KURUCIYAR JUMMAI Complete Hausa Novel
Gana gyaran k’afa….man shanu,man kwakwa,man rid’i da man allayyadi na had’a nan da dare zaki shafa a k’afa in zaki kwanta sai ki daure da leda,da safe ki wanke da ruwan d’umi ki shafa man zaitun da man r’idi.
Gasu nan ki tafi dasu ki juri amfani dasu ko a gidan ki,kina hadawa akai akai….insha Allahu zan kiyaye nan suka ta hira har lokacin sallah suka yi sallah…amina ta kirata akan ta iso…ok kiba umma kayakin ina gidan nafisa.
Amina ta shigo amarya kin sha kamshi..ke besty bana so fa,yasu mami lafiya lau suke suka ci gaba da hira sai karfe biyar na yamma mata uku suka kawo lefe,da dubu talatin sama na kayan lale kasan cewa basu samu daman saya ba…lefe yayi kyau kowa ya gani sai ya yaba,da zasu wuce aka basu kajin su da kayan drinks suna ta godiya…aysha sai santin kaya take yi koda suka k’irga gaba daya da atamfofi,less,shadda da material sun kama arba’in.,ga gudan make up kit babba,kai komi yaji sai san barka…..haka mitane ket shigowa ganin kaya sai santin kaya ake yi,allawiya ma mijinta ya kawo ta can gidan nafisa ta same su….jummai tace ki nga yadda kika zama big madam kuwa? Komi ya k’ara bunk’asa..atau kwanciyar hankali yafi komi dad’i banda matsalar komi yanzu sai d’an abunda ba a rasa ba…haka muke so Allah k’ara rufa asiri amin…sai da kafa ya d’auke suka koma gida sabida mijin nafisa 6pm yake dawo wa daga kasuwa.
Umma tace amina ga kayan ku nan da dubu talatin na kayan lalle….jawo akwatu nan tayi allawiya ta bude suka shiga duba kaya,nafisa sai santin kaya,amina na fadin kudin kaya,duk wanda aka d’aga sai ta fad’i kudin shi,jummai sai murmushi take yi tare da yaba ma mijinta akan namijin k’okarin da yayi wurin hada kayan nan….text mai dad’i ta rangwada mashi,ya kirata naga text na gode da adu’ar ki…kaya sun yi uncle Allah k’ara budi…amin akwai program din da za kiyi ne?dama walima ce kawai ranar yini za myi, sai d’un kuna da zan kai….hakan yayi kyau,kamar nawa kuke da bukata??…ko nawa yayi uncle tace cikin natsuwa…ki turo account number naki na turo maki dubu hamsin yayi ko?…Allah sanya masu albarka..ok ina jiran accnt No_din…ok.
Yana kashe wa ta tura mashi…nan da nan taji alert da yake mobile transfer yayi mata…tayi text na godiya.
Zare jiki umma tayi ta kai ma maman allawiya dubu ashirin cikon kudin dailu dilaliya ….sai dare driver ya zo amina ta wuce gida,alhaji saddat yazo daukan allawiya jummai tayi mata rakiya,bayan sun gaisa ya bata dubu goma gudun mawar shi,sabida yana mugun ganin mutuncin ta yadda ta kula da matar shi har komi ya dai dai ta tsakanin su…godiya tayi mashi suka wuce.
Da dare bayan ta gama shafe shafen ta na gyaran fata ta k’ara bude kayan suna kallo da aysha…umma tace aysha ku kwaso ma baban ku kaya ya gani…bude masa kayan suka yi sosai ya yaba da kayan ..umma tai mashi bayanin dubu talatin na kayan lale,yace ki aje hanunki.
Jummai taba umma 10k da alhaji saddat ya bata.
daga organization nasu “”da’awa commitee” suka had’a ma jummai dubu hamsin amiran su ta kawo mata,gudun nawar su,sosai umma ta k’ara gode ma Allah….da mami ta kai ma dadyn su amina kukan ya taimaka ma jummai basu da,cewa yayi me mami taga za a yi masu wanda zasu yi farin ciki,umma tace gado ko kujeru amma zata tambayi amina me jumman tafi buk’ata….ta samu amina kwance saman bed nata tana charting…sannu mami,yauwa daughter dama maganar jummai ne menene kike ganin sun fi buk’ata a yanzu??
Gaskiya mami gado ko kujeru amma zan tuntube ta naji….ok sai naji daga gare ku zuwa gobe zai bada kudin..mun gode mami.
