KURUCIYAR JUMMAI Complete Hausa Novel
Cikin ransa yace maybe su jummai na schl,amma fa da zumudin ganinta ya kwana gashi bai sameta a gida ba.
Sallama yama umma ya wuce side.
Babban fili ne an zagaye shi ciki aka gida 2bed rum flat da babban palour sai dining area,kitchen,store sai toilet cikin duk rum din.
Gaskia gidan yayi kyau sosai.
Su jummai ana can an zama yan kaduna,uncle bash shine idanunsu shike kai su ko ina cikin garin kaduna,family housd dinsu ma duk an saba da jummai,har zaria ya kai su cikin ABU ya nuna masu wurare.
Anty kuma ya zage sai koya masu abinci kala kala da wayar masu da kai yadda zasu zauna da mutane,idan kaga jummai yanzu zaka rantsr ba ita bace jumman umma da baba dan koli.
Raji yayi zuwa gaida umma har ya gaji bai ga jummai ba sanan girman kai ya hanashi tambayan ta.
Da haka ya yanke shawarar ya fada ma hajia gaskia jummai ce matar da ya zaba a
matsayin abokiyar rayuwar shi……..
*LEEMA*✍????
*BRILLIANT WRITERS ASSO*….????
????????????????????????
????????????????????????
*QURUCIYAR JUMMAI*
????????????????????????
????????????????????????
*HALIMATU SADIYA MUHAMMAD*
*LEEMA*✍????
*Dedicated to*;-
*Rukkaya Hassan othman*
*Gaisuwar ban girma gare ku brilliant writers asso.Allah kara basira da daukaka amin*
*Godia mara adadi gare ku masoya buk din “Quruciyar jummai”ina ganin sakwanin ku na fatan alheri da gaisuwa Allah bar mu tare ya bar zumunci*
*53-54*
Nifa kai nake sauraro ka tasani a gaba kayi shiru idan baka da abin cewa zan shiga daga ciki dare ya raba””cewar hajia””
Yace amh,ahm ahm,dama akan maganar yarinyar da zan aura ne.
Eyhim ina jinka dan albarka yar ina ce?
Shiru ya biyo baya na nan mintuna,can ya runtse idanu tare da karfin halin furta “”JUMMAI””ce hajia.
Ta ran gwuda ayururiiiiiii!
Alhamdulilah masha Allahu dama nai maka sha’awarta yarinya mai natsuwa da sanin ya kamata,tunda nura ya rasu take matukar bani tausayi nake adu’ar Allah bata miji da zai rike’ta da gaskiya,ashe Allah ya amshi adu’ata..
Tace ina fatan kun fahimci juna da ita?
Ya tsinci kansa da cewa eh hajia.
Tace Allah maka albarka gobe zani kuta wurin alhaji babba duk yadda mu kai zaka ji.
Yace tau sai da safe.
Tace Allah bamu alheri.
Yana shiga daki ya fada saman matrass nashi tare da ce wa oh ni muhammadu what have i gotten myself into,yarinyar da na tsana the most wai yanzu baki na ke furta ita zan aura,ita zata zama abokiyar rayuwata.
Wait shin ko tana sona har yanzu oho,ko ta samu wani saurayin?
Allah kama mini,haka ya kwanta da tunane tunane iri iri.
Da safe hajia tai kauyen kuta wurin yan uwansu domin maganar auren Raji.
Sosai sukai maraba da maganar tare da alkawarin zuwa friday zasu shigo nema mashi aurenta.
Cike da farin ciki hajia ta dawo gida.
Da dare take fada ma raji yadda tai da yan uwansu akan ya fada ma baba ranar friday za su zo neman auren jummai.
Tace insha Allah hajia zan fada mashi.
Safe kasuwa ya iske baba ya fada mashi.
Sosai baba yayi farin ciki.
Haka sukai sallama baba nata mamaki dai dai da rana daya bai taba sanin soyaya ke tsakanin jummai da raji ba,amma da ya tuna da irin hidimar da yayi tayi ma jummai kafin ta samu makaranta sai yaga ba abin mamaki bane.
Fatan alheri ya bisu dashi domin duk wanda ya samu raji a matsayin suruku tabas yayi babban dace.
Da ya dawo ne yake fadama umma yadda sukai da raji,tare da tambayan ta dama tasan da soyayar dake tsakanin raji da jummai ne?
Tai saurin amsawa eh
Yace maddala.
Haka umma ta yita tunanen yaushe har jummai suka dai dai ta da raji bata sani har yakai ga maganar aure.
Tace shin aysha dama raji sun dai daita da jummai ne?
Tace gaskia umma banda wanan labari.
