HAUSA NOVELKURUCIYAR JUMMAI Complete Hausa Novel

KURUCIYAR JUMMAI Complete Hausa Novel

Duk ya tuna yadda ya wuto ba tare da yayi sallama da ita ba sai yaji duk babu dadi(nikam nace muje zuwa mallam raji)

Yanzu su jummai sunyi resuming schl ta mai da hankali sosai akan karatun ta domin science class take,duk ta tatara maganan raji ta aje amma duk ta tunashi sai ta karanta ayar nan tare da ambato sunan shi sai taji wani sabon sonshi na kara shigarta.

Suna zaune cikin class during break fast,amina tace besty walahi wani abu ke damuna.

jummai tace tau faddi inji

Tace kinsan cousin brother na da suke lagos farhan wanda na baki labari yace yana sona ina masa wulakanci?

Tace sosai ma

Tace yanzu na fara sonshi har mun dai daita dashi,ammma kinsan daddy ya hananj kula samari sai na gama karatu har na samu aiki?

Tace nafa sani besty

Tace ranar mami ta kamani muna waya da farhan,ina faman fadin i miss u alot,i love u.

Umma ta amshe wayar ta kuma fada ma daddy duk abunda taji,fada sosai yayi kamar zai dake ni,yayi season wayar sanan ya kira abban farhan akan wai a ja masa kunne kada ya bata masa diya karatu zanyi.

Jummai tace yanzu duk dangan takar dake tsakanin dady da abban farhan haka ya rufe idanu ya ci masa mutunci?

tace hmmm baki san halin dady ba game da boko ko uwarshi yana iya cima mutunci da balle yayanshi.

Tace Allah kyauta,yanzu gobe zan shigo da phone dina schl sai kiyi masa text na ban hakuri maybe ya kira kima sai ku shirya yadda zaku rinka magana.

amma ba hujja vace ace wai sai mace baliga ta gama kadatun neman duniya sanan tayi aure,duk wani banna da zai auko a lokacin fa iyaye nada babban share nasu na zunubi.

Yanzu ma akan abinda muke da’awa kenan kauye da birnin kwana kin nan zamu fara tafiye tafiye da ameera na area council.

Amina tace gaskia ya kamata idan so samu ne har gidanmu ki turo su suhi ma su daddy wa’azi,dan gaski aure nike so fisabililah.

Tace kici gaba da adu’a ain shi aure lokaci ne duk lokacin mutum yayi babu wanda ya isa ya hana abun faruwa,kuma matar mutum kabarin shi.

Tace nagode sosai da shawarwarunki bestiy Allah var zumunci.amin
Any way har yanzu babu wani labari a ban garen uncle raji?

Tace uhmm babu fa sai idan yayu waya da hajia tace mun ai ya kirata yana lfy amma bai tava tambayata ba.

Amina tace kyaleshi walahi karya yace yace bai fara jin wani abu gane dake ba all this while,Allah dai ya dawo dashi lfy.

Jummai tace amin thumma amin.

 

Raji ya rasa yadda zaiyi har ya cika wata guda kenan a south africa kullum abu sai gaba yake,bashi da aiki sai tunanen jummai,sai yabaf abun akan tausayinta da kuma rashin mutuncin da ya mata yasa yake yawan tunanenta.

Dama gida aka basu,da yaje lecture ya dawo,yayi wanka dama ana basu duk irin abincin da suke so,ya kwanta ya huta sai idan ya gaji da tunane yaje zaga gari…

Duk ya kira hajia yana son tambayar jummai amma girman kai ya hana.

Jummai na kwance tana bacci bayan sun dawo daga wani kauye kuta wurin yawon da’awar su,taji wayanta na ringing.
Tana dubawa taga new number ;sallamu alaikum
Allawiya tace jummai don Allah kizo yanzu

Tace lfy Allawiya?

Ta fashe da kuka va lfy ba dan Allah jummai duk abinda kike yi ki bari kizo gidana yanzu.

Tace subhanallahi meke faruwa?

Tace kedai kizo
Tace tau gani a hanya.

Shiryawa tai cikin Riga da skirt na material milk colour da farar hijab ta fito

Umma zanje gidan allawiya yanzu ta kirani da dukan allamu tana cikin damuwa.

Tace tau ki gaisheta Allah sa lafia sai kin dawo.

Tace tau,adaidaita ta tsare ta fada mashi tunga lowcost
Yace hajia kudin ki dari da hamsin
Tace muje mallam.

