HAUSA NOVELKURUCIYAR JUMMAI Complete Hausa Novel

KURUCIYAR JUMMAI Complete Hausa Novel

Nafita ta wuce gida sabida tayi bak’i,wanka suka shiga aka shirya lokacin jummai ke nuna ma amina kayan da raji ya sayo mata,amina tace Allah bamu damshen ku kin samu miji mai zuciyar yi,nan aka bude make up kit amina ta tsatsara masu kwaliya suak shiga gidan mai jego ai kallo ya koma sama kyawo na dukan kyawo su farry sai yatsine yatsine akeyi,fedy tace wow kin hango wasu big girls kuwa?
Farry tace dallah can mallama cooker’s dinmu ne fa su jummai,taba amma sun fantama ai ko material din da ke jikinsu abun kallo ne sabida tsadar shi ga make up ya zauna a fuskar su daram masha Allah.
Mai jego ta saka nata material din irin nasu akayita hotuna hadda amina, sai yamma lis amina tai masu sallama ta kwashe tarkacen sevoniers ta wuce gida.

Bayan kowa ya watse ne an gyara gida allawiya tace ban san da wani irin baki zan maki godiya ba jummai kin fidda ni kunya wurin miji na,kin fidda shi kunya wurin abokanshi,badan kin tsara abubuwan nan haka ba kuma ya tafi according to plan da ai babu magana,tunda wayan nan yan iska su farry dana dauka abokan gaskia babu uwar da suka tab’uka min sai cika wuri da k’ananan maganganu da yatsine yatsine.
Haba allawiya nasha fada maki babu godiya a tsakanin mu,nima dana je kaduna hutu ne na koyi duk irin abubuwan nan wurin anty khadija kinsan mijinta babban dan siyasa ne idan zai yi b’aki haka muke yini a kitchen ana girke girke.
Tau gaskiya kafin na koma zaki koya min wasu abubuwa,baby rahama ce ta fara kuka jummai ta dauke ta sorry my baby wanene?mumy ce da friends nata suka hana ki hutawa yau ko.

ansheta ki bata tasha ga jikin yayi zafi ma sai kin bata paracetamol syrup,tana bata nono suna ci gaba da tataunawa kinga yanzu ya rokeni gafara akan duk abubuwan daya aikata min a baya sharrin shaidan ne kuma na yafe masa domin gaskiya da laifina ciki kinga kafin inyi aure yayi disvirgin dina,lokacin aure na babu abunda mama ta bani na k’arin ni’ima da gyaran jiki sai ma wasu uban capsule da su farry keta dura min na tighting gaban mace da gyara breast wai a cewarsu abunda ya kamata na gyara kenan kawai,koda nayi aure breast dina kamar silifas,gabana ya bude sosai,jikina in banda gel,cream da tubes na bleaching babu abinda nake shafawa ko turare ban damu dasu ba haka kai na yasha relaxer ya guiguye ina wata banyi cumbing nashi ba bate yaga kitso.

Gidana babu gyara ina sati guda banyi shara da mopping ba gani nake yi tunda daga ni sai shi gidan bai da dirty,ban iya wani abinci ba bayan shinkafa da miya,tuwo,taliya sai indomie da tea,ban san abubuwan da mijina yafi so ba ta fanin abinci,abin sha,sutura,colour da sauransu,ban san yadda zan tarbi miji ba idan ya dawo daga wurin aiki,ban iya magana mai dad’i ba kullum cikin fada da tashin hankali nida miji,ga kayan abinci iri iri amma ban san yadda zan sarafa su ba kullum daga charting da tsofin samari na sai waya da friends dina,su farry kuwa sai k’ara ingizani suke akan nayita shuka masa rashin mutunci kada ya raina ni,amma maganar gaskiya ina son mijina sosai.

