KURUCIYAR JUMMAI Complete Hausa Novel
Da dare abdulrahim ne zaune a zauren su jummai suna hira da aysha yake cewa honey badan na maki alkawari sai kin gama schl za a yi auren nan ba gaskiya da yanzu anyi domin na matsu baki shigo gida naba….haba dear idan kayi hakuri fa nan da wata takwas ne fa kamar gobr…what 8months ne kamar gobe lalai honey kin bar jin tausayina ko,bakya ma sha’awar su jummai yadda suke gudanar da rayuwar su?..ina sha’awa gaskia amma kasan kowa da yadda Allah ya tsara mashi rayuwarshi ka kara hakuri pls..babu komi Allah mana jagora amin..zan wuce ga kaya nan ki shiga dasu..an gode Allah kara budi.
Haka ta shigo gida su umma na hira da baba kasan cewa babu wutar nepa,jummai na daga palour tana karatun exams da text book..aje kayan aysha tayi gaban umma..menene kuma a ciki?..ban duba ba abdul ya ce na shigo dashi..jummai tayi chagal ta fito tare da warce ledar ta bude kayan ciye ciye ne su chocolate,buscuit sweet sai fruit irin su ayaba,lemu,kankana,apple da abar bar..baba yace oh Allah bai bamu fiya maza ba amma ya bamu sutukai masu kula damu kamar mu muka haife su..umma tace haka ne mallam duk wanda yayi hakuri a rayuwa sai kaga daga baya Allah ya azurta shi ta hanyan da bai zata ba…haka ne saratu Allah maku albarka baki daya ya kara rufa asiri..su jummai suka amsa amin baba..haka aka shiga ciye ciye har aka gama kowa yayi hanyar daki..Wayan jummai ya fara ringing uncle ta gani a rubuce saman scream din wayan..helo uncle ya gajiyan aiki?…babu gajiya ya jikin ki?…naji sauki..me kike ci haka naji bakin ki na motsi?…yaya abdul ne ya kawo mana kayan fruits dasu chocolate..nan kika fi auki ai wurin ciye ciyen..yasu umman?lafiya lau suka dama gobe zan je gidan hajiya…babu inda zaki sai kin gama exams sai son yawa ko tarewa baki yi ba a gidan miji amma sai shegen yawon tsiya ya kashe wayar shi…can ta matse maka dama haka kake daga abun arziki ka maida na tsiya ai gidan kune sai me daga ka hutar dani ba…aysha tace keda wa kuma..wa kika sani sister banda dan rainin hankalin nan raji…yau kuma jummai masoyin naki ne dan rainin hankali,ai hakuri ake yi kacokan auren kanta zalar hakuri nefa,dole sai wani ya dane zuciyar shi tsakaninku sai a zauna lafiya tun ba a kai ko ina ba kin fara mayar masa da martana..kada ki sake babu kyau..naji(asuba ta gari mrs raji da mrs abdul)
Alhaji saddat ne yazo bayan sun gama gaisawa da iyayen allawiya ya nemi alfarman allawiya ta bishi su koma sabida zai yi tafiya zuwa maleysia sai ya shafe wata guda zai dawo yana so su tafi tare..maman allawiya tace gaskia a al’adance sai mace tayi kwana arba’in zata zaga gidan dangi ta gaida kowa da kowa sanan ayi shirin koma warta gidan miji tare da kayan gara da za ayi mata,don haka yayi hakuri ya tafi wutin aikin shi dai dai koda zai dawo an gama komi sai su wuce tare…baba yace kuma ya kamata ka kaita kano taga yan uwanka duk da wasu sun zo lokacin haihuwa amma ya kamata itama taje can din su santa..yace haka nayi shawara dama idan na dawo daga maleysia muje can kanon tare,yanzu babu matsala ta zauna din har in dawo sai mu wuce kano ga kayan abinci nan da kudi..godiya suka mashi.
