KURUCIYAR JUMMAI Complete Hausa Novel
Baba yace ai itama maryamun sha bakwai ke gareta,aysha ce ma mai ashirin
yace subhanallah ka gani ko har shekara ashirin babu aure ai gara a hada su duka a daura ko?
Yace bari dai ayi da wanda ke bukata yanzu menene shawarar ku?
Yace tau kasan mu shawarar mu bata wuce eh,sabida kwandala bamu da na baka ayi jigilar buki haka bamu da na motar zuwa daurin aure ayi lafia Allah sanya alheri amin.dif ya kashe wayar
Umma tace nasan ayi haka sabida basu damu da kai ba bare abinda ka haifa.
Yace babu komi anyi mai wuyar ai.
Wayan nan da baba yayi ne jummai ta samu information akan raji da dalilinsa na son a daura aure cikin satin nan,amma abinda bata gane ba yaushe yan makarantar su suka ce aji mata jumping tayi waec da yan ss3?
bata da amsa dole sai taje schl gobe.
Misalin karfe goma na dare aysha ta dawo daga hadda,tace sis lafia baki zo hadda yau ba?
Tace har na shirya allawiya ta aiko kirana wai bata jin dadin jikinta haka dai na bata shawarwari,sai kuma ga baba da wani sabob magana wai za’a daura aure na da uncle ranar saturday.
Tace what garin yaya?
Nan jummai ta kwashe yafda akayi ta fada mata.
Tace yana iya yuwwu wa shiya je neman alfarman haka a schl naku fa
Tace komi mai yiwu wane sister,gashi bai taba zuwa hira wurina ba bare na fahimci likes and dislikes nashi.
Aysha tace mudai ci gaba da adu’a sister.
Dasu ka hadu da amina a schl ta fada mata abun dake faruwa.
Amina ta rankwada guda cikin class,duk attention na kowa ya dawo kansu.
Tace sa’idawar banza,yanzu duk yadda akayi shi yazo ya nemi alfarma wurin pc yanzu shekenan zaki koma ss3 da zama?
Tace ban sani ba sai naji daga pc
Tace amma wanan aure naku akwai drama miji bai taba wani hiran soyaya da mata ba komi yake so sai dai yabi ta hanun iyaye?walahi inda family namu ne da babu mai bashi aure,dan ya samu surukai masu sanyin hali ne kawai.
Tace ya zaayi ya labarin farhan?
Tace ya koma schl ai india dama holiday suka samu yazo kuna muna waya akai akai.
Jummai tace better.
Amina ta kurawa jummai idanu,tace lafia kike kalona haka?
Tace uhmm ina mamaki ne yanzu nan da 2days kin zama matar aure?
Tace ana mamaki da ikon Allah ne?
Tace a’a sai naji ma kamar nice dan na fiki bukatan aure,tace tab indai da uncle ne walahi baki fini bukata ba.
Haka suka ta hira har teacher ta shigo.
Raji ya dawo wurin baba dan jin hukuncin da suka yanke akan maganar sa,baba ya nuna amincewar shi dari bisa dari,godia sosai raji yayi,daga nan ya tafi kuta “da yake babu nisa da minna” ya fada masu yadda su kayi da baba.
Uncle nashi yace dama na dauki nauyin biya maka sadaki sauran yan uwanka zasu bada goro da minti nawa aka yanke sadakin?
yace ai sun ce duk abinda Allah ya hore.
Yace madallah haka ake so sai mun zo ranar saturday.
Haka yayi sallama dasu.
Duk wanda ya kamata ya san da daurin aure baba ya sanar dasu akan ranar saturday da karfe goma da rabi na safe.
Allawiya ta taya jummai farin ciki sosai domin duk wanda yasan raji yasan mutamin kirki ne,baida abokin fada,ga ilimi da natsuwa.
Da amina ta fada ma anty khadija murna sosai ta taya jummai domin darajar duk wata ya mace gidan mijinta,komin kankanta ko girmanki haka komin talauci ko dukiyar ki.
Dady da mami fada sosai suka ma jummai wai zata bata ma kanta career,tana karama a aurar da ita har kasuwa dady ya sami baba ya bashi shawara abar maganar auran nan har ta kare koda NCE ne.
Baba ya nuna ai yin Allah ne kuma lokacin ta ne yayi don haka duk abinda za ayi bazai hana auran faruwa ba.
Ta bangaren raji ya gayaci abokan sa da abokan aikin sa.
Haka mallaman islamiyyar su jummai da officials na area council maza hada sheik ahmad lemu duk sun sami halartar daurin auren;-
*MUHAMMAD RAJI*
&
*MARYAM SALIS*
Akan sadaki naira dubu hamsin.
