KURUCIYAR JUMMAI Complete Hausa Novel
Jummai ta nufi wurin shi kamar tababa maza sai kallonta suke,aysha kuma bata ma Ankara da abinda jummai tai ba.
dukawa tai a gabanshi tare dayin tagumi hanu nabiyu, kura mai ido tai tare da zub da hawaye, tace uncle; nura ya tafi ya barmu adu’a zamu bishi da ita domin itace kawar gatar da zamui masa a matsayinmu na masoyan shi.
Kura mata idanu yayi kamar mai nazarin wani abu,hannuwanshi biu ta rike gam tana zub da hawaye kauda kai yai yana kallon wani gun,ta kara matse hanuwanshi cikin nata tare da cewa uncle pls say something I can’t bear to see u in pain,uncle kai ne farin ciki na pls look into my eye and promise me that everything will be alright,uncle plsssss talk to me”cikin matsanaicin kuka.
Aysha tazo ta jayeta,tace manene haka sister ki dawo cikin hankalin ki,baki ganin mutane na kallon ku, ki barshi yaji da abunda ke damunshi mana.
Tace haba sister u won’t understand,na fishi shiga damuwa ta dalilin Halin da yake ciki.
Aysha tace haka ne jummai amma ba lalai bane ki fishi damuwa tunda shi jininshi ya rasa,ke kuma masoyi kika rasa.
Tayi murmushin yake tare da cewa sister shiyasa nace u won’t understand,bani da masoyi duk fadin duniyar nan sama da uncle, tunda na malaki hankalin kai na na tsinci kaina cikin soyayar shi dumu dumb, tun ban gasgata kai nava ina tunanin zuciyata yaudara ta kawai take Yi, ashe ba haka bane, kullun kwanar duniya da tunanenshi nake kwana nake tashi,nasan na aikata abubuwa da dama lokacin QURUCIYA ta amma yanzu na gane gaskia nayi nadama mai tarin yawa sister ki taimake ni kada son uncle ya halaka ni.
Aisha tace u better wake up from yr fake dream,kin manta dangan takar dake tsakanin nura da uncle NE?
ko kin Manta soyayar da kikai da nura dacan baya?
ko kuma manta wa kikai da irin rashin mutuncin da kika shuka masa lokacin baya?
Tace dangantaka!
Ai ba aurena nura yai ba,kuma addini ya yarje ma uba da da su nemi mace guda aure duk mai rabo ya dauka,bare ko aure na nura yai muka rabo Uncle na iya aure na.
Maganar soyaya kuma niban tava son nura ba duk da ina cikin QURUCIYA ya nemi soyayata bai samu ba bare yanzu dana mallaki hankalin kai na.
Abunda ya faru tsakanina da Uncle kuma ai QURUCIYA yasa na aikata hakan, sanan kada ki Manta sister ko Allah muka ma laifi muka tuba zai gafarta mana Bale Dan Adam.
aysha tace so serious, nidan kinga tafiya ta tunda baki da hankali.
Finciko jummai yai ya tatare hijab nata ya hada da wuyanta ya matse;yace kina hauka NE, dan tsabar rainin wayau saw rashin hankali ki dubi tsabar idanu na wai ni kike so,dan baki da kunya a gavana kike fadin baki son dan uwana wanda ya bar duniya ina cikin bakin cikin rabuwa dashi?
Walahi jummai OR what ever u call yrself na tsane ki,na tsaneki bana son ganinki,bana kaunar kids, bazan taba sonki ba wawiya dakikiya kawai mara imani da tausayi…
Aisha tace
uncle pls kada ka biye mata yarinyace na roke Ka da girman Allah Ka kyaleta plz.
Yace Aisha i hate this girl walahi, I hate seeing her around me ever since that incident occur,daurewa kawai nake ina kyautata mata all this while sabida yar uwata ce musulma.
Magan ganunshi yai ma aysha ciwo kwarai daurewa tai taja hanun jummai domin Jana’s sun fara fitowa masallaci kada a fuskanci abinda ke faruwa.
Jummai na turjewa, aysha na qara jan hannunta da zuciya ya dibeta wanke mata fuska tai da mari mai lafia tace kwakwalwar ki ya tabu ne?
Ko kin fara shan wani abu ne, namiji yace ya tsaneki bai son ganin ki dole ne ko shi daya ne namiji duk fadin duniya?
Kamar ki da kyan ki,assali da iliminki har namiji zai fito promp and clear yace yayi hating nake and u are stil wasting yr precious time on him, dallah mu tafi gida to hell with him.
jummai tace sister allow him to kill me, tunda bai son ganina amma walahi bazan bar sonshi ba kuma idan kaga bamui aure ba Allah ne bai nufa ba…
Haka aysha ta rinka janta har suka isa gida,umma tace lfy tun bayan LA’asar sai yanzu?
