KURUCIYAR JUMMAI Complete Hausa Novel
Baba na zaune saman tabar ma a kofar dakin su shida umma.
Yayi gyaran murya;
Dama kina soyaya ne da raji?
Haka taji maganar banbarakwai,ta kalli unna da mamaki.
Umma tai mata allama data ce eh.
Tace eh baba
Yace masha Allahu iyayenshi sun zo neman auren ki kuma na basu yanzu su muke jira aji abinda suka yanke game da lokacin aure.
Cikin matsanai ciyar farin ciki tace tau baba.
Yace Allah maku albarka.
Suka amsa amin baba,jan aysha tayi daki,tace sister yaushe raji ya dawo har ya fara sona tare da gabatar da iyayenshi?
Aysha tace lover girl wayan nan tambayoyi duk ni daya.
Nan ta kwashe komi ta fada ma jummai.
Jummai tai kabbara tace tabbas ayar da amina ta bani yayi tasiri akan uncle,but sister amma me yasa bai kirani yaji daga gareni ba?
Tace and so what badai shiya kawo kansa ba,ai yayi mai wuyar sauran duk mai sauki ne.
Tafawa sukai,tace bara na shafa ma amina labari tana kokarin latsa wayar ta ringing guda amina ta dauka.
Jummai tace guest what raji ya turo magaba tan sa neman aure na.
Tayi wani ihu na farin ciki sai da jummai ta rufe kunuwanta.
Tace ai na fada maki ayar Allah ba wasa ba kadan ma kika gani sai raji ya zama kamar rakumi da akala……..
*LEEMA*✍????
*BRILLIANT WRITERS ASSO*…..????
????????????????????????
????????????????????????
*QURUCIYAR JUMMAI*
????????????????????????
????????????????????????
*HALIMATU SADIYA MUHAMMAD*
*LEEMA*✍
*EDITOR*
ASM££NA X££YAN????
*Dedicated to*;
*Brilliant writers association*????????
*55-56*
Sallamu alaikum,sallamu alaikum,sallamu alaikum.
Wa laiku musallam bismillah,ah raji dama kana jin sallama ka kyale?
Na amsa bata dai ji bane.
Jummai ta shigo gurfana wa tayi ina kwana hajia.
Lafia lau yar albarka ya mutanen gida?
Suna lafia sun ce a gaida ke.
Yaushe kika dawo.
Jiya .
Ina kwana uncle.
Ko Kalonta bai yiba yaci gaba da latse latsen wayar shi.
Hajia tace kana jifa ana gaisuwa.
Yace na amsa ai.
Tace oh yau kuma ba’kin halin naka ya tashi ko dan ka kai kudin aure ka fara wani tsare gida?
Shima bai amsa ba yaci gaba da aikin gaban sa yana yi yana satar kallon jummai tare da mamakin yadda ta ka’ra kyau da girma duk wani halita na jikinta ya kara fitowa da kyau,cikin zuciyar shi yace tsarki ya tabbata ga wanda ya hallici wanan kyakyawar sura.
Tace ga tsaraba nan umma tace a kawo maki.
Hajia tace madallah mun gode sosai”arish potatoe ne sai cabbage.
Haka ta kari zamanta suna dan taba hira da hajia,tace zan koma gida hajia.
Tace tun yanzu ?
Tace eh mun koma makaranta akwai shirye shiryen da zanyi ne.
tace kai tashi ka maidata gida rana yayi zafi.
Mike wa yayi ba tare da yace komi ba yayi hanyar waje.
Mike wa tayi jiki ba kwari ta fita,tsaye ta same shi jikin bike din.
Gajia tai da tsayuwar shiru ta kama hanya zata wuce yace keeee zo nan.
ta tsaya ba tare data kalleshi ba.
Dari biyar ya jiro ya jefa mata,ya hau bike nashi tare da watsa mata ku’ra.
Hawaye ne ya cika mata idanu kota kan kudin bata bi ba ta kama hanyar gida.
Cikin zuciyar ta ce na shiga uku wane irin mutum ne uncle da dukan allamu yana sona sabida naga sona cikin kwayar idanunshi,amma meke faruwa ne?
Haka ta isa gida cike da sake sake cikin ranta.
Washe gari a schl take fada ma amina abinda ke faruwa.
Tace best friend kina da aiki sabida na lura raji irin mutanen nan ne masu shegen zurfin ciki,girmai kai,miskilanci,ga riko infact ma yana da i don’t care atitude,kinga kuwa kafin ka shawo kan irin wayan nan mutane sai kayi hakuri tare da yan dibaro.
amma definetly yana sonki baya so yayi admitting ne kawai.
