HAUSA NOVELKURUCIYAR JUMMAI Complete Hausa Novel

KURUCIYAR JUMMAI Complete Hausa Novel

Tana shiga gida umma tace uwar mai jego sai yanzu?umma mun fita ne fa da uncle.
Ke zo nan fada min gaskia ina da ina kuka je,babu abinda ya shiga tsakanin ku ko?
Kai umma masallaci yaje,wurin cin abinci daga can ma bacci ya kwashe ni muka dawo gidan hajia(idan baku manta ba jummai bata da d’abi’ar k’arya tun tana karama)
Kiji tsoron Allah bai maki komi ba ko?
Bata san inda maganar umma ya dosa ba,daki ta shige.
Umma tace babu shaka ai tsaru zan fara baki kafin amin aika aika(ku tayani gani mutum da matarshi har wani aika aika ake tsoron ya faru)
Aysha tace har kun dawo inace ko sai gobe?haba sister ai sai umma ta cinye ni danya,ta bata labarin yadda suka yi dashi.
Tab ashe kin wahala kuma fa da gaskiyar shi don Allah ki kiyaye.

Taso kiran amina amma wayanta na hanunshi haka ta hakura da akayi sallar isha’i tayi wanka tare da mulke jikinta da turaruka humra wanda anty khadija ta aiko mata dasu daga kaduna,duguwar riga na material tasa daga sama an tsuke shi ka’asa kuma an bude sosai bata daura dankwalin ba ta fito cikin gida.
Aysha tace u look????

thanks sister,umma tace sai ina kuma?
Fita zamu yi umma,sannu yar dad’i miji ina raba ki kina shige masa.
Haba umma mijinta nefa koma sayaya zasu ba wani wuri ba.
Ayyo ai sai kiyi bayani ko.
Suna cikin haka ya iso dukawa yayi a kofar gida suka gaisa da baba ya shigo ciki.
Ina yini umma,lafiya lau ya gajiyar hanya?
Babu gaji.
Ki tashi ku tafi kada ki bata masa lokaci tace tau mikewa tayi ta shiga daki.
Aysha tace sannu uncle,yauwa aysha ya makaranta?lfy lau.
Yace umma ga moto nan waje daga wurin aiki aka bani,tau Allah sanya albarka yasa a kashe lafia.amin suka amsa

Jummai ta fito sanye da kashka mayafi tayi rolling saman kanta,sai harara yake binta dashi.

Sai mun dawo umma,a dawo lafiya.
Suna shiga mota ya rik’e kunenta sai data saki k’ara,ke baki iya daukar simple instruction ne?wane irin dressing kenan wanan rariya da kika saka wai riga da wanan figaggiyar mayafi kina matar aure.

Kayi hakuri tau,hakuri guda ne idan mun isa ki tsaya cikin mota har in gama abinda zanyi,yaja mota.

A bakin “mustapha all store”yayi parking,tana kokarin fita yace ina zaki?go back my friend,zama ta gyara ya kuna mata AC ya rufe motar ruf ruf.
Man shafawa,sabulai,pad,turaruka,make up kit gaba daya ya saya nata kenan.

su umma sabulai,madara,milo,sugar cube,biscuit,chocolate da sauran tarkace ya kwaso masu aka mashi total ya biya.
Zuba kayan yayi a back sit yace me kike tunane?
Babu komi tace,jan motar yayi zuwa yahuza suya spot wuri ya samu can ciki yayi parking,wait for me yace.

Leda biu ya dawo dashi,yace ga naki wanan na hajia ne.

Tace an gode,plastic chair ya jawo masu guda biu suka zauna under umbrela tree.
Yadai kinyi shiru?babu komi,gara ki fadi kada ya kashe ki sabida am a stright forward man bana rike mutum a rai idan kamun ba dai dai ba zan fada maka gaskia,ba yabon kai ba ina da hakuri iya gwargwado,abubwan da kika ga inayi maki is for our own benefit,bawai bana sonki bane.
I love u the most maryam,ina so muyi building rayuwar mu based on soyaya,kauna,amana da gaskia,idan bamu gyara zaman mu yanzu ba sai yaushe?pls don’t be offended u will get use to it kinji my wife.

Insha Allah zan gyara uncle,gud girl vanilla ice cream ya dauko babban rkba cikin kayan,ya bude ya fara bata tun tana kawar da kai har ta fara amsa,suna yi yana bata labarin wurin aikinsu yace ko zaki bini?
Done kai tayi,ya karatu kina gane wa sosai hope ba wani problem?
Eh time table ma ya fito on 12 of march zamu fara biology practical,ki maida hankali sosai Allah kuma ya bada sa’a.amin sai 10pm suka koma gida.

