HAUSA NOVELKURUCIYAR JUMMAI Complete Hausa Novel

KURUCIYAR JUMMAI Complete Hausa Novel

Driving yake yi hankali kwance”cikin ranshi yace ya salam yarinyar nan bata da hakuri ita bata ga laifin data mashi ba ya bata umurni ta k’etare sanan yanzu tana masa vomiting rubbish a nan.

Bakin yahuza suya spot yayi parking,rik’e rigarshi tayi gaskia ni bara ka fita ka barni cikin zafin nan ba haka kawai in banda zalunci.
Buge bakinta yayi da bayan hanunshi stupid girl dama rashin kunyar naki na nan bai je ko ina ba ko?zan fita ba tare da nayi locking car din ba idan kin isa ko kofar motar nan ki taba kiga yadda zanyi k’asa k’asa dake a wurin nan idiot.

Wani sabon kuka ta fashe dashi walahi tunda ba ubana bane kai da zaka sa doka ban k’etare ba sai na fita tana yi tana bugun glass,yana kallon duk abinda take yi a nan inda ya ke zaune daga wurin ya dana lock na motar ta rufe,order yayi na rabin kaza sai sinasir da exotic hankali kwance ya zauna ya ci abin shi cikin natsuwa sanan ya tashi ya nufi mota, koda ya isa tayi bacci yace silly girl, ban da niyar cutar dake ko zaluntar ki “this is the only way da zanyi punishing naki” har kiyi realizing mistake naki amma nafi kowa sonki da tausayinki my baby.

Hajia ya kira take shaida mashi ai ta jima da dawo wa har tajlyi girki,yace gashi nan k”‘arasuwa gida,tunanin yadda zai yi da jummai ya shiga yi babu halin ya mai data gida a haka duk ta yamutse.

Yana isa kofar gida ya fara shiga ya bude dakin su na samartakaa dama a soro dakin yake da dukan allama hajia bata jima da gama gyaran dakin ba,ya dawo ya sungumeta zuwa cikin dakin ya kwantar da ita saman katifa ya kuna mata fan yayi locking kofar ta waje sanan ya shiga cikin gida.

Bayan sun gaisa da hajia tace ai kana fita baka dad’e ba na dawo sunday ke fada min kazo shine na gyara maka dakin na dafa maka wani abun.

Yace ai nayita kiran wayarki baki dauka ba shine na lek’a can wurin su jummai daga nan na wuce masallaci.
Tau suna lafia ko?lafiya zau suke.

Ya wurin aikin naku babu wata matsala injin,babu matsalar komi hajia muje kofar gida kiga mota.

mayafi ta dauka suka fita tace masha Allahu mota tayi Allah sa a mure,amin ya amsa
Bubude mata cikin motar yayi ta gani sanan suka koma gida,tace abincin a nan zaka ci ko cikin daki?
A’a hajia daki zani da nayi wanka inci abincin.

Tace dauki ka tafi dashi,saman tray babban kula ne da jug na ruwa,cup,plate serving spoon da spoon.

koda ya shiga stil bacci take hankalinta kwance,ya tube kayanshi ya shiga toilet wanka yayi sosai ya fito daga shi sai boxer shafe jikin shi yayi da vesine intensive care body lotion,yayi cumbing kanshi sanan ya fesa body spray .
Three qurter black yasa da red armless mara nauyi koda ya duba agogo lokacin sallar la’asar yayi dadage wa yayi iya karfin shi ya d’ad’a ma jummai dundu a baya,zabura tayi ta mik’e zaune tana kale kale
Yace kasa sarkin bacci, uwar mai jego,k’irjin buki,unguwan zoma kasuwa a kai maki dole shin Allah ya baki ikon yin ko da sallar azuhur ne uwar yawon kasuwa ga la’asar ta riske ki?
Tura baki tayi,would u get up kina turamin baki ga toilet nan ki shiga kiyi alwala ya fita zuwa masallaci,wanke fuska tayi sanan tayi alwala data fito ta shafa lotion dinshi ta dauki turare fuuuu fuuu fuuu ta fesa sanan ta kabarta sallah haka ta hada azuhur da la’asar,koda ya dawo ta idar tana zaune da tasbaha a hanunta.

Yace koda kwana kikayi istigfari walahi Allah baya yafe zaifin da kama wani sai musamman ma mijinki dan haka ki sauke girman kai ki nemi gafara wurin mijinki,banza tayi dashi.wanene ya baki izinin zuwa kasuwa?
Hab’arta ya daga ke bada ke nake magana ba?

