KURUCIYAR JUMMAI Complete Hausa Novel
*57-58*
Cikin dasheshiyar murya yace “whats wrong with u?”
“Everything is wrong wth me uncle”.
“Yau inaso nasan matsayina a zuciyar ka idan sona ne baka yi gara a warware auren nan it will be better for both of us”.
“Warware aure tsakani na dake ba abu bane mai yiwuwa dan haka zan tafi mutane na jira na a waje”.
Kara shigewa jikin shi tai cikin shagwa6a tace “gaskiya ni babu inda zaka sai ka fad’a min gaskia”.
Da yaga tana neman bata masa lokaci kada mutane su zargi wani abun yake mata cikin d’aki kawai yace “I love u baby”
Tace “say it again uncle”
I said “I love u is that all?”
“No”
“What next?”
Duk ta daburce farin ciki ya cikata tace “amma menene yasa baka kira na a waya?”
” I don’t have yr number”…. yace a tak’aice, hannu tasa cikin aljihun wandon shi ta zaro wayarshi kirar htc ta saka number ta tare da yin saving da “`baby love“`, tace “wallahi uncle yanzu ba da bane duk baka kirani ba sai na fad’a ma hajia”.
Dariya ta bashi yace “zan kira ai.
Promise?”
Yace “yes promise,sanan ta sake shi ya wuce”.
Haka gidan keta cika da mutane, jummai kaya kala uku ta saka suna ta hutuna da wayan Amina har yamma tayi, lokacin mutane sun watse Amina ce ta rage.
Tace “amma jummai kinyi kokari fa abinda kika mashi dazu”.
“Ah nidin ta wasa ce, cikin novel na gani shine na fara practicing”.
Suka ta6a hira,bayan sallah isha’i driver yazo d’aukar amina suka yi sallama dasu umma, Jummai zata rakata umma tace “ina zuwa?”
“Rakiya zanyi umma”, umma ce tayo kanta “da aure a kanki zaki raki ya? da izinin wa?,
Yanzu fa ba da bane.”
“Kai umma nan da k’ofar gidan
Babu inda zaki,idan kina son hakan kirashi ki fada mashi idan ya yarda falilahil hamd”.
Amina tace “umma ta fimu gaskia besty sai mun hadu a schl on monday”.
“Tau ki gaida mami”
“Zata ji$.
Suna kwance a d’aki ita da aysha,tace “sister walahi jiki na kamar an bubugeni”.
tace “gajiya ce sai kinyi bacci kin tashi zai watsaake.
Tau sister”.
Abdulrahim ne ya kira aysha a dan wayarta kirar gioonie p2,suka sha soyayar su.
Jummai cikin ranta tace “oh inama ni uncle ya kira haka ai da nafi kowa farin ciki,anyway ko yanzu ai cikin farin cikin nike tunda burina ya cika na auren shi”.
Da aysha ta gama wayar,tace “sister ko text ne ki tura ma uncle mana maybe gaji ce ta hanashi kiran ki”.
haka ta tura mashi zunzurutun text na soyaya,har tayi bacci babh reply.
Raji kuwa koda text nata ya shigo yana kwance a d’akin shi yayi nisa cikin tunane a ganinshi kamar yaci amanar nura ne daya auri wacce yafi so a duniya,sanan yaji takaicin biye mata da yayi lokacin har ya furta mata kalmar so,sabida yayi alk’awari bazai ta6a furta mata yana sonta ba koda zai mutu da sonta a zuciyar shine.
Sai yaga tun ba aje ko ina ba ya kasa controlling kanshi wani irin mahaukacin sonta ke fizgarshi musamman ma idan suna tare shiyasa yake avoiding nata,yaji dadin text din sosai haka ya kwanta cikin nishad’i.
Da safe bayan sun gama gyare gyaren gida sun karya,tace “umma zan shiga duba allawiya”.
Tace “kira mijinki a waya idan ya amince tau”.
Haka ta koma daki ta zauna ciki da takaici.
Yinin ranar tana gida babu inda umma ta bari ta tafi.
Sai da dare yazo masu sallama akan gobe tunda safe sai wuce abuja yayi reporting.
Bayan sun gaisa da umma da baba,ya k’ara masu godia.
Umma tace “ya shiga palour mana”,haka ya shiga ya zauna.
Can ta shigo da sallama dauke da jug da cup saman tray.
Doguwar riga ke jikinta na rubber pink sai stones a gaba da hanun rigar sai k’aramin mayafi bak’i ta yafa,ba laifi tayi kyau sabida rigar yabi jikinta.
Aje tray tayi a gabanshi ta zauna a hanun kujerar da yake zaune.
