HAUSA NOVELKURUCIYAR JUMMAI Complete Hausa Novel

KURUCIYAR JUMMAI Complete Hausa Novel

Daren lailatulk’adir
Yankin dare na karshe(daga karfe ukun dare zuwa asalatu).
Gurbin sallolin farilla(lokacin sallar farillah).
Tsakanin kiran sallah da ik’ama.
Lokacin saukar ruwan sama.da dai sauran su

wayan allawiya yayi ringing,tace kinga babanta ne ya kira maybe yazo ne,nima kin tuna min wayata a kashe take nasan uncle ya neme ni.insha Allah idan na zauna zamu ci gaba hadda nafiloli zan baki.

Tare suka fito,gaisawa jummai tayi da alhaji sadat
godia sosai ya mata akan hidimar da tayi musu,sai da safe tama allawiya ta shige gida tare da rufe kofar sabida kowa ya shigo.
bata samu daman yin wanka ba sabida dare ya raba alwala tayi ta sauya kaya zuwa na bacci ta haye gado tare da kunna wayanta text kawai ta gani na uncle yana mata ban gaji tayi reply har bacci ya kwasheta bai kira ba.
*asuba ta gari mallama maryam salis (mrs raji)*

*LEEMA*✍????

*⚜BRILLIANT WRITER’S ASS*..????

????????????????????????
????????????????????????
*QURUCIYAR JUMMAI*
????????????????????????
??????????????????????

*HALIMATU SADIYA MUHAMMAD*
*LEEMA*✍????

*Ramlat ar manga(real me dambu)ina taya ki murnar kamala littafin ki mai suna”KISHIYATA JAHADINA” gaskiya ya k’ayatar tare da nuna dumbin darusa jazakallah,inda kika yi kuskure Allah yafe mana baki da amin*

*inna lilahi wa inna ilaihi raji’un ina mika ta’aziyata gareku “”habeeba idrees da hawwa m.u(smasher)”a bisa rashi da muka yi na baba,Allah ubangiji ya jik’anshi da rahama yasa aljana fir’dausi tazam makoma agareshi,yasa can ta fiye masa nan.Allah baku hakurin rashi amin thumma amin*????????????????????????

*61-62*

 

Yau sun makara sallar asuba sabida gajiyan aikin buki haka suka tashi tare da yin sallah aka gyara gidan as usual.

Suna karya wa ne umma tace yanzu zan gagauta zuwa kasuwan gwari nasan sun fito yanzu a samu ko yan sabulai ne da zaki rik’a masu tsaraba,ah umma ai ba tafiyar safe bace tunda ba nisa yace sai zuwa karfe goma sha biu zamu wuce.
Duk daya ai gara a saya a aje in case koda ya canza shawara cewar aysha.

Baba yace shawar wari ake tsakanin uwa da d’iya ba a saka ni ciki?
Umma ttace baban su maganar tsaraba muke yi,ai hakan ma yayi kyau ni zan fita kasuwa jummai idan kun isa kya gaishe mun da su alhaji.
Tau baba a dawo lafiya.

Umma ma shirtyawa tayi ta wuce kasuwa,aysha tace yanzu kamata yayi mu amso kajin nan ayi miya dashi ko farar shinkafa ne a dafa ki wuce ma hajiya dashi zata ji dad’i,exactly sister kin kawo shawara.
Jeki amso bara na daura per boiling na shinkafa.
Da sallama ta shiga gidan nafisa,amarya ya kwanan su umma?
Lfy lau suka tashi dama kajin nan da na kawo ajiya nake bukata za muyi amfani dashi.

Tau bak’i za kuyi ne?a’a hajia zan ma abinci(white rice da stew)
Hakan yayi dai dai ga nik’a k’en tomatoe nan ki tafi dashi ku hada,mun gode fa da hidima.
Dama ina son magana dake akan batun allawiya ko zaki samu daman taimaka mata da gyaran jiki kafin ta koma?

Wanan ba matsala bane idan zata iya sayan kayayakin da zan buk’ata.
Mun gode zanyi magana da ita sai anjima,tau.

Aysha tace ke kuwa daga dauko kaji kin samu wuri kin yi zaman ki,kai sister magana na tsaya mukayi .
Hope ba sirrin mijinki kika kwashe kika fada mata ba?no maganar allawiya ne gama tomatoe ta bayar ayi miya,ok yanzu hasa wuta a murhun gawayi(chacol)ki wanke kazar ki sake soyata sai ki soya tomatoe din tunda alredy tafasashe ne.

Zuwan karfe goma har sun gama ta shiga wanka,lokacin umma ta dawo da sabulai na wanka yakai sunk’i shida,na wanki dozun uku,omo zip roal shida,sai maggi da gishiri mr chief.

Duduba kayan aysha tayi gaskiya sunyi kyau umma dai dai tsarabar yan kauye kenan,jummai ma data fito daga wanka taga kyau’n kayan.

Text ya mata cewa gashi nan zuwa sabida yau da yamma zai koma abuja,tace umma kinji ko gashi nan zuwa ma,ai anyi dai dai maza shirya da sauri kada ki tsaya nawa,aysha tace ga abinci nan ma mun dafa namu na gida na cikin kula har dare,ga na hajia dashi zata tafi.
Umma tace kunsan baban ko bai cikin shinkafa da dare sai dai na samo nashi tuwo wurin au allawiya.

super wax blue mai zanin yellow,red and white ta saka d’inkin riga da skirt,sai tar kacen yan kune,sarka,yan hanu da zobe,yadda amina ta mata make up ranar suna haka ta sake yin light make up ta shefe jikinta da turaruka ta fitar da babban mayafinta kashka yellow da takarmi half cover yellow.