Waya tayi ma jummai tare da mata bayani tace gaskiya nafi son gado besty sabida ya riga da ya gyara palour…ok gobe ki zo muje kasuwa da mami…ah basai nazo ba besty ki zab’a min colour mai kyau kuma kimin godiya..tau sai da safe.
Su umma ta fada ma baba yace Allahu akbar bani da abin cewa sai fatan Allah ya masu sakaya da gidan aljanah,umma kam kokan dad’i ta fashe dashi.
Da safe daga company da suka sayo gadon gida suka wuto ma jummai dashi,daga nan mami tagga kayan lefe.godiya kam da fatan alheri su mami sun sha shi,umma tace har gida zasu zo godiya ita da baba wurin dady…mami tace haba umman su mun zama d’aya ai haka suka tafi akan sai amina ta zo.
Gaba daya gaba daya suka hada kudin da aka samu,hadda wanda rajinya turo mata dubu d’ari da talatin,da yake anty balki ta dauki nauyin had’a masu walima a kofar gidan su jummai””mami tace lallai tunda balki ta kyauta tawa jummai nasu tazo d’aya””amina tace ai mugun shiri auke yi da jummai.anty khadija ta aiko ma jummai da turaruka na ruwa dana itace…na jiki,na d’aki,dana tsuguno..na ruwa kuma su rum freshner dasu humra…sai tsumin b’aure cike da galan,nonon rak’umi galan guda,tsumin dabinoda zuman mata kafin ta iso…
Bayan jummai ta zab’i kayan da za akai mata dunki
Su aysha da amina suka kai dunku nan material kala uku,less uku,atamfa uku da shadda uku express suke buk’ata da kyar ya amshi dubu ashirin sabida ma telan su amina ne shiya sa ya raga masu…sauran dubu d’ari akayi sayayan kayan kitchen da sauran abubuwan da ba a saya ba…suka dawo da kaya nik’i nik’i,umma tace gaskiya kudin sunyi afki…haka suka yita samun gudun mawa daga ban gare da dama har aka sayi katifa da sauran abubuwan da ba a saya ba…satin buki ya zagayo yan kauye suka fara tururuwan zuwa gidan umma ba masaka tsinke wani muciya,kwarya,kwanun sha,samira,tsintsiya, da sauran tarkace da ake samu moatly a kauye…ga buhun masara da na shinkafa shanshara buhu biyu…su aka kyara ana ci…kayan Gara kuwa gidan su allawiya umma taba maman su allawiya kudi a sayi flour nayin dib’ilan,cincin,alkaki,nakiya da dak’uwa.
Ango ya samu iso wa can gidan shi ya sauka da abokanshi, sabida gidan hajiya ya ciki da mutane…yaso ganinta a ranar amma ina mutane sun yi yawa gidan su jummai kuma umma ta hanata fita wai suyi hakuri haka nan har ta tare……washe gari ma haka yaso ganin matarshi umma na tsare da ita shawara suka yanke da ta saci hanya su hadu gidan shi da dare…sai da ta bare kowa ya kwanta ta susud’a ta fita can k’asan layin su ta hangi motar shi..kwankwa sawa tayi ya bude mata,ta shiga ya ja suka wuce……..
*LEEMA*✍????
*⚜BRILLIANT WRITER’S ASSO..*????
????????????????????????
????????????????????????
*QURUCIYAR JUMMAI*
????????????????????????
????????????????????????
*HALIMATU SADIYA MUHAMMAD*
*LEEMA*✍????
*Dedicated to my sweet BEE*????
*71-72*
Basu tsaya ko ina ba sai london street,gidan su…fita yayi ya bude gate ya dawo tare da shigar da motar…tace uncle basu aliyu na ciki ba(friends nashi da suka zo daga abuja)..matsoraciya suna wurin yawon su.
Da sallama suka shiga,ya kuna light palour ya dau haske…hugging nata yayi baby kin ga palour’n ki???
Wow amazing uncle ka iya za6e fa,am very impress,Allah bar mu tare…amin baby zaunar da ita yayi saman three seater ya aza kanshi saman cinyar ta….baby kin k’ara kyau da haske ga wani k’amshi na musamman na fita daga jikin ki””da yake kayan bacci ke jikinta ta d’auro zani sama…sai shak’ar kamshin jikin ta yake yi,menene sirrin baby?….far tayi da idanu kwanciyar hankali my darling husband…uhm yayi kyau ni da hankali na ba a kwance yake ba gashi nan duk na rame,nayi bak’i har kin fini haske yanzu…lokaci ne.