KURUCIYAR JUMMAI Complete Hausa Novel
English teacher ya shigo, duk suka mike..
Gud morning sir.
Yace morng,get sitted.
Wari ne yaji ya cika class din.
Yace what is smelling?
Kowa yayi tsuru tsuru
Koda ya matso kusa da jakar jummai,ya taushe hanci,
Yace ma jummai; why did u pollut the class.
Tace bani bace
Yace speak English
Ta rasa yadda rata yi,domin tana jin abunda yafe gadi,amma bata Iya mayar wa.
Ko da yayi checking bag din, ya fita da take away habba wari kamar mushe..
Tace ka bani abinci na,dama shi kake son ci tunda kaga daga gidan masu kudi ya fito.
Ko kallon ta bai yi ba ya fita dashi wake.
Allawiya na can daga baya sai dariya ta ke yi
Tun daga ranar duk inda taga English master sai tace ma yara ai Barawo ne,daga gidan masu kudi aka bata abinci tazo dashi makaranta ya dauke.
Sai da rana guda ya zanne mata jiki, sanan ta Shafa masa lfy.
Yau koda suka dawo daga schl an dafa ma jummai doya, allawiya kuma shinkafa.
Bayan ta tube uniform, taci abinci..
Umma tace yi sallah ki dauki doyar ki tafi.
Fita tayi kofar gida tace walahi umma ban zuwa tallan doya haka kawai ana zaune lfy…
Umma tace kada ki bari a kama min ke.
Tace sai dai ki kashe ni walahi banyi.
Kama hanya tayi zuwa gidansu allawiya,can ma ta iske Maman allawiya na fama da ita ta dauki tallan.
Magana tayi ma allawiya a kunne,suka taba, ai nan da nan suka sheka a guje..
Mama na ina zaku,ko kallo bata ishe su ba.
Basu tsaya ko ina ba sai bakin gate na siyona church,bukin engagement akeyi na yan church din.
Ga abinci iri, iri sai police band dake tashi.
Serving Kansu suka yi,sai da suka koshi,jummai ta fara dikar rawa,sai daf da magrib aka tashi..
Suna tafia ta ga wata tsohuwa zaune kofar gida, jummai tace hajia mai dawa mayya
Matar tace shegen yaro ,Allah tsine uwaka.
Jummai tace sai dai uwarki tsohuwar mayya.
Ta sheka,allawiya na biye da ita.
A gida kuwa, bayan sun gudu ne Aysha ta dawo daga tallan dafafan masara,umma ke fada mata yadda sukayi.
Tace kema umma da nacii kike,jummai har guda nawa take da zaki na daura mata talla,wadda babu komi cikin kwakwalwarta sai zallar quruciya.
Umma tace idan ba haka na mata ba,bara tabar yawace yawacen banzar nan ba.
Tace dan Allah umma kibar biyewa zugar mutane akan jummai,ni dinan na isa in maki duk tallan da kike so.
Yanzu bara nayi sallah na dauki doyar zuwa tasha baa rasa masu saya ba.
Umma tace Allah maki albarka,ita kuma ya shiryata.
Amin umma
Oh Aysha yanzu shike nan bakya da hutu; da asuba kije islammiya,ki dawo kije boko, idan kin daw kije talla,da dare ma talla,ko yaushe Zaki samu lkacin kan ki?
Muryan baba sukaji yana fadin sai ranar da kika dena daura mata talla.
Yace Saratu ban San me kike so ki zama ba,Iya gwargwado ina quqari a kan Ku,amma bakya gani sai kin bata min tarbiyar yara,su kenan Allah ya raya mana, haba Saratu.
Ba inda Zata talla walahi.
Ya juya fuuuu.
Tace Aysha aje maci gobe, je kiyi sallah isha’i ki tafi islamiyyar dare, tunda ja’irar yarinyar nan taqi dawo wa.
Da su jummai suka dawo gida, baba ya hana umma dukan jummai dole ta kyale ta
Allawiya kam tasha duka wurin yaya nafi’u.
Washe gari su jummai na zaune a class suna hira
“”Da yake sun kusa fara common entrance exams na shiga secondary schl.
Jummai tace ko yaushe zamu gama makaranta har muyi aure gashi ance tashin alqiyama ya kusa.
Wata daga cikinsu,wadda duk ta fisu girma, tace nikam aure zanyi da mun gama exams.
Allawiya tace lalai lauratu ZAKI zama Yar iska kenan.
Tace dallah Ku yarane Baku San komi ba.
Bayan sun koma gida,umma tace anshi sayo kuka gidan Maman bello saura ki tsaya wasa..