Bayan gama daurin aure dama umma sun shiryama maza walima wanda abdulrahim ya dauki nauyi.
Abinci ne kala kala daga safara resturant aka kawo maza suka ci suka sha tare dayin hamdala,sai fatan alheri ake ma ango.
Shidai raji ya rasa meke damun shi,tabbas yana son jummai so na hakika,amma ya rasa gane farin ciki yake ciki ko bakib ciki,a lokacin ya tuna da dan uwan sa nura lokacin da yake son jummai duk suka yi waya sai yace “”uncle yaushe zaka dawo kaga baby,ina son baby uncle idan ban aureta ba bazan iya rayuwa ba,sai yanzu ya gane bai ma nura adalci ba da ya rabasu da jummai rana tsaka gashi yanzu shi ya aureta,inda nura nada rai da wane ido zai kaleshi tabbas Allah kadai yasan abinda ya shirya shi yasa ya dauki ran nura.
Cikin gida kuwa jummai taci kwaliya da atamfa hollandis cikin kala ukun da anty khadija ta aiko mata dashi tay amfani dasu ranar daurin aure.
Riga da skirt ne dinkin ya amshi jikinta sosai sai yan kune,sarka,zobe da yan hannu kirar indian designe ta yafa babban mayafi silver da takalmi silver colour,ba wani make up tayi ba.
Haka mutane keta shigowa suna masu Allah sanya alheri maza da mata,da aka rage ne abdulrahim ya shigo.
Cikin zolaya yace my run away bride.
Tayi shiru
Yace yau baki ya mutu an zama babban mace tau Allah sanya alheri ya bada hakuri yasa anyi a cikin nasara.
Amina ta amsa da amin
Bayan ya gaisa da umma ne ta kara mashi godiyar dawainiyar da yayi naabinci da drinks
Yace ai yiwa kai ne,yaso kebewa da aysha amma ina mutane sunyi yawa kamar yau ake taron buki kasan cewa umma mai son hulda da mutane ga sun zumunci.
haka ya hakura ya wuce.
Raji ma ya shigo da abokansa sun gaisa da mutane,umma tace amina ta wude dakin babansu su raji su shiga,yaso yace zasu wuce ne abokansa suka matsa suna sun sanin amarya dole suka shiga.
Jummai ta shigo tare da amina cikin sallama.
Duk suka amsa banfa goga raji.
Bayan gaishe gaishe,da yabawa da sukai da zabin raji aka rufe da adu’a.
Sai wani abokin raji yace ku fito mu basu wuri su zanta naga wani cika yake yana batsewa sabida bai samu kebewa da ita ba
Sauran suka ce ai kuba ware kanshi na rawa ya samu yar shila sweet 17,aka sa daria.
Daki ya rage daga jummai sai raji,kare bata kallo yayi sosai da sosai haka itama ta daga idanu ta kare masa kallo shadda ce a jikinsa light blue yasha aikin hannu babban riga da yar ciki sai hula itama light blue yayi kyau cikin kayan bako kadan ba.
Yace lafia na kallo na haka.
Tace uncle laifin me nai maka da kake fushi dani?
Ya kyaleta,tace haba uncle kamar ba musulmi,idan ma wani abun ne sai ka fadamin na nemi yafiyar ka,idan kuma akan abunda ya taba faruwa ne tun ina cikin “”QURUCYA””ta ya kama ta ya by now ka manta dashi sabida ko Allah nuna ma laifi mu nemi afuwa ya yafe mana bare mu yan adam?
Ko dama ba sona kake yiba ka aure ni?
Mikewa tsaye yayi cikin rafin nama sai wuce ta rungume shi ta baya ta fashe da matsanaiciyar kuka mai ratsa zuciya……
*LEEMA*✍????✍????
*⚜BRILLIANT WRITERS ASSO*…????
????????????????????????
????????????????????????
*QURUCIYAR JUMMAI*
????????????????????????
????????????????????????
*HALIMATU SADIYA MUHAMMAD*
*LEEMA*✍????
*EDITING:- HASEENA OGANNIYA????????*
*wanan shafi naki ne ke daya kiyi yadda kike so dashi masoyiyata abin alfahari na,babu ya ke cikin birnin zuciyata a dad’e anayi sai gaskia murucin kan dutse sun buga dake sun barki,dakalin majina a hauki a zame ki hau mutum ki zauna dai dai, gaba dai gaba dai
*MY SADNAF*(nafisa ta sadiya haka taken yake)
*one love keep us together*????❤????