KURUCIYAR JUMMAI Complete Hausa Novel
Su anty balki,anty khadija,nafisa,allawiya da sauran mutane ma ba abarsu a baya ba suk sun hallara..yan gidan aogo ma haka su hajia da mutanen ta yan kuta….bayan bude taro da adu’a daga bakin amir na area council,sai karatun al-Qur’ani mai girma daga bakin PRO nasu…mal.alkali wada ya fara wa’azi akan hakki’in mace a kan mijinta,tare da shawar wari zuwa ga ango da maza baki d’aya,bayan ya gama akayi kabbara.
Sai mallama khadija mustapha tayi nata tunatar wa akan hakk’in mace akan mijinta tare da shawarwari zuwa ga amarya da mata duka,akayi kabbara..bayan anyi tambayoyi da adu’oi aka fara rabon abinci cikin take away mai marfi da manyan jakuna mai dauke da kayan buki..zuwa karfe 2:0pm aka tashi bayqn kowa ya ci,ya sha.
Gidan nafisa ta koma,
Wanka ta sake yi ta gabatar da sallah,ta shirya cikin shadda doguwar riga dark blue yasha stone work red ant white har k’asa…su amina ma an sake shiga cikin material less ta rako amarya gida ana ta gaisawa da mutane,suna yi mata fatan alheri har zuwa la’asar tana cikin gida..anty balki ta jata gefe ta bata had’in kaza da zata ci kafin a kai ta gidan miji….haka mutane keta tururuwan zuwa,umma na samun alheri..baba da abinci kala kala aka girka masa shida mutanenshi yan kasuwa…lokacin sallar magrib anty balki tace kiyi wanka gaba daya da hadin nan na sansamin lalle da turaruka sai ki dauraye jikin ki da ruwa mai kyau..bayan ta iddar da sallah ta zauna a natse ta cinye kazar nan tayi brush..wani simple material mai laushi milk colour aka fitar mata dashi riga da skirt ,idan tayi sallar isha’i shi zata saka..su amina anata faman hada kaya sabida daga gidan amarya gida zata wuce.
Bayan sun yi sallar isha’i,aka had’a mata turare na garwashei,na jiki ta rufa da bargo ta turara jikinta,sai na tsuguno ya shiga jikinta da kyau,aka cika mata cup da nonon rak’umi ta shanye duka,ai tsumin 6aure shima tasha….anty balki ta shafe duk wani lungu da sak’o na jikin jummai da humra..oya sa kaya ki ganni lokaci na tafiya,sai jikinta yayi sanyi duk wani matsuwa da tayi na ganin ta koma gidan mijinta taji bata ma son barin gidansu,kuka ta fashe dashi..nafisa tace ba ke bace,ina matsuwa kikayi baki tafi ba?aysha ta fara hawaye ku bari mana,sister shirya baba na jiranki…haka ta saka kaya jiki ba kwari,amina yan son make up har ta jawo kayan zata fara shafa ma jummai…anty balki tace No ai babu make up yanzu haka zata tafi anty make up artiste..akayi dariya duka.
Dakin baba aka kaita,dama umma na ciki da sauran kawun nan jummai na kauye…nasiha sosai akayi mata mai ratsa zuciya sai kuka take hadda sheshek’a..umma ma sai da tayi kwala.
Baba yace ku hanzarta suna jiranku,Allah sa aje a sa’a.amin cewar anty balki.
Motoci ne na kece raini kar guda biyar na daukar mutane zuwa gidan amarya…anty tace su wuce ita zata dauki amarya a motar ta zuwa gidan hajia ta damk’a amanar jummai,sanan ta wuce da ita gidan ta…haka akayi jummai dqi kunshe cikin lafaya sai kuka take sha da kyar aka banbare ta jikin umma,ta koma ta rungume aysha suna kuka da kyar aka rabasu,dan aysha tace bata iya binsu sai dai taje gobe..jummai da amina na bayan motar anty balki,allawiya na gaba,nafisa mijinta bai bata izinin zuwa ba..haka take ta rusar kuka har aka isa kofar gidan hajia.
Da sallama suka shiga,hajia ta mik’e tare da kamo hanun jummai ta zaunar da ita a kusa da inda gwagwanin Raji ke zaune..hajia tace bari kuka d’iyata haf’in Allah ne banq mutum ba fatan mu Allah ya sa maku albarka a zaman ku,ya azurta ku da zuri’a d’ayiba aka amsa da amin..anty balki tace ga amana nan mun kawo maku na d’iyar,yarinya ce don Allah idan tayi ba dai dai ba a tsawata matq.
