KURUCIYAR JUMMAI Complete Hausa Novel
Uncle ban san wace kalma zanyi amfani dashi ba wurin nuna godiya ta a gare ka akan hidimomi da kake ta faman yi,Allah k’ara rufa asirri…amin baby idan ban maki ba wa zan mawa?albashina fa na da yawa kusan #200,0000,kinga dole na kyautata maki,fata na ki za’ma kamilar mace,sawwama,k’awwama….insha Allah.
Suna hira yana k’ara shigewa jikinta,tana faman lumshe idanu”abunka da wadda ta tsumu””tana ta shafan suman kanshi a hankali,yana lumshe idanu.
Ya fara romancing nata sosai da sosai,gaskiya koda hakk’in sa zai nema bara ta iya hanashi ba sabida itama a buk’ace take….kasa ta6uka komi tayi sabida jikinta duk ya saki…haka yayi k’idansa yayi rawarsa har ya gaji dan kanshi ya kyale ta.
Bayan komi ya lafa ta duba agogon wayanshi karfe 1:30am…zaro idanu tayi,na shiga uku uncle me zan ce da umma idan na koma gida yanzu dare yayi sosai fa,koma a bud’e na baro masu gida….kada ki damu idan mun isa zan kira aysha ku shiga tare.
Suna isa kofar gidan su,yayi dialing number aysha,bugu biyu ta dauka..kun dawo ne?eh anty babba…ok ta shigo kawai umma na dakin baba ai…ya kali jummai ki shiga ba wata matsala matsora ciya kawai…da hanzari ta fita daga motar ta shige gida tare da turo kofa.
Aysha tace naga fitar ki ai,koda na kira wayar ki tana dak’i..shi yasa ban koma bacci ba nayi ta jiran dawo warki masu miji””ta k’are maganar cikin zolaya…nagode sister,kin san yunwa nake ji?walahi tun wainar da naci kwara biu da safe sai ruwa da nake ta sha…ya za ayi kiji yunwa ana d’ura maki had’e had’e na k’arin ni’ima,ga mijinki yazo kun ci soyayya kun k’oshi…kai sister am serious walahi yunwa nake ji…jona heater ki had’a tea,ga short cake nan ciki wanda mukayi order da abdul za a raba wurin friends day gobe….tea ta had’a mai kauri,tana sha suna hira har sta gama.
Aysha ta kalle ta yanzu sister banda gobe shike nan mun rabu??tunda aka haife ki tare muke kwana,bamu ta6a raba makwanci ba sai da na je sch,da lokacin da kika je kaduna…tausayin yar uwanta taji ya rufe ta,fashe wa da kuka tayi,aysha tace shhhhh ba kuka nace ki min ba ai hira muke yi ko?….haka ne sister sai na tuna da lokacin da nike fama da “QURUCIYA”abubuwan da nayi ta maki,ki yafe ni sister…common kema kin fad’i ai “QURUCIYA”ce,Allah yafe mana baki daya.amin..haka suka yita hira har aka kira sallar asuba,bayan sun iddar da sallah,yan k’auye suka gyara gida aka fara aikace aikace kasan cewa ranar za a je jere.
Zuwa 10:0am amina ta iso da kayanta na kwana…bayan sun gaisa tace anjima idan anty khadija ta iso zasu shigo da mami…wow Allah kawo ta lafiya amin.
Gidan nafisa suka wuce dama can za su zauna kuma a harabar gidan za suyi friends day da karfe 4:30pm…amina taje wurin taila ta amso d’unkunan jummai….ba k’arya sunyi kyau sosai,bayan sun gama ganin kayan ne aka shirya a wani akwati…aysha tace amina shiga gida ki bud’e kayan lefe ki ciro duk abubuwan da za ta b’ukata sabida yau zasu wuce jere da kayan duka…tau akwati guda empty ta ware ta cire ma jummai under wears,mayafi da su sark’a wanda za tayi amfani dasu yau da gobe,daga nan suka wuce wurin saloon aka wanke masu kai aka gyara suka dawo gida…mai lale har gida tazo(zanen fulawa) ta zana ma jummai manyar indian designe da yaji jan lale,haka aka yita ma su lalen…kawayen su har sun fara zuwa…babbban daki guda mai toilet ciki nafisa ta bar masu,allawiya ma ta iso ana ta hira cikin raha.