Uhmm ai ni best friend na fara tsorata da lamarin uncle fa.
Tace tafi can tunda har ya iya turo iyayenshi gidan ku tabbas ba karamin so yake maki ba.
Tace Allah mana jagora amin.
Ban garen aysha kuwa an kawo kayan na gani ina so(engagement)daga gidansu abdulrahim.
Kwalin biscuit uku,chew gum uku,sweet uku,kwalin bobo uku sai 5k.
Mamansu allawiya be yan tarbar kaya dasu nafisa,5k din sama aka ba su tukuici.
Da kyat suka amsa ciki da girma mawa.
Haka aka raba kaya aka aika mahuta wurin dangi saura aka raba ma makwabta.
Allawiya har yanzu babu wani lavari alhaji saddat yaki waiwayenta ga ciki yayi nauyi yanzu 8month kenan,jummai ke shiga idan ta dawo schl tana debe mata kewa da yake yanzu harkan da’awan su sai jefi jefi suke tafiye tafiye..
Posting letter na raji ya fito daga federal government,inda aka yi posting nashi national lottery trust fund abuja.
zuwa monday zai yi reporting,duk hankalin hajia ya tashi sabida ta tsani wani nata yayi nesa da ita tun rasuwar nura.
Tace gaskia ya kamata akayi magana da iyayen yarinyar nan ayi auren nan kusa idan yaso taci gaba da karatu a gidanka.
Yace tau hajia zan je na same su.
Schl nasu ya fara zuwa ya nemi principal da asa sunan jummai cikin yan ss3 masu waec bana.
Tace ko menene dalilin sa na yin haka?
Ya nuna mata ai jummai nada babban jiki tayi girma a ss2 tunda tana da ko’kari ayi trying.
Tace babu matsala za a duba masu.
Yana fita ya wuce kasuwa wurin baba,bayan sun gaisa.
Yace dama daga makarantar su jummai nake mallaman su suka kirani akan suna neman dama abari jummai tayi jarabawa da yan aji shida sabida la’akari da sukai da hazakar ta.
Baba yave madalla hakan ma yayi kyau.
Ya ka’ra sunne kai,sanan baba inaso ayi daurin aure cikin satin nan idan ta gama zana jarabawar sai ta tare,sabida an maidani aiki abuja kuma hajia duk ta tashi hankalinta.
Baba yace ba matsala zan yi shawara da yan uwan nawa na can mahuta duk yadda suka ce zan neme ka.
Yace na gode baba Allah kara girma.
Da dare bayan sun gama cin abinci yace saratu ina yaran na?
Tace jummai na wurin allawiya,aysha tayi wurin hadda.
Yace kinji kinji yadda mokai da yaron nan raji me kika gani?
Tace mallam maganar gaskia kada mu tsaya bata lokaci a amince da bokatan yaron nan,kasan yan uwanka dai ba kulawa ke gare su ba amma a kira su a waya domin fidda hakin su.
Yace haka ne,shigowan jummai ya dakatar da su daga zantawar da suke yi.
Baba yace zo zauna,ta bidi wuri ta zauna.
Yace dama yaron nan ne raji yake son a daura auren ku cikin satin nan kafin ya tafi abuja wurin aiki me kika gani?
Tace baba amma maganar karatu na kuma fa?
Yace ina ce ai sai da kokayi magana dashi kafin ya same ni.
dole ta amsa eh baba,yace maganar karatu ya fada min daga can makarantar naku sun nemi izini da a barki kiyi jarabawa da yan aji shida,bayan jarabawar sai ki tare.
Cikin matsanan ciyar mamaki ta amsa tau baba duk shawarar da kuka yanki dai dai ne.
Yace saratu karfe nawa yanzu?
Umma ta leka cikin palour 8:30pm mallam.
Yace au ashe dare bai yi ba,auta akwai kudi cikin wayar ki kuwa?
Tace eh baba,yace kira min baban ku na can mahuta yanzu.
Ta binciko number tayi dialing ringing biu ya dauka sallamu alaikum.
Baba ya ce waalaiku musallam yaya bala ya kuka wuni?
Yace lafia lau muke salisu,ya iyalinka da yara duka?
Yace duk suna lafia dama kan maganar auren maryam ne.
Yace kodai aysha?
Yace a’a ita mai nemanta ya amince har ta kamala karatun ta,ita maryam din ce dai yaron ya matsa yana so a daura aure cikin satin nan sabida ya samu aiki abuja idan ta kamala jarabawan gamawa sai ayi buki?
Baba bala yace ai hakan ma yayi kyau yoo menene amfanin bokon diya mace ma,gara su ma sun samu mu nan yaranmu ai suna da shekara goma sha daya muke aurar dasu.