KURUCIYAR JUMMAI Complete Hausa Novel
Tayi daria ban mance ba jummai jummai jummalaaaa
tace haaaa alawiya mai jagalin ido ba karfi sai tonan fada,suka tafa.
Wanka allawiya ta shiga,jummai ta gyara gidan sosai ya dau kamshi,ta girka masu vegetable macaroni,suka ci da akayi sallah ta kama hanyan gida.
Allawiya kamar tayi kuka haka suka rabu…
A kwana a tashi babu wuya yanzu su jummai 3rd term exams suke zanawa na shiga ss2.
aysha kuma sun gama semester exams anyi hutu,ta samu wani private asibiti kusa dasu tana zuwa koyon aiki,nan ta hadu da wani abdulrahim ya kawo kakarshi mace test na sugar,ita incharge nasu yaba tayi text din.
Kaka tace ke yarinya yanzo dan tsabar rashin imani wanan alurar zaki caka min a yatsata?
Tace kaka kiyi hakuri lafiyar ki muke bukata tafiye mana komi muhimmanci.
Tace ai sai da na fada ma abdo lfy ta lau yace alambaran sai ya kawoni.
Tace kaka ai ba ace kina da ciwon ba gwaji kawai za ai dan kara tabbatar da lafiyar ki.
Tace au kaji yar albarka amma shi ba haka yace min ba.
Abdulrahim yace siste don’t mind her pls do yr work.
Tace is part of my work to re-assure and make her comfortable.
Kaka tace shin wai shawarar me kuke ne,kada fa ku canza magana da turanci,idan inada ciwon ne kawai a fada min gaskia
Tayi murmushi kaka bayani nake mashi ai,domin yanzu nema zanyi maki gwajin.
Haka sukai ta drama da kaka har akayi aka gama,abdulrahim sai dariya yake masu.
Koda aka duba sugar ta is normal,ta nuna ma incharge nasu yace tai masu bayani mana.
Nan tayi masu bayana tare da masu shawar warin abubunda da zasu kiyaye idan basa so sugar ta hau.
Godia sosai abdul yayi,canza har she yayi kada kaka ta ganoshi yace pls sister may i have yr phone number?
Tace i dont have phone.
Yace wonderful as big as u are.
Tayi murmushi
Yace what of yr home address.
Nan ta fada mashi sukayi sallama,domin gaskia gayen ya kwanta mata a rai.
su jummai sun kare exams lfy anyi hutu.
Mami da kanta tazo har gida ta roki da umma subar jummai tabi amina kaduna hutu wurin anty balki,ya suka iya dole baba ya amince tare da mata nasiha mai ratsa zuciya.
Haka ta shirya cike da kewar yar uwarta suka lula kaduna garin gwamna…………
*LEEMA*✍????
*BRILLIANT WRITERS ASSO*….????
????????????????????????
????????????????????????
*QURUCIYAR JUMMAI*
????????????????????????
????????????????????????
*HALIMATU SADIYA MUHAMMAD*
*LEEMA*✍????
*51-52*
A gajiye suka isa kaduna GRA nan gidan anty khadija yake,babban gida ne wanda ya gaji da tsaruwa.
Da sallama suka shiga,ta ce lale maraba da mutan naija.
Amina tace anty hoo,ya gida ina izzidine?
Tace basu dade da fita ba tare da uncle bash inaga family house nasu suka tafi.
Jummai ta duka har kasa ina wuni,mun same ku lafia?
Cikin fara’a anty khadija tace lafia lau jummai barakallah masha Allah yau dai gani ga jumman amina ko?
Duk sai daria,tace ya mutanen gida su umma da mami?
Amina tace lafia lau suna gai daku.
Tace muna amsawa.
Anty tace kande,kande.
Naam anty gani
Dauki bag nasu ki kai the other room din.
Tace yes ma
Ta kali su jummai sannunku da zuwa anzo lafia tare da rusuna wa.
Suka amsa lafia lau.
Amina tace anty wata mai aikin kika canza ne?
Tace eh walahi ai kwatakwali ce yar binin republic kin san sun fi iya aiki.
Tace haka ne anty,aikin ma naki guda nawa daga wanke wanke sai share share ko?
Tace sai idan abban izzidine na gari wurinta yake kwana.
Tace ku karasa ciki mana ku wasa ruwa,idan kunyi sallah maci abinci.
Suka amsa tau tare da mikewa.
Daki ne babba dauke da family bed,dressing mirror,wordrop sai toilet.
Jummai tace amma gidan nan fa ya tsaru.
Amina tace ai mijin anty politician ne akwai ya’yan banki.