Cikin sanyin murya tace am sorry
For what?ai laifinki yawa ke dasu na farko kin fita bada izinin na ba zuwa kasuwa for that matter,nayita kiranki a waya baki d’aga ba,sanan jubi dressing d’in da matar aure tayi zuwa kasuwa fisabililah,sabida baki d’auke ni a bakin komi ba kuma ban isa dake ba ko?

Kin san da cewa ina abuja wani friend nawa ya kira ni wai yaga mata na a kasuwa ko mun zu weekend ne?all his thought dake naje abuja,haba maryam kina da ilimin addini fa,yanzu kinsa nayi loosing confidence a kan ki.

Bara na baki wani hint;-

*YARDA DA AMANA*;-walahi idan kika same su a wurin mijinki ki kwanta ki huta maryam,yarda shike sa mijinki ya amince maki,misali;kinga ke b’aka ce idan nace maryama fara ce tas koda baki daya mutanen duniyar nan zasu taru su ce maryam b’aka ce bazan taba yarda ba.
Menene ya janyo hakan?yarda da aminci dake tsakani na dake.
Idan kuwa babu yarda da amincin nan koda sun taru sunce ai maryama fara ce tas bazan taba amince wa da maganar su ba.Hope u understand?
Gyada kai tayi,kinga ni yanzu yarda dake nayi na baki amanar kula da kanki tare da kare mutunci na dana aurenki,amma kin manta kinyi facali dashi,kinga kuwa yanzu Allah kiyaye ko a hotel aka ce min an ganki bazan iya musawa ba duk da nasan halinki bara ki iya aikata haka ba.
I beg u in the name of Allah idan nace zauna nan maryam koda shekara zanyi ban dawo ba kada ki kuskure ki tashi daga inda na baki umurni ki zauna until i said so,did i make myself clear?
Daga kai tayi,uncle ka yafe min walahi hidima ce tayi mana yawa amma bada niyyar wani abu na aikata haka ba.
Babu komi maryam ai ba wani mugun abu kika yi ba is just that na tsani naga matar aure tana cud’anya da maza cikin kasuwa shine dalila,yanzu ci abinci na mai daki gida.

Dafafen doya ne da miyar stew,bata wani ci da yawa ba(idan kun tuna doya bata cikin tsarin abincin da jummai ke so).

Har kin gama?eh
Rufa mayafinki da kyau kinji?tau zan shiga in gaida hajia.
A’a ki bari ranar sunday tare zamu kuta ki gaishe su zan kai masu mota su gani.

Sun kama hanya yace gashi ban maki tsarabar komi ba ki shirya anjima muje shopping

Da ka barshi ai,bana son musu ke mata tace kuma ni nayi niyya ai ba ruk’o na kikayi ba.
Yana aje ta yace ki gaida su sai na dawo anjima.tau.

Yana juyawa ta shige gidan su allawiya(mai hali baya fasa halinsa)

Ah jummai masu miji sai yanzu?eh tace a takaice.
Amina ta shigo da kayan duka ko,kin duba komi yayi?
Eh na duba Allah bar zumunci.amin
Gobe tunda safe kiyi ma yaya nafi’u magana yaje bakery ya amso sauran kayan,bazan samu zuwa ba.
babu komi ai kinyi k’ok’a ri,ina baby rahma?
Tana wurin mama ana mata wanya,tau anjima bazan samu shigowa ba zamu fita da uncle.
Babu matsala an kawo dunkuna fa ki duba mana,wani babban leda ta jawo kaya ne kala tara.
A’a ba kala bakwai aka kai dunki ba?
Tace eh daga baya cikin kudin daya ke yawan bani na aika aka sayo min irin material din nan nawa kuma aka dunka maku keda anty aysha muyi anko,su mama ma na cire masu turmi biu sunyi anko da umma.
Allah sarki allawiya rayuwa kenan bayan wuya sai dad’i Allah kara rufa asiri ya barmu tare.amin
Yiwa kai ne jummai kin taimake ni a lokacin da kowa ya juya min baya dan haka idan na mance alherin ki ai na zama butulu.
Yanzun ma bayan suna akwai wasu adu’oi da zan baki kinga yanzu Allah ya amshi adu’ar mu mutumin nan ya fara gane gaskia,be kamata muyi sakaci ba k’ara bada himma zamuyi wurin kai kukan mu ga mahalici har komi ya dai daita ki samu kiga yan uwanshi.

Tau sai an k’are harkar bukin sunan nan,tau sai gobe.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button