HAUSA NOVELKURUCIYAR JUMMAI Complete Hausa Novel

KURUCIYAR JUMMAI Complete Hausa Novel

Admission din su aysha ya fito alhamdulilah taci weeding exams,takai duk wani kudi da ake bukata cikin ikon Allah Sun vata uniform da department”medical laboratory technician””diploma ne for 3years,kullum taje a taxi ta dawo a qasa,wata rana ma qasa take zuwa.

Tunda ta fara schl Samari sukai mata caa,students,leacturee da masu tare ta a hanya amma taki sauraren kowa sabida karatun ta tasa a gaba….

Da yake su jummai na hutu,idan aysha ta wuce schl sai duk taji gidan babu dadi yau dai shiryawa tai zuwa gidan allawiya, domin tunda aka kaita jummai vata sake zuwa ba.

Kwana Kin baya allawiyar ta kawo ma su ziyara wanda mijinta ya kawo ta sai yatsine yatsine take yi,ta kara fresh Hutu ya zauna.

Jummai tace allawiya wai ya maganar komawar ki makaranta ko secondary schl ki samu ki kamala.
Budan bakinta tace ai ana karatu ne Dan a samu abin digaro da akai,ita bata bukatan komi duk wani abu da diya Mace ke bukata mijinta na mata ita bata da matsalar komi..
Shine fa ya so zama masu fada da jummai sabidaw tana fada mata fascia, allawiya tace bakin ciki take mata taga ta samu inda zata huta ita ko mashinshiniu bata da,daga ita har yayarta….

Yanzu ta gama shiryawa kenan taji tsayuwar mota a kufar gidansu,tana dubawa taga Amina ce.

Da gudu ta rungume ta, tace Best friend shine ko ki kirani kice zaki zo?

Tace bari kedai muna zaune da mami nce yau gidan ku zan yini shine fa tasa driver ya kawo ni.

Tace ai kin kyauta yasu mamin?
Tace lafiya lau.

Tace ina su umma da anty aysha?

Tace umma sunje gidan buki ita da maman su allawiya, sister kuma Sun fara lecture.

Amina tace na tayata murna Allah nuna mana lokaci muma.
Jummai tace amin,ai da baki sameni ba danshirin zuwa gidan allawiya nai.

Tace wanan mara kunyar kawar taki,wait naga duk kin rame menene matsalar ki Best friend.

Jummai tai shru

Tace kodai mutuwar nura ne ya razana ki haka?

tace kedai bari akan Uncle ne,ta kwashe komi ta fada ma Amina.

Amina ta hasala

Tace to hell with him,shidin me takalan banza Wanda tsiya tai mashi kaka gida,idan banda kaddara me zaki Yi dashi?

Tace haba bestiy walahi Allah ya daura min sonshi fa ‘I can’t do without him ne.

Tace u too funny bestiy kamar raji kike ikirari baki iya rayuwa ba dashi ba?
Tacee did u know the worse part of it?
Yanzu mafa avoiding dina yake Yi,ga sonshi kullun karu wa take cikin zuciya ta.
V
Amina tace sha kurumin ki Zane baki wani adu’a ayar al-qur’ani ce duk kika karanta shi sau bakwai, a duk karshen ayar ki ambaci sunan raji da iyayenshi walahi walahi walahi ko sarauta dunguru gum ke Samar kansa dan girman kai walahi sai ya soki,so na fascia mahaukacin so Wanda bai taba ma kowa irin sa ba shida Kansan zai kawo kansa wurin ki………

 

*LEEMA*✍????

*BRILLIANT WRITERS ASSO*…????

????????????????????????
????????????????????????
*QURUCIYAR JUMMAI*
????????????????????????
????????????????????????

*HALIMATU SADIYA MUHAMMED*
*LEEMA*✍????

 

*49-50*

 

Jummai tace da kuwa nafi kowa farin ciki idan har uncle da kansa zai furta kalmar so a gare ni.

Amma kuma ya sahihancin adu’ar?

Amina tace ace maki ayar al-qur’ani har wani sahihanci kike nema kuma?

Tace yi hakuri bestiy kinsan gara kayi bincike sabida shirka tafi ko wani laifi girma a duniya.

Tace haka ne best friend ga aduar kamar haka;-fala yahzunka qauluhum inna na’alamu ma yusiruna waMa yu’ulinun(sai sunan shi)
Haka zaki maimaita har sau bakwai.

Tace masha Allah kamar nasan ayar cikin suratul yaseen.
Tace eh cikin suratul yaseen yake aya ta saba’in da shida(76)

Tace godia nike Allahu yabar kauna da aminci besty.

