HAUSA NOVELKURUCIYAR JUMMAI Complete Hausa Novel

KURUCIYAR JUMMAI Complete Hausa Novel

Waya yayi da abokin shi muktar sabida ya dauk’i su muhamamd da bello(abokan nura)aje a sauke kayan da yayi order a gyara palour..koda suka isa motar kaya na jiransu a kofar gida,gate suka bud’e aka shiga da kayan ,muktar na bada order yada za’a yi arranging kayan…royal chairs ne purple and white set guda aka jera a babban palour’n,sai center carpet the same colour da cen ter table nashi..babban plasma tv ne na company LG aka aza saman tv stand,sai decodar na DSTV da Manyan home theater,aka aza manyan frame guda uku na ayatul kur’siyu,falaqi da nas palour’n ya tsaru gaskiya..dama goga raji ya bada order kada a sa curtains sai ranar da zaa kawo amarya.

Su jummai an k’are exams sai fatan samun sakama ko mai kyau, haka ta rabu da friends nata wayanda akayi zaman mutunci tana mai cike da kewar su””da yake federal schl ne”most of the students ba yan gari bane daga other state suka zo karatu,d’a d’aiku ne yan gari kuma sun mata alkawarin zuwa wurin bukinta idan Allah ya yarda,sabida tun tana b’oye tana da aure har suka gane dalili kuwa bakin amina bai da linzami..jummai taso zuwa senfort walima da za a gabatar nasu a schl din mijinta ya nuna rashin amince warshi,haka ta hak’ura.

Buki saura sati biu hankalin baba ya tashi kwarai da gaske bai samu talafu wurin kowa ba ga lokaci na tafiya..umma ta bashi shawara da tunda d’akuna biu ke gidan jummai cikin dubu hamsin din nan a saya mata gado d’aya d’ayan dakin kuma a saka mata katifa.

Haka ko akayi jummai taje bank ta ciro kudin,maman allawiya tace ga shawara mai zai hana muje gidan dailu dilaliya ana samun kaya masu kyau wa’yanda basu sha jiki ba mu saya mata gado can?…umma tace tau muje mu duba.

Da yamma suka shirya sai gidan dailu dilaliya,koda suka isa an kawo mata wani set na italy’n bed wai mai shi aure da wata uku miji ya saketa yanzu kudi suke so ta koma makaranta…gadon sabo ne gaskiya da dressing mirror nashi,wordrop da site drower..umma tace nawa soka ce ,dailu tace gaskiya dubu d’ari suka ce..maman allawiya tace haba dailu an zama d’aya fa gaskiya dubh arba’in zamu biya…uhmm kun so kanku da yawa ai ko su dubu dari biyu da hamsin suka saya dan suna bukatan kudi ne tace a sayar haka….umma tace a taimaka mu bada dubu hamsin walahi shike nan ma a hanuna ko mi bamu saya bafa na kayan aure.

Tau maman aysha bazan k’ita taku ba amma bara na kira yarinyar kuji ta bakinta..ai ba wai mun karyata ki bane abunda muke dashi kenan.

Yanzu dai bara na kira taa waya idan ta amince banda matsala,akayi dialing number ta dauka,dailu tai mata bayani…gaskiya bai baru haka ba ina laifin dubu tamanin?maman allawiya ta amshi wayan baiwar Allah ki taimaka mana mu rufa ma junan mu asiri,kina sun kudi muna son kaya ko ba haka bane,gaskiya idan ya maku dubu saba’in ku biya domin idan kun duba kayan nan babu abunda sukayi fa kuma ko a saba’in din na fadi sosai….haka ne amma kiji tausayin mu ki kara ragewa walahi dubu hamsin nazo dashi”cewar umma”
Mama kun so kanku da yawa idan mai yi maku saba’in ba kawai mu bar shi,babu komi yarinya mun amince ama yanzu hamsin zamu bayar zuwa gobe a ciko saura…shike nan Allah sanya masu albarka don Allah ku cika alkawari mama…ai ba za ma a dauki kaya ba sai an cika kudi cewar umma.

Dubu hamsin suka ba dailu akan ta adana masu kayan har su tashi dauka…tace nata kason fa..maman allawiya tace nayi maki alkawarin dubu biyu….a hanya umma tace shin wai ke ina zamu samu cikon dubu ashirin?kada ki damu maman aysha Allah na sane damu insha Allahu kafin gobe zai bude hanya na alheri…haka suka rabu……da suka dawo ne aysha tace umma hajia tazo tayi ta jiranki baki dawo ba tabar sak’o a fada maki gobe za a kawo lefe…Allah kai mu kawai tace domin hankalinta baya jikinta komi ya daburce mata sabida idan baba yaji labarin gado kawai ta saya da dubu hamsin ran sa sai yayi mugun baci ko katifa ba a saya ba….raji ya kira jummai cewa za a kawo lefe gobe thursday shi sai wani sati zai shigo….bayan sun gama waya take fada ma allawiya batun kawo lefe,tace sai ta shigo…ta kira amina kuma ta fad’a mata,yanzu mai ya kamata ayi na masu kawo kaya?