Aysha da daura mata dankwali ne suka ji sallamar shi,rusunawa yayi ina kwana umma?lafiya lau ya mutanen gida,sannu da hidima fa Allah saka da aljana.
Amin thumma amin,ke fito haka nan ko wuce kada ki bata mashi lokaci.
Fitowa tayi dauke da basket inda kulolin abinci ke ciki sai babban leda na kayan tsaraba,mayafinta rik’e a hannu da purse nata

Aysha tace ina kwana uncle?lafiya lau ya amsa.

Umma mun tafi,haka da mayafi a hannu?ta aje basket din ta yafa saman kafad’a.
Kofar baya ta bude ta aje kayan,ta dawo gaba ta zauna gud morning uncle?morning yace a takaice yana mamakin hali irin na jummai.

A kofar gidan su yayi parking ta fito dauke da basket mayafi na fad’owa tana faman gyarawa suka yadda zango a paloun hajia.

Ina kwana hajia?lafiya lau ya mutanen gidan ku?
Lafiya lau suke ga abinci nan nace bara na kawo miki tace cikin jin kunya.
Ai ko kin gyauta don mijin naki yau a makare ya tashi kuma da b’akin hali ko karyawa bai tsaya yiba yace zai tafi dauko ki,dauko plate a kitchen ki zuba mashi.

Plate spoon da serving spoon ta dauko,shi dai sai dane danen waya yake yi,ta zuba mashi shinkafar kad’an sai nama kawai,dan ta lura dashi bai cikin abinci sosai sai kwalama.
Hajia yace dauki kaci,yace tau bai yi niyar ci ba amma da yaji dadin abincin bai san sanda ya cinye duka ba,ta kwashe kayan ta dauraye,hajia tace da kin barsu ai na wanke ku hanzarta rana nayi gashi ana neman ka a wurin aiki.

Tace tau sai mun dawo,ku gaishe su.

Sai da suka kama hanya sosai yace in tambaye ki mana?
Ina ji
Menene yasa bakya iya bin umurnin dana vaki?
Me nayi kuma uncle?
Wani tashen iya shege kw damun ki dazan hanaki yafa mayafi amma kin k’i hanuwa,ai da gani nayi da kike budurwa manyan hijabai kike sawa hada safa da nikaf yanzu ne da kika yi aure kike sha’awar tallar jikin ki?

Kayi hakuri naga ai babban mayafi ne kuma tare da kai zamu fita.
Oho mayafi ai mayafi ne komin girman shi,sanan idan tare zamu fita mutanen da zasu yita kallonki rufe masu idanu zanyi hadda wani make up ko?

Ya zama kai na farko kuma na k’arshe da zaki sake fita da mayafi koda vana nan ko make up,tau .

Cikin ranta tace na shiga uku wane irin mutum ne wanan mata na kwaliya mazajen su na apreciating,shi sai ruwan bala’i,yanzu yanzu zaka ga yana fara a anjima ya koma fada kamar mai aljannu.

Da ya gaji da zaman shiru ya kuna masu kira’a har suka isa kauyen kuta,a kofar wani babban gida suka yi parking,yace oya gyara mayafin nan ki aza shi saman kanki,ta gyara,sana wanan ledar fa tayi banza dashi.

Babban bishiyar mangoro ne a kofar gidan aka shimfida tabarma datijawa ke zaune suna shan iska sai yake suke faman yi,wuri ya samu ya zauna ya fara gaisawa dasu da yaren su na gwari suna amsawa cikin nisad’i,ya nuna ta tare da masu bayani da yare.
Ta shiga gaidasu,suna amsawa da fara’a duk suka mik’e zuwa qurin mota aka bude ana dudubawa da suka gama ya shiga cikin gida tana biye dashi akala part part dake cikin gidan yakai ashirin,sabida babban gida ne sosai(family house)
Haka akayita shiga da ita lungu lungu tana kai gaisuwa wasu ma ko hausa basa ji,duk inda ta shiga sai ta aje masu sunk’in sabulu na wanka guda,na wanki manya yanka uku da omo zip,haka tayi ta rabon tsaraba wasu ma kudi ta basu kasan cewar kayan basu iya va.
Anata zuwa kallon matan raji yar gayu kowa ya yaba da hankalin ta,abinci kuwa kala kala(duk wanda yasan gwara wa yasan su a noman doya)haba sakwara kwanu kwanu da miyan ganye da kaji,ko wane sai data tsakura “gata ba gwanar son doya ba”kada dai suce ta kyamace su.
An zaga da ita taga gari,shima fita yayi zuwa gidajen abokanshi na kauye sabida tun farkon rayuwar shi nan ya tashi da ya gama junior secondary schl zamanshi ya dawo hanun hajia kasan cewar kauyen babu senior secondary schl.
Sai zuwa la’asar suka ma yan kauye sallama,tsaraban doya,mango,cashuw,da kayan miya cike da buth na raji ga motar nashi karama(vibe ce)haka suka lalab’a sai da suka hau titi sosai yace nan gidan da muka fara zuwa nan ne gidan mu,inda aka haifeni kuma gidan mai unguwa da iyayen mu suka mutu ya rage k’anan iyayenmu,yanne da sauran diya da jikoki suke cikin gidan yanzu.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button