Tace haba ai yiwa kai ne.
Suka ci gaba da hiransu na duniya har umma ta dawo suka gaisa da amina.
Tace amma jummai baki da kirki haka akeyi kin bar diyar mutane da yunwa sai hira kuke yi.

Amina tace umma ai ban jima da zuwa ba kuma sai zuwa anjima zamu dafa indomie.

Umma tace aikin kenan kullum indomie,idan kukai aure ya zaku qare da maza jenku?

Jummai tace kai umma ai zamui masu abinda suke so.

Tace Allah nuna mana lokaci.
Suka amsa amin umma.

Sai 30pm aysha ta dawo nan jummai ke bata labarin shawarar da amina ta bata.

Aysha tace insha Allah amina zatai kokari ta gwada Allah dai ya mana jagora amin.

Bayan sallar la’asar driver ya dawo amina tai masu sallama,tsara umma ta bata na danyar masara,danyar gyada da mango.
Sosai amina tai godia dan abubuwar da tafi so kenan.

Tace tau besty sai munyi charting ko?

Tace ina gaida mami dasu anty duk abinda ake ciki zan fada miki.
Haka amina ta wuce suna daga ma juna hannu.

*WACECE AMINA MUHAMMED*?

Diyace a wurin ambassador muhammad kere da hajia sadiya muhammad kere.
Asalin su nufawan lapai ne a niger state,aiki ya kawo su cikin minna,diyansu hudu guda ya rasu.

anty khadija ce babba tayi aure tana kaduna nurse ce danta guda iziddine,sai bros aliyu yana zaune a cikin minna a federal high court yake aiki matar shi balki da diyansu biu safna da humaira,sai amina,sai yusuf daya rasu.

 

Jummai ta maida ayar da amina ta bata a matsayin abin fadin ta kullum cikin karantawa take tare da ambatar sunan raji hade dana mahaifinshi,amma shiru har an share sati babu shi babu labarin,sosai take kai ma hajia ziyara tana debe mata kewa,duk wani aikin gida ita ke mata amma bata ganin raji.
Har dai ta gaji ta tambayi hajia,tace mata ai ya tafi south africa course na 6month.
Haka jummai ta dawo gida jiki ba kwari.

Tace umma ashe uncle tafia yayi?

Umma tace eh yazo yai mana sallama ai kuna islammiya ranar.
Tace amma umna shine ko ki fada mana?
Tace kona fada maki maganin me zai maki,sai ma tashin hankali da damuwa da zaki sa ma kanki.
Tace babu komi Allah na nan.

Umma tausayin yar nata ne fil cikik ranta,ta rasa wanan irin bakar kaddara,ace kamar jummai wai namiji zai nuna ma kiyaya,tafi aysha kyau,dira da tsarin jiki hasken fata kawai aysha zata nuna mata.

Ban garen raji kuwa tafiyar a vazata tazo mashi unexpectecd aka kirashi akan yada daya daga cikin wayanda kwamnatin kasar ta zaba zuwa south africa course kuma 3days aka basu suyu duk shirin da zasui na tafia.

Da zai tafi hajia ta nuna rashin amincewarta a cewarta ta hanyar karo karatu a wata uwa duniya ta rasa tilon dan ta nura,yanzu vara ta bara guda gudan kaninta ya tafi har south africa karatu ba.
Da kyar ya rarasheta ta amince domin taso ace ya fitar da mata idan ya dawo ayi batun aure tunda shi daya take da dan’uwa da suka fito ciki daya gashi iyayensu sun dade da rasuwa.

haka ya lalabata ya samu ya tafi da alkawarin idan ya dawo zai kokari ya fida mata.

Yana kwance a hotel din da aka sauke su bayan ya dawo lecture duk kwana kin nan tunanen jummai yake yawan yi,ga wani feeling na mussaman da yake ji game da ita,duk ya runtse idanu ita yake gani duke gaban shi tana rokonshi yaso ta,babu kalmar dake yawo cikin kunuwan shi kullum kanar cewa da tayi;-
*uncle nura ya tafi ya barmu ad’a zamu bishi da ita domin itace kawai gatar da za muyi masa amatsayin munamasoyan shi*………

Duk ya tuna da wanan kalamai nata sai yaji bugun zuciyar shi ya tsanaita ga yawan faduwar gaba da yake ji duk ya tuna da ita,sai yanzu ya fara regretting abinda ya mata lokacin domin yanzu mugun tausayin yarinyar yake ji duk ya tuna da ita.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button