KURUCIYAR JUMMAI Complete Hausa Novel
Da dare suka zauna da aysha suka yi list din irin kayan da take so a saka a cikin lefe…kai sister sunyi yawa fa..ai haka ake yi kinga idan ma sunyi yawa can wa yanda zai aika zasu rage kayan ne…tau shike nan.
Da dare da ya shigo zobo kawai ta bashi don yace bai jin yunwa,haka suka sha hiran su na soyaya,ta bashi list din..kai baby ai sunyi k’adan kayan..ah uncle ina cewa ma sunyi yawa…No baby ai right naki ne insha Allah zanyi kokari..Allah k’ara bud’i na alheri.amin sai munyi waya kennan dan bazan shigo ba da safe,ranar monday ki shirya fa da wuri,..hugging nashi tayi Allah tsare ya kare ka a duk inda kake…amin baby light kiss ya bata a lips nata sabida baya son jawo ma kanshi aiki da daren nan haka suka rabo cikin shauk’in juna.
Haka ta kwana cikie da kewar mijinta,ranar sunday tunda safe baba ya wuce mahuta kwana biu yayi suka had’o shi da buhun masara,buhun gero,buhun dawa,buhun shinkafa biu shashara…shawara ya yanke akan ya sayar ya kunsa kudin shi ya dawo gida ya sayi wasu tunda bai iya dauko su daga can,daya sayar kwata kwata dubu ashirin ya tashi dasu,dole ya had’da ba babban gonan shi na gado da aka saya dubu talatin,duk kudin sun kama dubu hamsin,haka baba ya dawo gida cike da takaici………
*LEEMA*✍????
*⚜BRILLIANT WRITER’S ASSO..*????
????????????????????????
????????????????????????
*QURUCIYAR JUMMAI*
????????????????????????
????????????????????????
*HALIMATU SADIYA MUHAMMAD*
*LEEMA*✍????
*Wanan shafin naku ne member’s na”HAUSA NOVEL’S ONLY”Group*
*Kuna a birnin heart d’ina masoyya na hak’ik’a*;-
*maimunat S kole*
*Hauea Ado Ahmed*
*Ummiabdallah*
Da ma sauran member’s na ‘HAUSA NOVELS ONLY”group kuna rai na soyayar ku a gare ni bata fad’uwa sai fatan Allah ya bar mu tare ya k’ara soyaya da aminci,amin.????????
*Daga taskarrrrr marubutan muuuu;-*
*kada kubari a baku labari brilliant writer’s sun sake dawo maku da wasu zaffafan littafai wanda shahararun marubutan nan kamar haka suka kawo maku*;_
*Rubutacciyar Al’amari by jamila musa(meelat)*
*&*
*Ummu affan*✍????
*Dace da juna by Saleehat*✍????
*Kishiyata by maryam hassan muhammad(little)*✍????
*musha karatu lafiya*????
*Nida ya Moha by Ramlat ar manga”real mai dambu zuciyar meelat musa*
*69-70*
Haka baba ya dawo rai ba dad’i,shawara umma ta bashi da a aje kud’in cikin account na jummai zuwa nan gaba idan an samu k’ari,idan ma ba a samu ba su tatalashi haka nan ko yar katifa so saya mata….haka kuwa a kayi jummai takai kudin bank.
Su jummai an fara neco sosai kai ya dau zafi,kullum ckin karatu take,bata samun kiran mijin ta akai akai kamar lokacin baya,sai shi in aiki ya masa sauk’i ya kirata,lokaci sai tafi yake yi ta bangare biyu’n shirye shirye ya kankama na bukin auren jummai.
Aysha kam ta gama exams tana ci gaba da zuwa koyon aiki a wani private lab”” ganisol laboratory “” dake k’asan layin su,soyaya tsakaninta da abdul sai abunda yayi gama..ta b’an garen yan uwanshi kuwa kowa yasan labarin aysha sun matsu bata shigo cikin su ba sabida natsuwan ta.
Allawiya ansha gyarana jiki har an gaji,sabida anty balki taba jummai shawara da kada a fara mata yanzu ta bari har ta gama exams,ta samu natsuwa hankalinta ya kwanta,babu inda take zuwa sai a fara gyaran fata da sauransu,amma taci gaba da amfani da had’e had’en da aka mata na k’arin ni’ima….Allawiya taso kwarai alhaji sid ya bari a gama auren jummai sai ta koma gida,ya nuna rashin amince wa sabida yayi missing nata sosai,musamman yadda yaga ta k’ara kyau,tayi fresh komi ya k’ara cika,ya matsu basu koma gidan su ba.