Ajiyar zuciya jummai tayi, ina nan ina zagin bawan Allah ashe kece mai laifi allawiya walahi yayi mugun maki adalci da bai sake ki ba,watan lokacin nan kyale ki yayi ko zakiyi realizinig mistakes naki amma inna kanki na hayak’i shiyasa ya koroki gida kuma dole ya amshe wayanki yace ciki ba nashi ba tunda ba cikin hayacin sa ya yi kwanciyar aure dake ba ga kuma zahiri yana gani kina charting da samarin ki kamar ba mai ilimin addinin ba,gaske dai ya mashe wayar duk hanUKnka mai sanda yake maki amma kika rumtse idanunki,mace babu gyara taya zai samu gamsuwa da natsuwa dake?dole yake neman matan banza,kullum ya nufoki sai warin mayukan bleaching ke tashi a jikin ki instead of turare,babu tsafta kullum cikin kazanta dole ya raba d’aki dake,abinci kala guda kike girka masa kullum dole nefa ya bar cin abincin ki.
Yanzu yaushe yace zaki koma?
Eh tau idan munyi kwana arba’in.
Zanyi ma nafisa magana kinsan yar gaya ce shiyoyin nijar,can garinsu sana’an da akeyi kenan gidansu gyaran jiki na amare,zawarawa da matan aure duk ta iya sosai yanzu ma ita umma tai ma magana zata fara min,yanzu dai zan daga maku kafa a fara dake tunda kwata kwata 3weeks ya rage ku koma.
Nako gode jummai Allah barku tare da mijinki.amin

Nace shawara kayayakin nan dana samu na buki ya zanyi dasu?
Gaskiya kudadenki tunda suna da dama a saya maku fegi(land)kinga idan Allah ya hore ku gida abunku su baba su koma ku huta biyan haya.
zanuwa da sabulai ki raba gida uku,guda na mama,guda naki,guda ki ba mijinki kice kason yan uwanshi ne kiji mai zai ce kota haka zaki samu shiga wurin dangin shi koda bai kaiki inda suke ba, kayan baby kuma ki aje mata abunta idan ma buki ya kama baki da abun bayar wa kina iya dauka ki bayar.

Am so impress wai yaushe kika yi hankali haka jummai?zama cikin masu hankali mana,lokacin da nake cikin ku in banda k’ara izani da kuke yi ina aikata rashin hankali babu abunda na k’aru dashi sai zallar QURUCIYA.

Na tuna bani adu’oin na fara daga gobe sabida bamu da enough time.

samu biro da takarda,shinfid’e baby tayi cikin gadonta ta dauko sabon memo mai hotun baby da biro ina jinki mallama maryam muhammad raji.

Bara mu fara da wurudi(lazumi kenan)

1-ki yawaita salati ga annabi(SAW) a k’alla koda sau d’ari ne a rana Allah zai biya maki kowace irin bukata da kike dashi,saba’in a lahira,talatin a nan duniya.kinga ko muna da bukatu da dama.

neman gafara domin kin tafka kura kurai da dama kafin kuyi aure koshi na iya hanaku samun kwanciyar hankali.
ki laminci karanta
Subhanal lahi sau talatin da uku(33)

alhamdulilahi sau talatin da uku(33)

Allahu akbar sau talatin da uku(33)
Sanan ki cike na d’arin da
“la’ilaha illal lahu,wahdahu la sharika lahu,lahul mulku wa lahul hamdu wa huwa ala kulli shai’in kadir”
Idan kika rik’e wanan Allah zai shafe maki zunuban ki koda sun kai yawan ruwan teku ne.
kuma kina iya hadawa da
“subhanal lahi wabi hamdihi” sau d’ari(100)
ko
“astagfirul lahal lazi la ilaha illa huwal hayyul kayyumu wa atubu ilaihi”
Sau uku a duk lokacin da kikayi sallah.

haka idan lamari ya dagule maki,kin shiga mumunan kunci da rasa mafita,to tashi kiyi alwala,ki fuskanci alk’ibla karanta fatiha,ayatul kursiyyu da suratul-tinni sai inna anzalnahu,sanan ki daga hannunki sama rok’i Allah bukatan ki,Allah zai amsa.

insha Allahu zan dage dayi..
Adu’oi kuma akan mijin nan naki kinsan burtsatsen namiji ne.

ki kyautata alwala kiyi sallah raka’a biyu sai ki karanta aya ta goma a cikin suratul khafi kafa dari uku da goma sha uku(313).

Idan kuma kishi ya ko dangin miji ne suka taso ki gaba ki tashi cikin dare yi alwala kiyi sallah raka’a biyu sai ki karanta
astagfirulah sau dari(100)
lailaha ilallahu sau dari(100)
Allahuma sali ala sayidina muhammadun wasalim sau dari(100).

na sanki da saurin fushi allawiya ga afu’ar yaye fushi;-lailaha illahuwal azimul halimul la’ilaha illahuwal rabbul arshil azim,la’ilaha illahuwa rabbus samawati wa rabbul ardi wa rabbul arshil kareem.

Amma wani lokuta ya kamata nayi wanan adu’oin?
Ko wane lokaci kina iya yi musaman ma idan kina cikin tsarki.
amma lokuta da wuraren da ake karbar adu’a sune;

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button