KURUCIYAR JUMMAI Complete Hausa Novel
Bara na baki wani guntun labari kafin muyi aure soyaya muke kamar mu cinye junan mu da mijina,ni yar zuru ce,na taso cikin lovely family,one big family,iyaye na ba masu arziki bane,rufin Asirin Allah ne,mahaifina primary schl teacher ne,mamata kuma cleaner ce a federal medical center birnin kebbi,kebbi state ,mun taso cikin gata,kulawa da wadata ban taba ganin iyayena sunyi koda musayar magana bace idan babana yace yes,ya zauno babu wanda ya isa yace no koda kuwa no din nan is the right thing..bani da wani buri lokacin da ya wuce nima nayi aure nayi rayuwa irin yadda naga iyayena suna yi cikin farin ciki da anashuwa,bayan nayi aure ko sati ba ayi ba kullum sai munyi fad’a da mijina,in yita kuka ina hada kayana zan bar gida..sai dai ya rarasheni akan bazai sake ba,stil gobe ma the same thing fada,ke tun yana rarashina har ya fita batuna da mun fara ya tsalake ya barni naci kuka har nayi hakuri..ke har mukayi sati hudu babu abunda ya canza na zaunar dashi nace gaskiya ka sawake min domin shine kawai mafita na gaji da zama cikin bacin rai tun kafin mu samu haihuwa diyan mu su taso suga irin zamar da muke yi..yace balkisu walahi bazan sake ki ba sabida ina sonki…haka muka ci gaba da zama har wata nace ya kai ni gida lokacin na fasa ma mama halin da nake ciki, kin san me ya kawo mana rashin jituwa?
Da farko da ya fara naman aure na kullum sai yazo hira safe,rana,dare bamu da hira sai na yadda zamu rinka romancing junan mu idan munyi aure,yara nawa zamu haifa,sau nawa zamu rinka yin sex..bamu tsaya mun fahimci halayen juna ba, likes and dislikes nawa da likes and dislikes nashi ba,wani irin abu ke faranta masa rai,wani irin abu ke bak’anta masa rai,wani irin abinci yafi so,wane colour ne best colour nashi,wani irin kaya yafi so mace ta saka da sauran su,haka shima bai san duk wayan nan abubuwa ta bangare na ba…aka yi aure yau nace ina sha’awar cin indomie sai yace shi kuma shinkafa zai ci,mai makon ni na hakura da choice dina mubi nnashi sai nace lalai sai abunda nake so shi zai min kinga kuwa ban nemi zaman lafiya ba,choice namu bai taba zama daya ba..instead of a matsayina na mace wadda take kar kashin shi na sauke girman kai,nayi hakuri tare da bin ra’ayinshi koda hakan ya sab’a ma nawa ra’ayina abun ya fara isa na,na zauna nayi tunane shin dama haka aure yake?iyayen mu da sukakyi shekara da shekaru a gidan aure dama haka suka yi hakuri?ina fa son mijina yana sona menene ya kawo maga rashin ji tuwa…research na fara yi akan aure,tare da neman shawarwari na manyan mallamai mata wa’yan da suka dade a gidan mazajensu sabida am new into the system…bayan na gama ne ya zauna na natsu na fahimci mijina da duk abinda yake so dama wa’yanda baya so,nasan dai ance zo mu zauna ko mu sab’a..iban ma wani abu ya shiga tsakani na dashi na rashin jituwa hakuri nake bashi cikin kwanciyar hankali koda ni keda gaskiya har shima da kansa ya ne halina muna zama lafiya yanzu,idan ma laifi yayi min sai na bare ya gama yawon shi ya dawo gida zan ce masa idan ka samu time ina da magana dakai..nan zai ce balkisu ko zauna fadi maganar ki,sai nace abu kaza da kamin lokaci kaza banji dadin shi ba,kinga babu halin fada sai yace yi hakuri balkisu bazan sake ba final ya wuce.
Yanzu shekaran mu bakwai da aure,babu wanda ya fini sanin mijina hata uwar data haife shi,shi yasa nayi b’akin jini wurin yan uwan mijina,sabida yadda nake kula dashi tare da tarairayan shi.
An kira sallah muje zuwa sallah idan mun idar zan baki wasu hints na zaman aure…….
*LEEMA*✍????
*⚜BRILLIANT WRITER’S ASSO*…????
????????????????????????
????????????????????????
*QURUCIYAR JUMMAI*
????????????????????????
????????????????????????
*HALIMATU SADIYA MUHAMMAD*
*LEEMA*✍????