Ga wayanki,kuma kinyi kyau sosai yau irin dressing din da ake ma miji a cikin gida kenan bana zuwa unguwa bane take note.am a jelousy type.
Thanks for every thing uncle u make my day.
Di’nt worry,sleep well and always be a gud girls.
Kayan ta kwasa ta shige gida,idanun umma kyam bata yi bacci ba.

Umma baki yi bacci ba?ta ya hankali na zai kwanta kina waje,yanzu ya kwanta tunda na dawo ga kaya nan daya saya mana.
Ki aje gar gobe shidai baya gajiya da hidima.
Wanka tayi,ah sister baki yi bacci ba?eh yanzu muka gama waya da abdul,zata fara ba aysha labarin abubuwan da ya faru tace ke me yasa baki da sirri ne kullum bakin ki na yoyo ki bada labarin abinda ya faru tsakaninki da miji,ba haka ake yi ba boye sirrin ku zaki na yi ko umma bai kamata ta san abunda ke tsakanin ki da mijinki ba bare friends naki,naga bakinki bai da birki da abu ya faru ki kwace ki zazaga ma amina mutum sai Allah fa.
Tau sister zan kiyaye.
Kiranshi ya tada ita da asuba,tana dauka yace atashi ayi sallah ya kashe.
Sallah sukayi suka gyara gida kasan cewa yau suna,kayan ta fito dashi aka zazage umma tace masha Allah yayi kokari Allah sa albarka bara baban ku ya dawo daga wurin radin suna a nuna mashi kayan,akwai turmin zani da dubu biyar da abdulrahim ya kawo jiya bayan fitan ku aba mai haihuwa,ba za a bada kudi ba yanzu za acire sunk’in sabulu biu a hada da turmin zanin,kudin sai ki ma mutanen kuta tsaraba.

da baba ya dawo aka nuna mashi godia yayi,aysha tace kajin nan akai gidan nafisa ta aje mana a freazer tunda gasashe ne har mu tashi buk’aata.
Umma ta shiga da kayan taba maman allawiya sukayi godia taba allawiya ta ajiye.

Text jummai tai mashi akan zata kashe wayanta suna da aiki
Yayi reply uwar buki ayi aiki lafiya.
Su umma masar shinfa sukayi da safe,zuwa rana zasuyi jelof rice na taron buki.
Gidan su jummai kuwa alhaji sadat da kanshi ya damka mata komi za a masu tuwon semo,amala sai white rice shida abokanshi
Allawiya kuma tace dambun shinkafa take so sabida friends nata masu zuwa,jummai ta koma kamar mahaukaciya ita da aysha saukin su daya nafisa ta shigo tayasu aiki can sai ga amina ta iso.
Murhu uku aka hasa guda akayi miyar danyar kubewa plain,miyar ayoyo plain sai stew da yaji soyayen naman shanu.
Aka kwashe a kulali,sai white rice,kayi tuwon semo sai amala zuwa sha biu sun kamala,ai sai ga kaji kuma da za ayi pepper chicken da cream salad nacin shinkafa.
Saukin su guda an gyara kajin an yanyanka suka shiga tafada da kayan kamshi aka samu aka soya aka haka.
Su nafisa da amina ragwaye suka koma aikin zaune na yanke yanken cabbage,cucumber,carrot da su albasa aka hada zuwa karfe 1:30pm ya aiko daukan abincin amina da aysha suka kwasa zuwa mota.

Can cikin gida kuma vmasaka tsinke mata sun cika mai jego sai shiga ake ana sake kaya ita da baby rahma sunsha kyau.
Sai da sukayi sallah suna hutawa aminna tace amarya ya kukayi da angonki baki kirani ba nasha labari(da yaje amina irin mutanen nan ne masu shegen son jin gulma)

Aysha tayi saurin taron numfashin jummai tace nafisa na neman alfarma ki koma gidanta maganan gyaran jiki da tayi ma umma zaku fara yanzu,tace gaskia sister yayi sauri fa.
Nafisa tace ke kwata kwata waec da neko wata hudu akeyi fa kuma ya ishemu muyi duk abunda zamuyi cikin natsuwa ya bi jikin ki sosai kafin ki tare.
Tau naji bara mu aza tukunyar dambu kafin mai jego ta fara mana aike.
Haka suka ta hidima,anata serving mutane friends nasu duk sun zo hada yan karya su fedy da farry, basu suka gama ba sai lokacin sallar la’asar.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button