Umma tace kinji kinji abinda raji ya fada ma babanku.
Tace amma abun da mamaki gaskia ace jummai sun fahinci juna amma bata fada ma kowa ba tabbas akwai wata a ka’sa,amma jummai sai tafi kowa farin ciki idan taji wanan labari.
Umma tace Allah dawo da ita lafia.
Amin aysha ta amsa.
A kaduna kuwa jummai an zama yar gayu,an ka’ra waye wa,yanzu shirye shiryen dawowa gida suke yi sabida tun last week hutu ya ka’re.
Ranar friday baba ya gayaci abokan arziki su taya shi tar ban wakilan raji.
Tabarma babba aka shimfida a zauren gidan zuwa 10:30am suka iso su hudu cikin 406.
Tarba na musamman suka samu wurin su baba.
Bayan sun gabatar da bukatan su,baba ya amince.
Dubu goma suka bayar na gaisuwa da kwandon goro,chew gum da kwalin sweet.
Suka nuna bukatan su na son ayi auren cikin shekarar nan.
Baba ya nuna masu ai ss2 take ko yar’ta bata yi aure ba bare ita,suyi hakuri har wani shekara ta kare secondary schl.
Suka ce a basu lokaci su yi shawara da raji idan zai iya jira.
Ana taro ya watse cikin mutunci da girmamawa.
Da baba ya shigo gida ya fada ma umma yadda sukai.
Tace gaskia yadda suka ci buri akan sai jummai ta samu wadatacen ilimi kafin su aurar da ita.
Baba yace haka ne kana naka Allah na nashi duk da haka suna iya ba raji auren jummai domin sun san zai tsaya mata tayi ko wane irin karatu take so ko bayan sun yi aure.
umma tace haka ne baban su.
Da aysha ta dawo hospital(da yake yanzu attachment su ke yi)
Umma ta fada mata yadda aka yi.
Tace tau umma duk abinda kuka yanke dai dai ne.
Yanzu allawiya cikinta ya shiga wata na bakwai alhaji saddat ya dawo da ita gida kan sai ya neme ta ya gaji da ganinta da cikin shege a gidan shi,taji kukan bakin ciki sosai ranar mussaman yadda iyayenta suka nuna halin ko in kula a kanta kota kanta basa bi.
*A KADUNA*bayan driver ya gama loda kayan su a booth din mota suka ma anty da uncle bash sallama,izzidine sai kuka yake yu.
Uncle bash yace matafia Allah tsare ya kiyaye hanya sai kun zo aure na ko?
Jummai tace insha Allah.
Amina tace ai sai mun rigaka aure.
Yayi daria.
Anty tace jummai ki gaida gida na gode sosai da ziyara Allah bar zumunci,amina sai munyi waya.
Haka driver ya ja mota kamar su zub da hawaye.
Sai after 2pm suka isa minna,gidan mami suka sauka.
Sai da suka ci abinci sallah sanan mami tasa driver yakai jummai gidda tare da tsaraba niki niki.
Umma tayi farin cikin ganin yar nata cikin kwanciyar hankali haka aysha.
labari ta basu yadda kaduna ya ke irin zaman da sukai gidan anty da wuraren da suka je yawo.
Cikin tsarabar data dawo dashi akwai cabbage,arish potatoe,carrot,apple sai chocolate da sweet kala kala.
Umma ta cike na gidan su allawiya da sauran makwabtansu.
Aysha tace umma an cire na hajia kuwa?
Tace haka gara da kika tuna min bara a cire gobe sai jummai ta kai mata.
Umma tace shiga ma ki gaida Allawiya sabida tayi rashin lafia har ta kwanta asibiti wai hawan jini ke gare ta kuma ga tsohon ciki.
Tace subhanallah ashha abu bai yi kyau ba.
Haka ta kwashi tsaraban gidan su allawiya ta shiga.
Sallama tai mama tace ah mutanen kaduna an dawo lfy?
Tace lafia lau mama ashe allawiya bata ji dadi
ba?
Tace ai taji dama cikin halin ko in kula,shiga daga ciki mana tana daki.
Allawiya makure karshen gado duk tayi zufa
Jummai tace ashha allawiya sannu ashe abu yakai haka?
Ta kwashe komi ta fada ma jummai.
Jummai tace ai yanzu kan sai dai muci gaba da adu’a lamarin alhaji saddat ya girmama.
Tace kin san Allah tunda ya dawo dani gidan nan kusan sati biu kenan har yau ko leke bai zo ba.
Tayi ta kwantar mata da hankali tare da bata shawar wari.
Aysha ta shigo jummai baba na kiran ki,tace tau muje.
Sai da safe tama allawiya da mama.