Haka ta matsu bata isa gidan ba.

Tana isa da sauri ta fito tare da bashi kudinshi,ta bude gate din gidan cikin sauri.
Nocking din part na allawiya tai,tace shigo a bude yake.

Shiga tai komi kaca kaca,ga allawiya daga ita sai daura gaba zaune dabasss saman tiels.

Tace yar uwata menene ke faru dake?

Tace na shiga uku ummai ashe alhaji saddat ba mutumin arziki bane,makaryaci,ma yaudari,mazinaci,azzalumi ta kara fashewa da kuka.

Jumma tace calm yrself,ki natsu ki warware min abinda ke faruwa.

Tace da farko da ya fara neman soyayata naki amincewa su farry suka zugani akan yana da arziki in amince naci arziki,haka muka fara tun bana jin sonshi cikin zuciyata daya fara mani hidima sosai na fara mugun sonshi,duk wani abu da nake so na mure rayuwa yana min,har ya fada nemana da fasikanci da farko ban amince ba ya nuna aurena zaiyi duk da haka naqi,su farry suka yita zugani har na vashi kaina muka fara zina ya maidani kamar matar sa a lokacin duk yana da bukata yazo schl ya daukeni zuwa hotel har na samu ciki ya kaini hospital aka cire,nace masa gaskia na gaji da aikata sabon Allah sai dai ya fito mui aure,yace idan na amince na hakura da karatuna,da naki yace tau na biyashi duk abinda ya kashe bin,domin yasan bamu da halin biya da haka har na gabatar dashi wurin su baba da yake masu son abun duniya ne babu wanj dogon bincike suka amince dashi.
Dama ban san yan uwanshi ba yacesuna kano da haka har mukai aure tun dana shigo gidan nan hakuri nike yi,ya raba daki dani baya kusan tana,gadai kayan abinci ya aje da kudi amma babu kwanciyar hankali,idan nayi magana yace ai duk abunda yake bukata gareni ya riga ya samu kwanciyar me zai dani yanzu,idan ya fita sai tsakiyar dare yake dawo wa,yavar cin abinci na, baya kulani,ya amshe wayata daya saya min,zinari daya saka min cikin lefe ya amshe abinsa,sai kawo matan banza cikin gida,ranar ya dawo cikin maye dana fara masa wa’azi ya zane ni ya mani kaca kaca kuma ya kwanta dani a wulakance ashe tun daga lokacin ciki ya shiga,daga ce banda lfy ya bani 5k naje hospital aka ce shigar ciki ne yanzu haka yace va cikin sa bane tunda bai kwanciya da ni,kinji halin kuncin da nake ciki…..

Tace allawiya sai dana baki shawara akan kibi komi a sannu gagawa ba naki bane amma ina kika ki amincewa,gashi aure tun ba a je ko ina ba an fara samun matsala.

Yanzu kam ciki nashi ne dole ya amsa kuma sai kinyi hakuri sosai,kinsan ita aure ibada ce,idan kika daure kuma kika dauketa a matsayin ibada sai kiga Allah ya baki ikon cin wanan jarabawa,ki rike sirrin ki da mijinki kada ki sake fadda ma kowa halin da kuke ciki kosu mama ne,sanan duk wani kyautatawa da kika san kina masa ki linka akan na baya,duk yadda zai kai ga wulakanta ki kada ki gaji da kyautata masa
Ki kire wayan nan abhbhwa da zan zayano maki insha Allah za a samu canji;
Ibada
Tsafta
Ladabi
Biyaya
Kyautatawa
Gyaran jiki
kalolin abinci masu dadi,koda baya ci kada ki gaji da dafawa kina aje masa.
Duk dare kada ki bari ya fara neman ki kibi duk wata hanya da zaki ja raayinsa a kanyi har ya kwanta dake.

Duk da baki san danginsa ba,duk wani aboki da kikasan yana hulda dasu ki kyautata masu kada ki sake su san halin da kuke ciki.

Maganan karatu daya hanaki,kiyi hakuri haka Allah ya tsara maki,haka waya idan ya hanaki rikewa kada ki kuskura ki masa gadama,idan ma gida yace kada kije the same thing ki bishi da yadda yake so indai bai sabawa addini ba.

Yanzu tashi ki shiga wanka,na tayaki gyara gidan muyi girki.

Tace nagode nagode sosai jummai hakika bani da yar uwa da aminiya ta gaskia sama dake.
Tace haba allawiya ko kin mance QURUCIYAR mu?

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button