Da suka kebi ya jaguli matarshi son ranshi..zanyi mising naki my heart desire,pls ki kula da kanki da mamata(rahma)..kada ka samu damuwa am all yours sweet fata na dai kai mana adalci ka ji tsoron Allah tare da tsare mutuncin ka a duk inda ka kasance..insha Allahu zan kiyaye,kaya sunyi ko akwai abunda kike bukata?..babu komi mijina Allah tsare min kai .amin makulin mota na hanun abubakar idan kina da bukatan fita anguwa sai ki kirashi ya kai ki, sai munyi waya sabida da safe jirgin mu zai tashi bye..bye bye ya wuce
Haka rayuwa ke tafiya jummai da raji yau fasa gobe a shirya,duk bau da hakuri wani bai iya dane bacin ranshi daya taso mata tun tana masa shiru har ta fara mayar da martani..sai sun gama fadan su a waya ta fara kuka tana fadan data san haka aure yake kullum cikin tashin hankali da bata yiba..wai cikin tana sonshi kenan ma take tausar zuciyarta da sun gama tayi mashi text na ban hakuri,na nuna tayi nadamar abubuwan da ta fada mashi na bacin rai..ta dalilin haka yaki zuwa weekend ma sabida ko da yazo baccin rai zai tarar duk da kewarta da yaji.Gashi har sun gama weac yau za suyi hutun sati uku su fara neco.
Yanke shawara tayi da ta na zuwa gidan anty balki matar yayan su amina neman shawarwari yadda zata gyara tsakaninta da mijinta..dama suna shiri sosai da anty balki…text ta mashi na neman izinin fita..reply yayi a dawo lafiya,dreess properly and don’t stay long..dadi taji a ranta tashirya cikin riga da zani na atamfa sharaton da hijab har kasa sai nikab data saka..umma zani gidan anty balki..a dawo lafiya tau..a daidaita ta tsayar zuwa bosso estate har kofar gidan ya sauke ta,already anty balki tasan da zuwanta,bayan ta sallame shi ta shiga..tunda ta bude gate ta fara jin kamshin turare mai dade na tashi har ta isa kofar palour tayi nocking..wata bufurwa yar kimanin shekaru goma sha uku ta bude mata kofar..tace anty balki na ciki?
Eh shigo..ai lumshe idanu jummai tayi sabida kamshin turaruka ne iri iri ya hade da sanyin AC ya bada wani kamshi na masamman…palour ne babba babu wasu tarkacen kaya daga set na kujeru sai kayan kallocan gefe kuma daga saman wani step bargo ne babba a ka shimfida a kasa aka jera trow pillows yadda kasan inda matan sarki ke hutawa.
Anty balki ta fito cikin karamin riga iya guiwa pink mai hanun vest,kanta yasha k’ananan kitso sai kamshi ke tashi a jikinta…sannu da zuwa maryam amarya yasu umma?..lafiya lau anty..yanzu sai kinyi hakuri mijina na ciki wanka zan masa na shirya shi ya fito sanan mu fara magana ..karima kawo mata abun motsa baki..yarinyar da aka kira da karima ta cika ma jummai gaba da drink da snacks ta koma inda take renon yara…jummai cikin ranta tace tab ashe yar iskan mata ce wanka kuma ayi ma namiji,a shirya shi,sanan ko kunya bata ji da wanan figagiyar riga ai dole su amina suce ta mallake masu dan uwa.
Jummai takai minti talatin zaune anty balki ta fito rungume da mijinta sai shagwaba take zuba masa haka matsar kwala..jummai sake baki tayi cikin nikab tana kallon ikon Allah..tace ina wuni yaya..lafiya lau amarya yau an tuna damo,yasu umma?lafiya lau suka..hanyar waje suka yi haka tayita zuba masa shagwaba jumma na leken su ta window taga anty balki ta zauna saman cinyar shi,yana zaune saman driver sit yace baby yanzu zan dawo ba dade wa zanyi ba kinji…naji take care of yrself..i will ta hade bakinshi da na hot kiss ta bashi sun kai minti biyar..yace i will miss u baby badan fitar nan ya zama dole ba da babu inda zani ko zaki shirya muje tare? Kasan inada baku’wa ka dawo lafiya ina gaida su mami..zasu ji ja ga motar shi.
Ta dawo cikin gida sorry maryam idan yana gida bana da hidima sai nashi,bana da time na kowa sai nashi har sai ya fita koda bai bukatan komi ina nan tare dashi har sai ya fita…uhmmm sanu anty.
Maryam naji bayanin ki ta waya kuma naji dadi da kikayi shering matsalarki da ni atlest u wil learn one or two things a wuri na.
Da farko aure kacukan kanta ibada ce,kuma dole idan zaki gmyi ibada ki natsu ,ki mai da hankali, kiyi hakuri ,ki danne zuciyar ki,ki saukar da kanki domin cin ribar ibadan nan.