Tana tafe tana rera waqa bata Masan takai kofar gidan sale ba,Ji tayi an turata cikin gida an rufe gate.
Tace lfy mallam?
Yace yau zan rama iskancin da kika min ranar, mazza tube rigarki ki cire wando, bani kike kira kwarto ba?
*L££MA*????
[13/01, 19:59] +234 812 140 7930: ????????????????????????
????????????????????????
*QURUCIYAR JUMMAI*
????????????????????????
????????????????????????
*HALIMATU SADIYA MUHAMMAD*
*L££MA*????
*@AM££NCI WRITERS ASSOCIATION*????✍????
*INA masoyyan jummai wanan shafin naku ne,kuyi duk yadda kuke so dashi*
*gaskia nayi farin cikin sosai yadda littafin nan ya samu karbuwa*
*nagode da adu’ar Ku masoya Allah yabar kauna*
*9-10*
Shekewa da wani mahaukcin daria tayi.
Tace Ji yadda kake tadda jijiyoyin kai,kana wani zazare idanu kamar tsohun maye.
Yanzu baka Ji kunya ba?
Kamata Yar kankanuwar yarinya kake cema tube riga tube wandu,kamar wadda ya samu wata uwar mata.
Idan na tube me zaka min?
A haihuwar kaji dai ka haifi iri na.
Kuma ance maka kwarto ko karya nayi?
Almaqashi ta dauka,na rantse da Allah idan baka bude min gate na wuce ba,sai na yanke gindin nan,sanan in Tara maka jama’a,in qala maka sharrin da har ka mutu bara ka mance da Jummai ba.
Sum sum ya dauki key ya bude mata gate.
Tace zaka San kayi da mai yi,MU zuba shege ka fasa dan halak sai yanka,TTA wuce abinta hankali kwance.
Tana fita ta sheqa @360,tace Allah na gode maka da kayi in mai baki, nasan da shegiyar can ne mai shegen tsoro kamar farar kura da yanzu ya gama da ita(Aysha).
Data dawo gida umma ke fada masu ai fati na nan zuwa idan sun samu hutu.
“Fati diyar kaunan umma ce daga kauyen mahuta dake kebbi state zata zo,warin jummai CE.
Murna jummai tayi””domin akwai ta da son baki ko din ta basu labarin yan anguwarsu.
Yanzu Aysha bata zuwa talla,sai gashin masara from 8:00pm to 10:00pm.
Idan ta daw schl tayi aikin gida,da yamma taje islammiya.
Jummai kam sai abunda ya qaru na rashin jin ta,islammiya bata zuwa,idan an turata ta wuce wurin wasa,schl din ma sai taga dama.
“Da yake irin gifted child din nan ne,da an koya mata ABU ko sau guda ne ya shiga kanta kenan, ko bata class akayi data amsa BUK din yan class diny ta duba ya zauna kenan,Dan tun tana primary 3 ta iya reading both English a and Hausa, ga hand writing mai kyau sai dai bata copying note, tana jin turanci amma bata iya Mayar wa, duk da haka ita ke daukan 1st KO 2nd position a class din.
Su allawiya kam in banda tsabar satar amsa babu abinda ta iya, sai karatun Hausa,idan kaga taci exams sit guda suka zauna a jummai.
Shi yasa da fada ya hada ka da jummai sai tace duk baka kyaleta ba bara ta baka amsa ba,ko tana son abinka sai tace ka bata, ta baka amsa.
Anyi lokacin da jummai ke sayar da amsa, idan maths and English exams ne, 50 naira each raka biya ta amsa ta rubuta maka, sauran subject din 20 naira each.idan ta taraa kudinta,ta sayo;awara,taliyar fulawa,dawake,gulisuwa,tuwon madara da sauran su………
Sun fara common entrance exams a sa’a,da yace oral exams ne.
Bayan sun qare ne,suka rabu cikin kewar juna.
Yanzu kam jummai an samu freedom, ba boko,ba islammiya,sai bakar yawo.
Da dare tace su rabe Ku zo muje wurin
Ubale mai kanti dibar madara sukace whhhh muje.
Shago ne babba NA kayan masarufi,mutane ne makil sunata sayan kaya, kasan cewa kayanshi Nada saukin kudi..
Su jummai na isa suka qusa cikin mutane da babban ledar su, su dumbuji madara su zuba, su dunbuji milo su zuba su dumbuji sugar su zuba..
Wani inyamuri ne yazo sayan maganin sauro ya hankalta dash.
Yace hey Hausa pikin na wa for u
U don get promotion be dat
Frm beggin to thieving people property.