KURUCIYAR JUMMAI Complete Hausa Novel
*31-32*
Mallam salis da Saratu sun kasance yan asalin qauyen mahuta ne,karamar hukumar fakai dake kebbi state.
Almajiran ci ya kawo shi niger state,minna,daga haka har yayi uban gida alhaji mande yana masa tsaron shagon zanuwa,lesuka,takalma da jakuna.
Mallam salis mutum ne mai amana,hakuri,riko da gaskia,shiya sa zaman sa yayi dai dai da alhaji mande.
Yana da shekaru goma a minna,dai dai da shekarun haihuwar shi 25.
Yaje ganin gida, lokacin Allah ya hadashi da Saratu suka dai daita Kansu akai masu aure ya dawo da ita minna.
Saratu wadda yan uwanta ke kira da “”qade”” ita guda mahaifiyarta ta haifa, bata da yan uwa na ciki guda sau yan zuba
Cikin gata ta taso, Mace kyayawa mai natsuwa da alkunya,karatun allo kadai tai.
Alhaji mande ya mallaka masa madaidaicin gidan da yake ciki har yanzu.
Gidan daya kunshi dakuna biu da palour
Daki guda da bam,shine na mal.salis katuwar katifa tun na samarta kanshi ke ciki,akwatin kaya saida table mai dauke da tulin littafan addini.
sai ciki da palour a gefe nan ne na umma,babu komi ciki sai 3 seater a palour leader carpet,shima Matar alhaji mande ta basu,cikin dakin kuma gado ne 6/7 na silver irin na da sai dressing mirror.
Toilet na wanka da bayan gida hade yake shima a gefe sai madaidaicin kitchen.
Haihuwa uku tana yi duk basu tsaya ba,sai a kan Aysha wadda taci sunan mahaifiyar umma.
Cikin gata Aysha ta taso, yarinya kyakyawa mai hakuri tun tana qarama bata da kwaramniya,fara ce tas, siriri mai Yar karamar jiki,irin na mahaifinta.
Sai da Aysha ta shekara 6 aka samu cikin jummai.
Murna sosai mal.salis yayi.
Umma kam ansha fama da laulayi,sai da cikin yai wata biyar taji daman laulayin.
Ranar jumma’a da dare umma ta tashi da naquda sosai,gashi ana zabga ruwan SAMA kamar da bakin kwarya,garin dif babu wutar nepa, wasu gidajen duk iska ya yaye masu rufin gida,wasu Katanga ta zube, ga pole’s na wuta sun fafado.
Haka umma ta haihu a galabaice.
Kowa dai yasan jinjirai farare ake haihuwar su.
Amma jummai baqa wuliq aka haife ta,gata barakallah,fuskar ummanta San
Kyakyawa,mai duguwar hanci,sai kananan idanu, baki madaidaici,sai ci ga fitinar tsiya.
A washe garin ranar central market minna ta kama da wuta,duk manyan shaguna sun qone,ciki hadda shagon alhaji mande.
Da ya samu labari stroke ya kamashi akai hospital dashi,washe gari yace ga garin Ku.
Haka akai zaman makoki,ranar suna kasan cewa hankali ba a kwance yake ba,kuma ana cikin halin rashi, a masallaci aka rada suna””MARYAM””sunan mahaifiyar mal.salis ake mata lakabi da jummai
Ko taron suna ba ayiba.
Bayan kwana arba’in aka raba gadon alhaji mande,an barma mal.salis gidan da yake ciki kasancewa margayi ya rigada ya malaka masa.
Yanzu kam mal salis komi ya qare masa, dole hayar rumfa ya kama central market minna yana sai da kayan koli,dunkin takalmi da sauran magungunan gargajiya na itace.
Jummai ta taso cikin rashin ji, gata kazama duk yadda akai mata wanka sai ta bata jiki ta,Jan fada,gashi bata son karatu ko kadan.
Tun suna yara Aysha ke masu wanki ta gyara gida.
JUMMAI akwai son yawo,duk inda ake buki tana can,haka duk gidan da akwai TV can take yini.
Shiyasa abotansu yayi karfi da alawiya duk cikin yaran unguwar.
Tare aka kai su IBB primary schl ajinsu daya har izuwa yanzu.
*CI GABAN LABARI*
Su jummai an zama vice ameera sai cin zalin diyan mutane ake,Idan an tara kudin sadaka na MSS jummai ta aika fanke wurin kutimi mai fanke.
Yau an tashi break, ita da alawiyya suka haye saman window sai gulman teacher’s sukai
Duk wadda ta gifta sai anyi gulmanta.
