HAUSA NOVELKURUCIYAR JUMMAI Complete Hausa Novel

KURUCIYAR JUMMAI Complete Hausa Novel

Anty tace haka ne fa,yanzu shawarwarin da muke basu idan sun zo ANC(awon ciki)

breakfast;idan koko ne ko wane iri a zuba madara kona naira goma ne,ko a sayi kosai a hada dashi.

Lunch;idan shinkafa ne a hada da wake,ko ganyen alayahu,zogale,cabbage ko latas,idan da hali a sa kifi ko danya ko busasa.

Dinner;idan tuwo ne ayi miyar ganye da manja,idan kuka ne asa wake ciki ‘before u know kayi balancing diet naka.

Amina tace amma anty ai wasu basu da halin canjin abincin sai kiga daga shinkafa,dawa,masara,gero,wake sai sai doya idan da hali,su ya zasui tunda abinda mazajen su keda halin saka kenan.

Tace haba amina kamar ba mace ba,kina iya sarafa wayan nan kayan abincu ta hanyoyi da dama misali;-

Shinkafa;-

A dafata da miya,jellof ko da mai da yaji.
Ana dambun shinkafa

birabiskon shinkafa

Faten shinkafa.

Garinta ana kunun shinkafa
Wainar shinkafa

Tuwon garin shinkafa da sauransu.

Masara;-

Tuwon masara

dambum masara

Fatan masara

Kina iya surfata a jika har sai tayi taushi a dafata haka fara kamar shinkafa aci da mai da yaji ko ayi jellof dinta da wake.

ana wainar ta

Ana kokon masara da sauransu.

Dawa;-

Ana tuwo

Danwaken garin dawa

Ana dafata da wake aci da mai da yaji

Kokon dawa da sauransu

Gero;-
Tuwon garin gero

Wainar gero
Gumban gero

furar jero

Wake;-
Ana faten wake
Miyar wake
Alalan wake
Dan waken garin wake
Ana dafawa da shinkafa,doya,dankali da sauransu.

doya;-

Sakwara
A dafa da miya,fate ko da mai da yaji
Ana soyawa da kwai,ko haka nan

Ana alalanta
Da sauransu.

Tace kinga ni mijini da yake yafi gane ma tuwo da dare,sai na tukashi ruwa ruwa yadda ko ya yacita bara ta cika masa ciki ba.

Jummai tace agaisheki anty lalai ilimi nada dadi mussaman ma fanin har kar lafia,idan kayi karatun sai ka tafiyar da gidanka da iyalinka bisa ka’ida.

Tace haka yake jummai shi yasa muke so kuma ku dage ku sabo ingantacen ilimi yadda al’umma zasu amfana.

Tace ku raba kanku da yawan cin indomie da kwai.

Amina tace sabida ne naga ai light food ne.

Tace light foid for where?

Ai indomie yafi komi hura mutum nan da nan aga kayi mugun nauyi ko kiba,sabida shi indomie flour ne,flour ko da cassava ake yin da wanda yana daya daga cikin carbohydrate,kwai kuma colestrul ne yafi komi kawo heart failure.

Jummai tace insha Allah zamu kiyaye anty,ko yanzu mun karu da abubuwa da dama.

Amina tace ai shiyasa nake son zuwa gidan anty.

sai bayan isha’i uncle bash ya dawo da izzidine dasu ice cream,chocolate,biscuit da sauran kayan kwalam.

Da sallama uncle bash ya shigo.
Duk suka amsa,yace ah mutanen minna ne kunzo lafia.

Amina tace uncle bashari lafia lau.
Yace kin fara ko?
Kin san bana son basharin nan fa,ya juya wurin jummai sanu da zuwa kawar mu ya hanya?

Tace lafia yau ya muka sameku

Yace lafia lau sister

Amina tace ka ma bar wani kashe murya babu abinda zakai da kai.

Yace Allah sarki amin dago mai laya tambayi anty ai na fitar da matan,idan ba don haka va da walahi baki isa ki hanani auren kawarmu ba.

Tace see you tsofai tsofai wace mace zata aure tsoho irin ka

yace talk true ko ke kin kyasa ai nace banyi dake,shike ake wani kushewa.

Anty tace bismillah kun fara kenan,dama duk amina tazo garin nan banda hutu idan uncle na nan.

jummai dai daki ta koma ta bar masu palourn domin sun isheta da surutu.

Bashar wanda aka fi sani da uncle bash yara da manya a family nasu ka’ni g mijin anty khadija,ya kare ABU zaria tunda yayi service nashi a kaduna ya dawo gidan anty khadija da zama,dama can tasu tazo daya suna mugun shiri da ita.