Zuwa karfe biu lokacin anty khadija ta iso gidan su jummai ita da mami…cikin girmama wa aka tarbe su kayan ciye ciye aka cika masu gaba da shi…bayan sun gaisa da umma da sauran yan uwa aka k’ara yi masu godiya akan hidimar da suka yi…can sai ga anty balki ta iso da moton ta discussion continue ash colour cikin shiga ta alfarma nan kallo ya koma kanta,ko kamshin ta na daban ne…da sallama ta shigo,anty khadija sai hararar ta take yi…cikin girmamawa ta gaida mami ta amsa ba yabo ba falassa,ta gaida anty khadija itama haka…ta koma cikin gida suka gaisa dasu umma…ina amaren suke??suna gidan nafisa,yaro aka sa ya rakata gidan…cikin farin ciki jummai ta tarbe ta da allawiya,amina kam sai d’ari d’ari take da ita…..ita ta ware ma jummai kayan da zata saka yanzu wani hollandis hadad’e ash colour mai manyan furan ni grean da fari”kudin sa yakai 25k)dunkin riga da zani,sai wanda zata saka anjima na friends day swiss less ne lemon grean da orange,dunkin riga da skirt…gasu nan na fitar maki,zamu wurin jere maybe koda zamu dawo kun gama…tau anty naso kina nan fa?ke maryam ai sai yan mata….
Umma ta aika duk inda suke da ajiyar kaya an amso,kowa sai santin kaya yake yi…babban motar kwasan kaya biu raji ya aiko dashi..Nan anty balki tayi ma umma magana akan su uku zasu jere…ita,anty khadija da yar uwar baba na kontagora,basa son tarkacen mutane da yawa.
haka kuwa akayi bayan an gama loda kayan suka wuce london street inda gidan jummai yake…a cikin mota tana ta jan anty khadija da hira’da yake su motar da suka shiga’tace motar kaya yayi gaba zasu bisu baya… Da suka isa sai yaba kyau’n palour’n suke yi,tun anty khadija na share anty balki har ta sake maza suka shigo masu da kayan …gadon da daddy ya saya ma jummai shi aka saka a dakin miji,sabida yafi kyau da tsada,wanda umma ta saya aka saka a dakin jumma,aka gyara kitchen komi yayi tsaf tsaf…bayan sun sa curtain anty balki tace kada a shimfid’a bed sheet sai gobe da yamma dai dai an kusa kawo amarya…haka akayi suka share gida suka kulle gidan..
Su jummai an sha kyau ciki indian material lemon grean da orange kamar ka sace ta…su aysha,allawiya,amina, nafisa da suran k’awayen suyi ankon cikin riga lemon grean polo an rubuta happy marriege life a gaban rigar,baya kuma an rubuta
princess maryam salis
&
Prince muhammad Raji
Wasu wando suka,wqsu tommy skirt abun ya k’ayatar.
An gyara harabar gidan da canopy da kujeru sai table da aka aje abinci kala uku wanda suka girka da drinks kala kala,ga cool music na tashi…jummai na zaune a high table tare da amina sai gift ake aje masu,ana daukar pic kala kala,masu rawa nayi,masu cin abinci na ci,masu hira nayi hara masu daukar pic nayi…sai daf da magrib aka tashi….a hanzar ce ta shiga wanka,koda ta fita amina tace su anty sun koma gida,sun shigo kina wanka sai zuwa gobe idan sun dawo..tace kash nasu magana da anty balki kuwa,amma zan kirata..alwala tayi tare da gabatar da sallah…bayan sallar isha’i aka sa amarya a lalle sai faman kuka take kamar ranta zai fita…bayan komi ya lafa ta kira anty balki akan kada ta manta da dahuwara kaza da zata zo mata dashi gobe…yar dad’i miji ban manta ba..sanan sukayi sallama…pic na friends day ta tura ma mijinta ta wttsapp,suna ta charting har dare ya raba.
tun da asuba tayi wanka da had’in tattaciyar madarar shanu,ta mulke jikinta da turaruka masu kamshin gaske,ta shirrya cikin shadda dinkin half gown da zani…koda 10:am yayi an wuto da abincin walima daga gidan anty balki dama ita ta dauki nauyin walima…su amina na can suna faman saka kayan rabo cikin manyan jakuna na rabo kasan cewa 12:0pm zaa fara walima..kafin kace me dan mutum ya cika gidan su jummai,an gyara filin kofar gidan nan za a yi walima…zuwa 11:0am mutanen ta na area council suka iso mata da maza cike da bus,bayan sun shiga ciki sun gaisa da mutane suka koma waje inda za a yi walima suka zauna..wurin zaman mata dabam,na maza dabam..k’ira’a suka kunna yana tashi cikin suratul nisa’i haba nan da nan shiya ya dauka mutane nata tururuwar zuwa,bama da suka ji mal.alkali wada da mallama khadija mustapha zasu gabatar da wa’azi ba..ango ma ya iso da tawagar shi,cikin shiga ta alfarma kallo sai ya koma kan su ..table nasu dabam….a hanzar ce shirya cikin wata dakakiyar less mai laushi,wanda a k’alla kudin shi yakai 40k,simple dinki akayi na riga da skirt yasha stone work,sai alkebba da aka daura saman kayan…zo kaga kyau abunka da black beauty sai ta haska cikin kayan,sauran friends nasu black abaya kowa yasa yayi rolling red veil abun ya k’ayara..cikin natsuwa suka fito ana take ma jummai baya…mijinta sake baki yayi yana kallon matar shi,ga wani kishi daya taso mashi yadda abokanshi ke yaba kyau’n mattar shi.