Jummai tace allawiya Kali maths teacher yau English wears yasa
Allawiya tace dan izala ne fa,kullum cikin shadda.
Jummai tace ai ko yanzu ya nade kafar wandan.
Suka sheke da dariya tare da tafawa.
Tace alawiyya yau 12pm zan wuce gida,sabida last period copper Elena muke da.
Ni bazanyi attending ba dan walahi ko turanci bata Iya ba, talk less of teaching.
Allawiyya tace shegu sai aukin neman mata.
Jummai tace duk yan warin mu nefa.
Allawiya tace dadina dake son girma kamar gyambo.
Suka CI gaba da hiran duniya.
Su jummai an fara hankalinsu,ana kama ma umma aiki kuma an rage yawo.
Samara caa su kai mata, amma sai wulakanta su take yi.
Salamu alaikum
Ahh nafisa ce sannu da zuwa,ya kwana biu,ke ke tafe da ranar nan ga tsohon ciki?
Tace eh umma,ya gida.
Lfy lau nafisatu,kinga Yar banzan yarinyar nan jummai kona turata ta dubo min ke sai taqi zuwa.
Tai murmushi babu komi umma,ana jin labarin su Aysha ko?
Lfy lau suke, Baban nasu ma yace wani shekara data shiga aji biyar za tai jarabawa da yan aji shida tunda tana da kokari.
Tace Allah taimaka.
Dama umma TV na Bango na yayi alhaji ya saya mana shine nace ko kuna son karamin?
Umma tace idan babu matsala Yar nan ai munfi kowa bukata ko dan jummai ta huta yawon Bin Gidajen mutane kallo.
Tace bara an ba almaJirina ya zo ya hada maki.
Godia sosai umma tai mata
Haka ko akai yazo ya hada masu sai ga NTA minna channel 10 ya fara ana gabatar da shirin””BABA RAMUTA “”
JUMMAI na dawo wa islamiya tace umma ke kika sai TV ko Baban Mu?
Tace nafisatu ta bamu.
Jummai tace cab sai an mayar mata daabinta salan ta rena MU,tana kokarin cicibar TV…..
c
*47-48*
HAJIA tace nura ya rasu aysha lokaci yayi sai adu’a
Sallati aysha keta maimaitawa, jummai ko jugum tai kamar Matata domin mutuwar yai mugun tabata.
Aysha tace dama yai rashin lfy ne?
Wata yar uwar hajia tace yadda abokanshi suka bada labari lafia lau suka yini cikin dare matsanai cigar ciwon ciki ya tadda shi daga bacci kafin su isa asibiti nura ya cika da kalmaar shahada tare da neman gafarar Kowa.
Hajia ta kara fashewa da kuka tace nura ya tafi ya barmu da kewar sa,ya bar dan uwansa cikin matsanaiciyar tashin hankali domin raji haihuwar nura ne kawai bai Yi ba amma duk wani abu da iyaye kan ma dansu raji ya na nura babu irin gata da kulawa da Bai bashi ba ashe kwana kinsa ragagu ne.
Talatu yar uwar hajia tace bari ai raji na cikin tashin hankali domin yayi babban rashin dan’uwa kuma amini.
Hajia cikin kuka tace ina kika san yana cikin tashin hankali ma Wanda tun jiya da aka dawo da gawar nura idan banda kuka babu abinda yake yaki ci,yaki sha yaki magana da kowa ko gaisuwa aka masa bai iya amsawa sai kuka har yanzu aikin kebab.
Aysha tai nanauyar ajiyar zuciya tace haka ne hajia idan lokaci yayi babu Wanda ya isa ya hanaka tafia,duk wani kuka, rashin cin abinci bashine zai kawo saukin radadin da muke ji a zukatan mu ba aduar mu kawai ita yake bukata, kuma itace gatan da zamu masa a matsayin muna masoyan shi.
Hajia tace haka ne Aisha, jummai dai jugum tai duk gabobinta sunyi sanyi nura take gani a idanunta, tare da tuna moments din da sukayi spending tare lokacin tana cikin QURUCIYAR ta.
Adu’a sosai aysha tai aka shafa,tace jummai muje gida magrib ta gabato,mikewa tai jiki ba kwari bata ce da kowa komi ba ta kama hanya.
Hajia tace jummai ai hakuri tabbas keda raji akai ma mutuwa amma sai kun daure Kinji?
Daga kai kawai tai,suka kama hanya.
A kofar gida maza har Sun fara always, raji suka gani daga can gefe misa dakali zaune da buta a gabanshi da dukan alamu alwala zai amma ya tsaya shiru sai hawaye ke tarara a kyakyawar fuskar nan nashi.