saman engine suka zauna gashi ya dau zafi sai suya yake masu a mazaunin su.

Jummai tace kyale nida shege ko sisi bara MU biya ba.

Koda Karen mota yace su bada kudi jummai tace ai ba gudu zasuyi ba ya bari har su isa mana.

Ana isa Mobil suka arce.

Jummai tace mu biya rumfar baba na

Tace tau.

Kona suka isa,jummai ta gaida mal.hassan makwacin baba,yace dama makaranta kuke haka?
Alawiyya tace eh
Yace Baban Ku na masallaci Ku jira shi.

Suka zauna.
Can baba ya dawo, yace sai a yanzu aka tashi makarantar?

Jummai tace baba komi bamui ba a makaranta, gidan kawar mu muka je kuma basa nan.

Yace gashi babu kasuwa yau naira dari nayi,fura da nono da aka damu mashi ya basu

Bayan sun gama sha suka sha ruwa.

Yace kuje gida duk abinda na samu zan kawo anjima.

Jummai tace mu biya masallacin yarbawa mui sallah.

Koda suka isa an idar da sallah,alwala su kai,suka shiga massalaci,bayan sun idar da sallah.

Jummai tace allawiya ina ma nan ne gidanmu, ga tiels ga fanka kamar an kuna AC,ni sai nayi bacci ma kafin

Allawiya tace walahi sai dai mu hadu gida, nikam na gaji ko yunwa bakya ji idan kika samu yawo.

Tace kai alawiwi,muje dai.

Suna tafia har sun kai kasuwar gwari suka hango cinko son jama’a.

Jummai tace ke mu leqa mu gani.

Koda suka rutsa mai wasa da maciji so ka gani.

Jummai tace shege azzalumi,mushiriki,maketaci kawai ya Tara mutane sai cin amanar su yake yi,wai maganin farin jini, arziki,ilimi Dana budin kasuwa.

Ke allawiya mu wuce idan ba haka ba walahi sai na watse taron nan.

Suka kama hanyar gida.

Motar alhaji KABIRU mai shadda ta gani, cikin ranta tace masha Allahu yau zan rama qetar Daka min tsohon najadu.

Tace allawiya yita duba min idan babu mai zuwa wani muhimiyar aiki zanyi.

Tace tau Maryam salis cika aiki.

Ta Ciro compass cikin mathematical set na allawiya,dan ita bata da arzikin shi.

Ta duqa kamar mai bidan wani abu ta hude tayar gaba dana baya duka.

Tace na farko kenan saura na biu,yadda na mulmula cikin yashi, kai cikin kwata za kayi iyo da motar gaba daya.

Sunzo gitawa ta shagon nura ta tsaya.

Tace ina wuni mal.nura.

Yace kwana biu Mallama Maryam ya karatu.
Allawiya tace alhamdulilah.

Jummai tace in kawo dunki?

Yace sai ki zo.

Tace ina gaida Hajia.

Yace zata Ji.

Suka isa gida, qanzon tuwon masara umma ta gyara yaji alayahu da man kyada.

Tace jummai Allawiyya yanzu sabi da Allah sai yanzu kuka ga daman dawo wa?

Da safe har PZ naje kai nikar masara, makarantar Ku rufe babu kowa
Daga ina kuke.

Jummai ta fada mata.

Tace yanzu da Ku dawo gida kuna kama mana aiki Ku samu lada kun gwamace kui ta gantali cikin gari, har dabi ta titin jirgi matatarar yan shaye shaye da barayi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button