Fari ne kyayawa dogo,yana da fara’a sosai da son mutane musaman ma ka’nanan yara,yana ji da izzidine kamar shiya haife shi,shi yasa duk yana gida suna tare idan fita zai haka izzidine zai lake masa dole sai sun fita tare..

Izzidine yazo kyakyawa fari tas dan shekara 7 ya rugu da gudu oyoyo anty.

Amina ta rungume shi oyoyo boi,how u?
Yace fine anty.

Haka suka ta hira cikin raha da annashuwa har dare ya raba kowa yayi hanyar dakin shi.

Tana shina ta samu har jummai tayi bacci,tace kassar banza bata da wuyan bacci,ta bidi wuri ta kwanta(asuba ta gari yan matan anty khadija).

 

A minna kuwa soyaya mai tsafta ke gudana tsakanin aysha da abdukrahim.
Yazo har gida ya gabatar da kanshi wurin baba,bayan dogon binciki ne baba ya amince masa da zuwa wurin aysha,haka suke gudanar da soyayar su cikin tsafta,har waya ya kawo mata kirar gioonie p2 da kyar ta amsa,yanzu shike kai ta schl da safe idan zai je wurin aiki wata rana idan yana da time ya dauko ta idan bai da ta hau bike.

*WANENE ABDULRAHIM*?

Abdulrahim king haifafen garin kontagora,niger state ne,mahaifinshi mamman king sanane ne a garin sabida babban dan siyasa ne kuma dan kasuwa ya rike muka’mai da dama na gwamnati kafin Allah ya amshi abinsa.

Yana da matar aure daya hajia ramatu wacce ake kira da hajia yaya,dayan ta takwas akwai general garba duba yana kaduna tare da iyalin sa,hajia iya tana aure cikin kontagora,hajia fati wace aka fi sani da anty ladin mustapha(kasan cewa sunan mijinta DR mustapha),ibrahim(iro)yana minna da matarshi,mustapha shima yana minna da matarshi sai ka’ramin su abdulrahim wanda bank manager ne a nan minna.

Allawiya kuma tana can sai faman wahala a gudan alhaji saddat,yadda ta aje break fast haka zata dauke shi ta aje lunch,shima haka zata dauka ta aje dinner ko kallon inda abincin yake bai yi,shawarwarin da jummai ta bata babu wanda bata jaraba ba all in vein,data matsa mashi ma cewa yayi bayan ya gama da ita a waje me zatayi ya burgeshi,duk wani abu na burgewa da mace zata ma namiji ta gama mashi a waje dan haka tabar wahalar da kanta,duk tayi baki man bleaching ya ka’re,ta rame ga laulayin ciki ya tasata gaba.

Raji kuwa ya gama course nashi a dadafe kullum da tunanen jummai yake kwana dashi yake yini,tun yana aje abun a matsayin tausayawa har ya gane soyayar jummai ke neman halaka shi,babu bata lokacu ranar saturday ya hada inashi inashi ya gar zayo gida nigeria.

Hajia tayi farin ciki sosai domin ya dawo cikin koshin lafia,yayi kiba ya kara kyau ga fatar nan nashi sai sheke yake yi.

Tace masha Allah nayi matukar farin cikin dawo warka,Allah sa a amfana da abinda aka karanta.

Yace amin hajia,na same ku lafia?
Tace lafia lau raji,yanzu sai maganar aure ko?domin ginan ka daka bari ana yi sun kamala da yake ka bar masu isasun kudin aiki,yanzu wireing ya rage.

Yace eh hajia muna communicating dasu ai gobe ma insha Allah zanje inga yadda aikin ya kasance.

Tace ba wanan na tambaye ka ba,matar aure nace ka fada min yarinyar da kake so ai ma yan uwanka magana suje neman aure.

Yace haba hajia daga dawo wana ko hutawa banyi ba.

Tace kada fa ka manta kai kayi alkawari kana dawo wa zaka fitar da mata.

Yace ban manta ba hajia ki kwantar da hankalinki zaji ji labari mai dadi kwanan nan.

Tace Allah tabatar da alkhairi.amin.

Da safe ya shirya tsaf cikin riga da wando ash colur na yadi mai sulbi,kayan sun amshi jikinshi,yayi kyau sosai,sallama yama hajia akan zai ji side(can inda ake masa gini)

Tace a dawo lafia

Gidan su jummai ya fara zuwa,umma na zaune tana kyaran shinkafar tuwo.
Cikin fara’a ta tarbeshi,suka gaisa,tace saukar yaushe?

Yace jiya umma,ya su baba da sauran yara?

Tace lafia lau suke

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button