Aysha da zuciyay ya kai mata ko ina cikin bacin rai tai ma umma bayani tun daga kan mutuwar nura da suka isko har rashin hankalin da jummai tai wurin m. Raji.
Sallati UMMA tai tace Ashe nura lokaci yayi Allah bai nufa yaci muriyar karatun da yayi ba,Allah masa rahama yasa can ya fiye masa nan,yakai haske kabarin sa Amin.
Amma jummai banji dadin abinda kika aikata ba a bainar jama’a kamar ba mace mai hankali ba,haba ina iliminki,tarbiyar ki da natsuwar ki jummai?
ta fashe da kuka umma ya zanyi da rayuwata, na dade ina dakon soyayar shi UMMA, gara na fada mashi gaskia yafi min, dama option biu ne,either ya amince da soyayata ko kishiyar haka.
Tau jummai lalai kina cikin tsaka mai wuya Allah mana jagora kici gava da adu’a kinji auta ta.
Tace umma pls kada kuga laifina bani na daura ma kaina sonshi ba Allah ya daura min.
Aysha tace na fahimce ki sister zan tayaki da adu’a, suka rungume Juna,aysha tace see u ba kunya ni yayar ki naki ydda da soyayar kowa amma as little as u are kin san soyaya silly girl????
Daria jummai tai,umma tace bana Son kowa yasan da maganar nan hata baban ku,mu barshi tsakanin mu kunji?
Suka amsa tace kuje kui sallah kuxo kuci abinci…
Suka Mike zuwa daki,jummai ta Dade cikin sujada tana kwararo adu’ar neman zabin Allah akan soyayar ta da uncle daga karshe tai ma NURA adu’ar neman rahamar ubangiji..
Shawar wari aysha ta bata akan yada Zata shawo kan uncle cikin ruwan shanyi.
Sosai jummai taji dadin shawarwarin yar uwarta.
Da safe bayan Sun gama karyawa Baba yace zai tafi wurin amsar gaisuwa daga nan zai wuce kasuwa,umma ma ta shirya ta shiga gidansu Allawiya ta fada ma mamar su allawiyay ko zta samu daman zuwa suje tare gaisuwar anjima.
Jummai tace sister ya kamata mu shirya muje wurin ansar gaisuwa.
aysha tace kin mance shawarar dana baki jiya ne akan ki nisanta kanki da nura duk hanyar da kika san zaku hadu ki gujeta, kada ki sake mashi text ko kiranshi ta haka rai fara damuwa dake kuma yasan muhimanci nki.
Tace anya kuwa sis zan iya?
Tace insha Allah zaki iya,yanzu sai ranar adu’ar uku zamu koma.
Tace tau.
Bayan kwana uku suka shirya zuwa gidan hajia,hijab har kasa aysha tace jummai ta saka da nikab,sanan ba tare zasu shiga ba yadda idan yaga aysha ita guda Zai tunanen abinda ya faru ranar ya hana ki zuwa.
Tace yr wish is my command sis,suka tafa.
Jummai na gaba Aisha baya har suka isa kan jummai na qasa ta shige gidan,aysha kuwa hadda dukawa tai ma mazan waje gaisuwa,raji ko kallonta bai ba,duk da ranta ya baci haka ta daure ta shiga ciki.
Bayan gaishe gaishe suka nemi wuri suka zauna har su UMMA suka shigo lokacin aysha tace bari su koma gida tunda umma ta shigo,zasu fita ne shi kuma yana sauri ya shigo su gaisa da su umma yayi Karo da jummai tsaki yayi yace wane irin rayuwa Jeanne mutane kuna tafia baku kallon gabanku, ga wani tsumma da kika rufe fuska dashi tun kina yarinyarki useless ya shige gida.
Jummai hawaye ta fara yi suna tafia ta ce sister kin gani ko da gaske nefa Man din nan yayi hating dina cikin ma bai ga fuskata ba yake wanan bala’i inaga ya gane nice?
Aysha tace take it easy sister with time komi zai dai daita.
Haka jummai taci gaba da daurewa,duk wani kissa Da kisisina da mace Zatai ta mallaki zuciyar namiji jummai taji har ta gaji ba sa’a,raji sai wulakanta jummai yake duk ta kirashi zagi da cin mutunci,idan a hanya suka hadu the same thing,yanzu ko zai zo gaida su umma sai ya daidaici jummai bata gida,ita kuma UMMA bata taba nuna mashi tasan abunda kenan ba.