KURUCIYAR JUMMAI Complete Hausa Novel
Tace “dama uncle naki ya nemi alfarma kiyi exams da ss3 students wanda nasan babu tamtama u can make it,yanzu zaki fara shiga cikinsu kuna revision tare sabida time table na waec ya kusa fito wa”.
Tace “thank u”
Amina tace “ai na fad’a maki shi ya nemi alfarma gaskia am sorry to say yr husband is simple definately very hard to understand”.
Har aka tashi schl hiran raji suke yi.
Koda ta dawo gida ta bud’e wayanta ya mata text biyu.
Na farko yana shaida mata ya kama hanya ta taya shi da adu’a.
Na biyu kuma ya isa lafiya yana gaida mutanen gida.
Ango raji ya isa abuja lafiya office ya fara tsaya wa inada aka nuna mashi office nashi a matsayinshi na director tare da yin introducing nashi ga sauran maaikatan.
Sai 4:30pm suka tashi aiki motor suka bashi kyauta da matsakaicin gida a wuse zone 2 1bedroom ne da palour sai toilet ciki,a office zai rink’a yin breakfast da lunch.
Komi akwai a gidan na more rayuwa haka ya wuni da tunanen jummai.
aysha sun gama attachment nasu yanzu ta shiga 200level karatu babu kama hannun yaro,fanin soyayarta da abdul sai abunda yayi gaba.
Jummai dai kullum cikin tura ma mijinta text take yi sabida ta d’au alk’awarin bara ta ta’ba tsallake umurninshi ba tunda yace kada ta kira shi barata kuwa kira ba koda sonshi zai zama ajalinta.
Oga raji yayi 3weeks kenan a abuja aiki suke sosai babu kama hanun yaro sai dare,yana ganin text na jummai kuma hakan na masa dad’i sosai amma bai ta’ba attempting yin reply ba,sabida duk yaji muryanta yakan tsunduma cikin halin sha’awarta gashi yana tsoron aikata sa’bon Allah.
A ko wane lokaci ya kasance shi d’aya tunaninta ke adabar shi musamman idan ya tuna da lokacin da yayi kissing nata sai duk hankalinshi ya tashi.
Da dare allawiya ta tashi da nak’uda ranga ranga aka kwasheta sai general hospital minna bayan doguwar nak’uda da asuba ta haifi d’iyarta mace kyakyawa sak babanta.
Allawiya anji jiki sai kwanan wahala ake yi sai k’arfe biyu na rana aka sallamo su daga hospital.
Jummai na dawo wa schl umma ta fad’a mata ai cikin murna ko tu’be uniform bata yi ba tai hanyar waje da gudu umma na kekeke,ina har ta fad’a gidansu allawiya
Tace “Allah mai iko d’iya sak mahaifinta,sannu allawiya ya k’arfin jiki”.
Tace “naji sauk’i”.
“babanta ya sani kuwa?”
“Eh yazo hospital d’in ma ina bacci yaga baby wai har ya mata hud’uba da sunan mahaifiyar shi ramatu,ga kaya can daya kawo akwatuna ne set guda shak’e da kayan baby dana mai jego sai set d’in kayan wanka”.
Jummai tace “better ai tunda ya kula ya aiki da wani abu”.
Yanzu alhaji sid kullum sai yazo ganin baby Allah ya d’aura mashi mugun sonta sai hidima yake masu.
Kaya suka ware kala bakwai aka ba tela ya d’unko ma mai jego,jiki na rawa ya bada kud’in d’unki.
Jummai tace “Allah ne ya amshi adu’ar mu”.
Allawiya tace “haka ne jummai Allah kara shige mana gaba amin”.
Ana gobe suna babban rago ya kawo da buhun shinkafa buhu guda na flour da sauran tarkace.
Dole jummai ta kira amina akan tazo da driver gidan su suje kasuwa sayan sevoniars.
Jummai abu ya kai garesu bata nan bata can
Jalabiya ta zura baki ta yane kanta da mayafinshi sai slipers dake k’afanta suka kama hanyar kasuwa.
Aysha na schl umma na gidan su allawiya anata faman aikin masa na gobe.
Da suka isa basu nan basu can sai sayaya suke yi ana rugawa cikin buth har 1:30pm
Tace ma driver ya biya dasu oasis bakery suyi bucking na donut da short cake k’wara d’ari d’ari na gobe da zasu sa a take away na ‘yan walima.
Mallam abu driver yace “hajia ko hanzarta ko zamu samu sallah juma’a”.
Jummai tace “ai na sha’afa yau juma’a”.
amina “tace ina wayanki?”
“maybe yana gida fa”.