Ranar asabar da yamma bayan jummai ta dawo daga schl wurin rubuta exams aka shirye Allawiya sosai tasha lale(zanen flower)na bak’i da jan lale,ga guiguyayen kan nan yasha mayukan gargajiya na tadda suma ya k’ara bak’i,tsayi da shek’i aka yarfa mata kitsun ta kanana gwanin sha’awa…amina ta mata light make up tayi kyau sosai domin yanzu jummai ta hana ta shafe shafen nan na mayukan bleaching..mai na musamman anty balki ta had’a masu na gyaran fata dashi take amfani yanzu.
Mota biyu alhaji saddat ya aiki dashi guda na kwasan kayan gara,guda na daukar mutane dama daga umma,jummai,amina sai allawiya..already ya sa an share gidan an gyara..da suka isa umma ta kara mata nafisa sosai mai ratsa jiki tayi masu sallama…jummai da amina suka k’ara gyara gidan yayi tsaf dashi kamar na wata sabuwar amarya shawar wari suka bata suka suka kama gaban su…da dare wanka ta k’ra yi ta sa wasu fitinanun kayan bacci,bayan ta k’ra turare gidan tayi ma baby rahma wanka ta aje ta cikin bed nata sai bacci….da sallama ya shigo ta tarbeshi da fara’a(abunda bata taba yiba kenan da can)kaji biu ya sayo da hollandia yuoghut,suka ci suka sha sai hamdallah…ruwan wanka ta had’a mashi yayi wanka ta fitar mashi da jalabiya milk colour..bayan ya shirya kamar maye ya fara laluban ta haka sula faranta ma juna rai cikin natsuwa basu runtsa ba cikin daren nan..sai da akayi kiran sallah sukayi wanka,lokacin baby rahma ta tashi sai tsala kuka take yi,da sauri ta fito daga toilet ta amshe ta,pampers ta fara cire mata tayi mata tsarki da ruwa masu dumi ta zauna cikin natsuwa tana shayar da ita…haka ya fito daga wamka ya same su gwanin sha’awa…murmushi yayi Allah maki albarka allawiya ban taba samun natsuwa dake ba irin jiya,fatana Allah sa farin ciki ya d’aure a cikin gidana,ya bani ikon kula daku…amin mijin ina mai nan afuwar ka akan abubuwan da suka faru a baya laifina ne,nice ban baka kulawa yadda ya kamata ba amma insha Allah hakan ba zata sake faruwa ba…haba my life nima da laifin nawa tunda ke yarinya ce kina ta aikata abubuwa cikin rashin sani amma ban lurashe ki ba na saka maki idanu muna ta kwasan zunubai nima ki yafe min matata…babu komi ya wuce Allah bar mu tare amin,na tafi masallaci..data gama shayar da ita ta aje ta itama ta kabarta sallah….haka rayuwa mai dad’i ya kasance a gidan allawiya da mijinta tana kokari sosai qurin faranta masa,kuma tana kulla da yar ta iya gwarwado,shima yana kokarin sauke duk wani hakk’i nata da Allah ya d’aura mai.
Ta ban garen raji kuwa duk wani abu da ake buk’ata na kayan lefe da kayan lale duk ya h’ada..matan abokin shi dake lagos ya tura ma kudi aka sayi lesuka yan uban su kala goma,material kala biyar sai takalma da jakuna kala goma da akwati purple mai ratsin fari(best colour nashi fara jummai kuma purple)aka aiko mashi da kayan abuja…na kano kuma tare suka je da antyn shi dake kuta dama busineas dinta kenan idan za ayi aure a bata contract na had’o kayan lefe,tado suje tare da jummai ta zab’i abunda take so da kanta, ba da raji ba..amma jummai na exams.
Tamfofi daga manya zuwa k’anana kala goma,shadda biyar,hijabai kala goma,gyale kala shida..bai so a sayi gyale ba anty tace kada ya kuskura yama diyar mutane kulle sabida wani dalili nashi na banza wai kishi,ai ko manyan mallamai yanzu matan su na saka gyale zuwa programs,gidan buki ko cikin gida tana iya rolling gyale tai masa kwaliya.
Vest da half vest kala goma,breziar kala goma sha biu,under wear skirt kala goma sha biyar,skin tight kala goma,slepping dress kala goma,jalabiya kala biyar,english wears kala biyar,darduma kala biyu,sai tarkacen kayan make up,su sark’a yan kunne,da yan hannu,da kayan man shafawa,sabulai, da sauran tarkace..haka suka dawo lefe ya kamalu a abuja suka tsaya ta shirye kayan cikin akwatuna dole hand bags da takalma cikin ghana most go aka zuwa akwatuna sun cika..ita ta wuto da kayan zuwa minna gidan hajia sabida bazai samu zuwa ba sai satin buki..