Jummai tace dama ana yin wani abune ba tukuici ake bayar wa ba?….ah besty yanzu ai an bar bada tukuici kaji ake soyaa masu kamar guda biyar haka da drinks ko katon biyu ne…tab ina zamu samu kudin sayan kaji har biyar?….haba kibar magana haka mana kamar ba musulma ba Allah zai kawo sai nazo goben…ok Allah tashe mu lafiya amin….mami tace keda wa awaya?….walahi jummai ce har ta bani tausayi lefenta za a kawo gobe kuma basu da abun ba masu kawo lefe,ina tunanen ma komi fa basu saya ba na auren nan?

Ayah poor them shine ai nake kokari nayi ma baban ku magana da khadija ko akwai abunda zasu iya yi akai…pls mami ki taimaka basu da ne suna cikin halin rashi…kada ki damu my daugter maganan kaji kuma gobe da safe ki tuna aje gidan gonar baban ku a yanko guda biyar d’in su gyara sai ki soya masu,drinks kuma ga 5k on your way ki saya masu nidai bazan samu zuwa ba muna da meeting a office,daga baya naje….mami u are the best Allah saka da alheri mun gode..haba baby yima kai ne,duk fa wanda ya taimaki wani Allah zai taimake shi.

Haka kuwa akayi tayi ma jummai waya akan zata zo da wa’yan nan abubuwa godiya sosai tayi ma ta…take fada ma su umma ai gashi yadda suka yi da amina hada kukan farin ciki umma tayi a cewarta mami ta fitar da ita kunyan surukan ta.

Jummai gidan nafisa ta shiga ta amso had’e had’en da zata fara amfani dasu
Na farko hadin gyaran fuska…man zaitun mai kyau,zuma da kwakwa aka guga ta aka tace ruwan sai ta hade su wuri guda..su zata rinka shafama fuskarta yayi 10minut a wanke.(ga masu pimples da black spot yana kashe su sosai)

Na gyaran fata kuma…kur kur,dilka,zuma,kwai da lemun tsami ta hade wuri gudakamar yadda ake kwaba lalle”amma yafi kwabin lale ruwa sai a shafe jiki da fuska bayan awa guda a shiga wanka.

Ta hade mata na sa laushin jiki…lalle,kwaiduwar kwai(egg yolk)guda uku,manja cokali uku sai kurkur…shima kwabawa tayi ,tace ki shafe jikin ki zuwa awa guda sai a wanke da ruwan dumi.

Had’in sabulun wanka…dettol,sabulun ghana,garin zogale,fararr albasa a hade wuri guda a k’irba su cikin turmi ana wanka dashi,ana wanke fuska(ga masu k’urajen fuska,yana kashe pimple da black spot)

Ga wani hadin na musamman dana hada maki…lemon tsami,tatacciyar madara,danyen kwai guda d’aya da ayaba…matse ayabar nayi da hanuna bayan na bare ta,na zuba tataciyar madarar shanu,na fasa kwai farin na zuba banda kwaiduwar ta(yolk) sai na matse lemun tsami ciki na gauraye ..ana shafe jiki yakai tsawon awa guda a wanke da ruwa dumi,kwana uku kawai za kiyi amfadi dashi zaki sha mamaki(yana sa laushi,tsantsi da shekin fata ke harda wani kamshi na musamman za kiji yana fita a jikin ki)

Sanan gana ganyen magarya da sabulun salo dake su nayi suka hade wuri guda shima na wanka ne.
Wanan hadin lalle da garin ridi ne,ga kuma man zaitun da garin ridi duk shafe jiki za kiyi dasu bayan awa guda ayu wanka da wa’yan can sabbulai.
Don Allah jummai ki kula da amfani dasu kada kisa lalaci da wasa,domin har kullum ina k’ara fada masu sun fi sabulan turawa inganci da gyaran fata.
Duk da nasan suman ki na samun kulawa sosai amma ki guji amfani dana turawa sabida chemicals nasu,ga natural one’s nan
hadin mayukan gyaran gashi,gasu nan na hada maki..man zogale,man kwakwa,man zaitun na hade wuri guda ana shafawa ana kitso dasu.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button