“Ina yini uncle” tace tare da kashe murya tana fari da idanu.
“Wai meke damunki?”
Ta turo baki “da kayi me kuma?”
“Sit proper mana kada wani ya shigo ya gan mu haka”.
“Sai me ai kai mijina ne”,ta tsiyaya ruwan a cup ta kai bakin shi.
Yace oh my God wace irin yarinya ce ke”.
matar uncle raji ce ni,ya amshi cup d’in a hanunta yayi sipping ruwan kad’an ya aje cup d’in.
“Uhm gobe zan wuce abuja probably zan kai a month ban shigo ba sabida sai na gama sanin kan aikin zan fara zuwa weekend,idan kinje schl ki sami pc zata fada maki class din da zaki koma,idan kuma da matsa just text me a matsayina na mijinki ban baki izinin kira na ba”.
“Amma saboda me uncle”?.
“Saboda haka nake so ayi,so don’t ague with me”.
“Kaga fa yanzu ko k’ofar gida zani sai umma tace lalai sai na nemi izininka yanzu ya zanyi?”.
“Maganar fita ban hanaki indai within this area ne,gidan hajia,schl,islamiya ko wani aiki na da’awa indai cikin gari ne amma aikin da ya wuce cikin minna ban amince ba,wani zuwa kasuwa,buki da sauran su”.
“Gidansu amina da family nasu fa?”
“Ai kinji abinda nace ziyara cikin minna ban hana ba”.
“Zan tafi sabida ban shirya kayan tafiya ba,biyo ni ki amshi sako”.
Kuka ta fashe dashi sosai.
“Kin fara ko?
Menene aka miki na kuka?”.
“Inda ban zo ba kice ban maki adalci ba,pls ya isa haka”.
ta fad’a jikin shi “yanzu idan ban yi kuka ba me zanyi,tafiya fa zaka yi babu ranar dawo wa”.
Tausayinta ya kamashi,k’ara rungumeta yayi sosai a jikin shi,wani irin feeling yake ji game da ita,gashi tak’i barin kukan.
Cikin natsuwa ya had’e bakinshi da nata,yana kissing nata a hankali,sai ajiyar zuciya take sauke wa,sai da ya tabbatar ta natsu ya cika, baki shi cikin nata idanunshi sunyi ja kamar garwashin wuta.
Bai iya magana ba sabida halin daya tsinci kanshi ciki,hanyar waje kawai yayi koda ya fita umma har sun rufe k’ofar su yayi hamdallah cikin ranshi.
Binshi waje tayi jiki ba k’wari,ya d’auko babban leda ya mik’a mata,tak’i amsawa hawaye ne ke ambaliya a fuskarta.
Aje ledar yayi a k’asa yaba machine nashi wuta ya wuce sabida idan ya biye mata sai su kwana ana abu d’aya.
Tana ganin tafiyar shi ta sake fashewa da sabon kuka,aysha da duk abinda ya faru tsakanin su tana ji da yake su d’akin baccin su cikin palour yake kuma tana ciki.
Dafa kafad’arta tayi,sister kiyi hak’uri wata rana sai labari,ledar aysha ta d’auka tare da rufo gida
Tana ta ba jummai baki har tayi shiru.
Da safe koda suka duba ledar man shafawa ne,turaruka,sabulai na wanka dana wanki,man kitso,always pad shampoo da dai sauran tarkacen mata sai 10k da yar guntuwar takarda.
Aysha ta kwasa kayan takai d’akin baba.
Umma tace “Allah sarki irin albarka hadda d’awainiya”.
Baba yace “Allah mashi albarka ya k’ara bud’i”,suka amsa da “amin”.
Baba yace “jummai ta rik’e kud’in a hannunta idan wani lalura ya tashi mata na kudi tayi amfani dashi”.
Tace “A’a umma ta rik’e idan ana bukatan wani abu ayi amfani dashi”.
Haka ta shirya jiki babu k’wari zuwa schl dole babban hijab ta sa har k’asa idan ta shiga schl ta cire,sauk’in ta guda makarantar su mata zallah ne.
Suna zaune a class ta fito da guntuwar takardar da ya saka cikin kedan kayan da ya kawo mata,rubutu yayi kamar haka;-
” *sallamu alaikum ga kaya nan da 10k kiyi hakuri babu yawa idan akwai wani abu da kike da bukata text me*”
Tsaki tayi kare da mutsitsike takardan.
Amina tace whats wrong?
“Nothing that remaind me during break ki rakani office na pc”.
Tace “ok”
Lokacin break suka tafi office din,bayan sun gaisheta jummai tai mata bayanin abunda ya kawo ta.