Wanka suka yi tare da yin sallah,suka shirya kayansu a wordrop.
Shiryawa sukai cikin riga da wando na pakistan wanda mami ta saya masu lokacin da taje dubai.
Koda suka fito anty na zaune inda suka barta tana kallon zeeworld.
Tace yan matan mami har kun shirya?
suka ce eh anty,tace muje table muci abinci,vegetable macaroni ne sai yam porrage.
Haka suka cika cikinsu cikin nishadi,suka dawo palour aka ci gaba da hira tana tambayansu labarin gida.
Tace wai amina ya su aliyu da matar shi?
Tace uhmmm anty suna nan dai yadda kika sani babu wani canji anty balki ai ba dama wurin keta duk ta mallake mana dan’uwa sai yadda tace yake yi.
Anty tace kada kiga laifinshi ai yan zuru haka suke da zaran kayi sake dan’ka,dan uwanka ko mijinka ya aure su sunan ka sorry sai yadda suka juya shi idan anyi magana suce ba boka ba mallam baiwa ce.
Jummai dai bata sa masu baki ba sabida family issue ne bai shafe ta ba.
Da la’asar tace me zl zaku yi dinner dashi kande ta dafa maku ko kuna iya shiga kitchen?
jummai tace anty indomie ya ishemu ma sai after isha’i zamu dafa.
Tace ya maku kyau bara kuyi aure ai komin son jikin ku sai kun dafa heavy foid ba takamar ku cin light food ba.
Amina tace ai kema shaida ce anty babu bani receipy da bamu iya dafa wa ba kawai ra’ayi ne cin indomie fa.
Tace nima ai dietying nake yi cu’s nayi adding weight da yawa ina son ragewa ne.
Jummai tace amma anty yadda kike siririya haka kice kinyi nauyi da yawa.
Tace tab ai badaga nan take ba sai kiga mai kiba amma baida weight sai mara kiba,kamar ni yadda kike ganina haka ina weighing 70kg fa.
Amina tace lalai kam ba daga nan ba,yanzu ya kike dieting din?
Tace kala kala ne depending on kona month nawa kike son yi,kina iya na 1month,2,3,4,5 har zuwa 6month,kinga ni yanzu na 3month zanyi.
Yadda na tsara;
9:am zanyi break fast da tea babu milo ko bounvita,sabida milo na hura mutum sosai.
Sai kuma 2:pm inyi lounch da vegetable,ko cream salad kawai.
Dinner 8:30pm fruit salad ko coffe.
Amina tace tab har 3month ban ci abinci mai nauyi ba har da nama fa anty?
Tace kina iya cin fish mana,nama kuma once in a while amma banda red meat(naman shanu) yafi komi hatsari,kawai zakiyi avoiding carbohydrate ne sosai irrin su rice,millet,yam,maize da sauransu.
Jummai tace ai kuwa mu yan arewa munfi kowa zake ma irin abincin nan musamman shinkafa da tuwo.
Anty tace ai rashin sani yafi dare duhu sabida abubuwan nan sunfi komi kawo mana matsala,sai kiga mace da safe anyi breakfast da kokon dawa,gero kona masara,ko aci masa.
Ayi lounch da shinkafa da miya
Ayi dinner da tuwo kona masara,dawa,shinkafa da sauransu kinga kuwa duk carbohydrate aka yini ana ci babu mixed diet ko wani canji yadda za’ayi balancing diet din.
amina tace amma anty ai karfi ba daya ba,idan wani nada hali wani bai dashi,sanan duk abinda ake samu a birni ba lale bane a samu a kauye.
Anty tace inji wa?
ai yan kauyen ke noma,suke shigo da amfanin gonar birni,ki fada min tsakanin kauyen da birni ina ne babu ganyen alayahu,zogala,tafasa,rama,dinkin da sauran ganyayakin.
Haka kazali ka tsakanin kauyen da birni ina ne ba’a kiwon kaji,awaki,zabbi,tantabara,zoma da sauran dabobi da ake ci.
Ina ne babu babu kwai,madarar shanu,wake ya’yan itatuwa(fruits)
Ke duk kauye sun fimu wayan nan abubuwa,sabida grednsee nasu basa ci bayan sun fimu bukatar abubuwar nan sai kaga sun kwaso an kawo birini ana sayar wa cikin farashi mai sauki,hadda tayin wulakanci ake masu..
Jummai tace haka ne anty walahi sai kin gansu a minna kasuwar kwara idan sun shigo cin kasuwa da su tomato,tatasai,tarugu,water melon,pineapple,mango,gurva haka zasu ta fama cikin rana babu sai masu tayin arziki sai na banza.