Haka kawai raji yaji gabanshi na mugun fad’uwa yayi ta kiran hajia bata d’auka ba,daga baya ya yanke shawarar kiran jummai yayi mata wajen 20miss calls bata d’auka ba yasan something is wrong,tun 12:am ya had’a kayanshi zuwa minna weekend da yake motar shine bana kasuwa ba 12:14pm a k’ofar gida tai mashi.
Koda ya duba k’ofar gida a rufe yake,ya tambayi mechanic na k’ofar gidansu yace mai hajia taje kuta tun jiya,ya sake trying number not rechable.
Tsaki yayi domin bai san ranar dawowanta ba yanke shawarar zuwa gidansu jummai yayi,yana gunguni yace “ita kuma wanan yarinya ko wane iskanci ne yahanata d’aukar waya oho”.
Yana isa k’ofar gidan yayi parking mota gefe sallama yayi ta kwadawa shiru sai ga aysha ta dawo daga schl suka gaisa.
Tace “uncle saukan yaushe?”.
Yace “ban jima ba,ya schl babban anty?”
Tace “lafia lau,baka shiga ba ka tsaya waje?”
“Nayita sallama ne shiru babu kowa”, tace “eh maybe suna nan gidansu allawiya sabida ta haihu gobe suna aiki suke yi”.
Yace “ai nayita kiran wayanta bata dauka ba”.
Tace “shiga daga ciki bara na dubo maka ita”
Tare suka shiga a bashi ruwa a jug, ta aje littafan ta tana shiga gidansu allawiya ta fad’a ma umma raji yazo.
Tace “ai kuwa jummai na kasuwa tun safe ga wayanta nan na tsince shi ta yar saman gado ita uwar mai jego”.
Tare da umma suka shigo gida, rusunawa yayi ya gaida umma cikin jin kunya.
Tace ” sannu fa ya aiki ya hanya?”
yace “lafiya lau
gashi kuwa jummai suna kasuwa tun safe ita da amina ga wayar nata nan can na tsinto shi”.
Amsar wayan yayi a hanun umma ranshi idan yayi dubu ya baci “wai yarinyar da yama gargad’i banda zuwa kasuwa shine yau tun safe take kasuwa har yanzu”, sai yayi ya dubi agogon hanunshi yana tsaki.
2:0pm suka dawo gida suna k’ok’arin sauke kaya raji kuma ya fito zuwa masallaci.
‘Kare mata kallo yayi da kyau, jalabiyar mai sul6i ne sosai yabi jikinta ga mayafin shi data yafa ya tatare ya koma kamar d’an kwali jelar sumanta kwance a gadon bayanta ya ya barbaje mugun takaicinta yaji.
Har gaban motan yaje ya damk’i hanunta ya wurgata back sit na motar shi ya bata wuta……
*LEEMA*✍????
*⚜BRILLIANT WRITER’S ASSO*….????
????????????????????????
????????????????????????
*QURUCIYAR JUMMAI*
????????????????????????
????????????????????????
*HALIMATU SADIYA MUHAMMAD*
*LEEMA*✍????
*EDITED BY*;-
*LEEMA*
*masoyana abin alfahari na*;-
*Habeeba idrees(hubbeey)*
*Jamila mopol*
*Hawwa M.U(smasher)*
*Mienarh and her suruki hassan ATK*
*Hak’ika kun numa min k’auna da soyaya kuna a cikin birnin heart d’ina Alherin Allah ya isko ku a duk inda kuke a fad’in duniyar nan*??????????????❤
*Hubbey Allah ya ba baban mu lafi mai amfani tare da albarka,yasa zakar jiki ne amin*????????
*59-60*
A parking space na central mosque minna yayi parking motar yana k’okarin fita,tace uncle ina zaka?
Bai bita kanta ba ya fita tare dayin locking car din ya shige masallaci.
Haka ta zauna cikin zafi gashi duk wanda ya gifto sai ya kaleta dole ta kwanta saman sit.
Koda aka idar da sallah ya dauki kusan minti talatin(30minut)a cikin masallaci kafin ya fito wanda da gaya ya mata haka taji kwatan kwacin b’acin ran da ya shiga.
Data gaji da kwanciyar ta koma a zaune mutane da sun zo wuce wa sai sun kaleta gashi ya daidaicin inda keda rana sosai yayi parking kuma bakin hanya,tsaki tayi mutane dai akwai iya shege da auren ka ayita faman kallonka(nace wayanda suka kale ki a kasuwan kuma ba mutane bane ko mallama jummai).
Yana iso wa ya bude motar tare da bata wuta,ta fashe mai da kuka haba uncle wani irin zalunci kenan walahi dana san haka kake da ban yadda da wanan k’adararen auren ba,idan ma wani laifi na maka ai bai kamata ka hukunta ni ta wanan hanya ba ni mace ce mai rauni kuma mutum kamar ka.