*Edited by*;-
*LEEMA*
*Dedicated to my lovely son”jafar abubukar tambuwal”*
*Readers kuna ba mai rai dariya walahi*????????????
*Masu magana a group da masu bina private naga tambayoyin ku kamar haka*;-
*Don Allah ke matar aure ce*?
*Kina sayar da magunguna ne*?
*Menene ma’anar ‘LEEMA’*?
*Hummm babban magana*????
*Halimatu sadiya dai ba matar aure bace mai niyya ce insha Allahu nan da k’an k’anin lokaci*
*Bana sayar da maganin komi,abinda mutane basu fahimta ba shine rubutu ba k’aramin aiki bane musamman idan kana son mutane su amfana kuma sak’on da kake son isar wa ya isa ga al’umma dole sai kayi reseach sosai,kamar yadda muka sha fada maku mu yan brilliant writer’s bamu rubuta labari kara zube sai mun tabatar da ingancin labarin,garuruwan da zamu yi amfani dasu cikin labarin sai ka nemi mazauna garin ka samu information akan garin da wuraren dake cikin garin,so idan mutum ya kawo maka labari kai zaka natsu ka tantance menene da menene ya kamata na k’ara a cikin labarin nan wanda mutane zasu amfana dashi sai kayi research,menene da menene zan rage a labarin nan sabida rashin ingancin sa ko rashin amfaninshi ga al’umma another research(sabida haka rubutu na buk’atan natsuwa da bincike)in har da gaske sak’o mai amfani kake son isar wa ga al’umma,maganan sayar da magani bata taso ba yadda kuka gansu nima haka na nemo kuma na gansu na rubuta,ina fatan bayanin da nayi ya wadatar*
*ma’anar leema kuwa Ha/leema,kunga HA aka cire cikin haleema ya bada leema,da fatan kun gamsu ,nagode sosai da kulawa,jazakallah*????????
*65-66*
Bayan sunyi sallah,sun ci abinci tace bara na baki a gagauce sabida nasan duk inda yake ya kusa dawo wa gida..idan kuwa ya dawo am sorry to say bara ki samu kai na ba sai wani lokaci…babu komi anty ai kota nan nak’aru.
Allah da kanshi yace;mace ta gari ita ce mai kamewa,mai biyayya ga Allah,da kuma mijinta,kuma mi kiyaye duk wani hak’i na mijinta ida yana nan ,ya fita ko yayi tafiya…akwai ayoyi da hadisai da yawa da suke bayana matsayin mace ta gari wurin Allah
manzon Allah(SAW)yace;Duniya wani d’an wuri ne na jin dad’i,amma mafi jin dad’in abin dake cikin duniya shine mace ta gari.
Haka kuma wani hadisi da ibni hibban ya rawaito daga Abi wak’as(RA)yace manzon Allah(SAW) yace;Wanda duk Allah ya bashi abu hudu a duniya,to wanan mutum Allah ya bashi jin dad’in duniya baki d’aya,sune;-
Mace ta gari wacce in ka umurceta sai ta aikata abinda ka umurceta ba tare da ranka ya b’aci ba,idan kayi fushi sai ta rarasheka,in ka nemi hak’in auran ka sai tazo a duk lokacin da kake so,idan kuma ka kalleta sai kayi farin ciki…shin maryam cikin wa’yan nan abubuwa da aka ambato wane daga ciki mijinki ya samu a gare ki?…cike da nadama ta girgiza kai babu anty.
Maryam nasan ke yarinya ce k’arama,amma tunda aka riga aka maki aure kin wuce wanan stage din na yaranta,ki nutsu,ki saurari abinda zan fad’a maki,don Allah ki wanke zuciyar ki,kiyi duba da nazari,kiyi tunane,ki auna shin abinda zan fad’a maki gaskiya ne domin mu gudu tare mu tsira tare.
Na farko juriya da hak’uri;a duk lokacin da mijinki ya bata maki,ko ya shiga wani hali na rashi,kiyi hakuri tare da jure wa.
Kiyaye sirrin mijinki,kada ki yadda ko iyayen ki susan abinda ke tsakanin ki da mijinki,idan ma sab’ani kuka samu,fada ne,rashin jituwa ko wani jarabta na ubangiji ya same ku,hakuri zaki yi kina kai kukanki ga mahalici,domin idan kika dubi halin da wata ke ciki a gidan mijinta sai ki gode ma Allah,kamar ni yanzu bani da abokin shawara daga littafai sai wayana,idan kina research zaki samu wata mai matsala irin naki,har ma wanda yafi naki kuma ta nan zaki samu maganin matsalar ki ba tare da kin fada ma kowa ba.