Suka amsa mun amsa hanu biu biu Allah taya mu rik’o,haka akayi tama amarya nasiha daga nan aka wuce da ita gidan ta..duk abunda ake yi Raji na dakin su na samar taka ya kulle kansa sai rusan kuka yake yi,ya tuna da dan uwanshi”Nura”yana ganin bai kyauta ma nura ba da ya auri jummansa,babynshi.
Koda suka isa gidan jummai mutane sun rage..da kafar dama ta shiga aka aje ta tsakiyar gado tana ta sheshekar kuka..haka suka zare jiki allawiya mijinta ya fara zuwa suka wuce,anty balki ma ta zare jiki ta matsu bata koma wurin mijinta ba daga ita sai amina sukayi saura.
Abokan ango sun yita kiran wayanshi a kashe,hajia akq kira tace baya gida sosai hankalinta ya tashi…ga dare nayi ba a ga ango ba..hajia tace suzo gida tana son ganin su…nan ta tambaye su ina da ina suka san yana zuwa??..kowa yace babu wqni dogon yawo da suka san yana yi…muktar yace a duba dakin shi mana..haka kuwa akayi yaci kuka har yayi bacci.koda aka ta6a jikin shi zafi rau…hajia tace da dukan allamu bai jin dad’i ku bashi yaci gaba da baccin shi,ku kira min jumman a waya.
Amina kam har ta gaji da zama,ba ango ba dalilin shi gashi tana son zuwa gida..can suka ji wayanta na ringing,amina tace Allah sa lafiya hajia ce mai kiran…jummai ta dauka da sallama muryar ta ya dashe…kina jina mijinki bai ji dad’in jiki ba yana kwance yar yayi bacci kina iya kwana ke d’aya ko zaki dawo nan ki kwana dashi???A’a hajia amina na nan zamu kwana tare Allah bashi lfy,ta kashe wayar tare da fashe wa da sabon kuka.
Amina tace what again???..cewa tayi bacci da lafiya wai har yayi bacci,wai dqn wulak’anci nida mijina har hajia na tambaya ta idan zan zo na kwana dashine kl zan iya kwana ni d’aya a k’aton gidan nan,i hate him walahi…haba ki dawo cikin hankalin ki mana,nasan mijin ki yadda yake son ki bazai shirya komi on purpose ba….haka tay ta bata magana har tayi hakuri suka yi bacci.
Can gidan kuma basu runtsa ba kowa na tunanen halin da raji ke ciki”shiko hankali kwance yake baccin sa”…sai lokacin sallar asuba suka tashi wanka sukayi tare da gabatar da sallah,bayan ta idar suka zaga gida lokacin jummai taga yadda iyayenta quka yi namijin k’okari wurin gyara mata gida…suna zaune a palour ne aka yi sallama..faruk ne abokin raji ya shigo da flask da kula daga gidan hajia.
Bayan sun gaisa,amina ta tambqye shi jikin raji?yace yaji sauk’i damq strees ce kuma ya warware…Allah k’ara tsare wa..amin amarya bakya magana ko?murmushi tayi.
Haka suka yi breakfast mutane nata zuwa ganin gidan amarya..hadda dangi na nesa both fanin ango da na amarya…aysha ma tazo lokacin amina rayi masu sallama ta wuce gidan.
Sai da suka ke6e take fada ma aysha abunda ya faru jiya…hakuri ta k’ara bata tare da shawarwari.
A gidan hajiya kwa bayan yayi wanka ya karya,hajia tace ya tashi ya bar mata gida tunda abun ya zama lalaci,baya son zuwa gidan shi haka ya shirya ya koma gida da tawagar abokanshi… tana zaune suna hira da aysha ne quka ji tsayuwar motoci a harabar gidan,aysha ta lek’a,tqshi ki gyara mijinki ne da abokanshi…gyara fuska tayi ta canza shiga cikin hanzari tare da rufa babban gyale….da sallama suka shigo palour tare da zazaunawa aysha ta fito suka gaisa…raji yace tai ma jummai magana ga abokanshi sun zo mata sallama zasu koma abuja…..kamo hanun jummai tayi suka fito tare,ta nemi wuri suka zauna,bayan gaishe gaishe,akayi adu’a tare da fatan alheri,nan suka mata sallama aysha tace itama ta tashi tunda yamma tayi su aje ta gida..nan idanun jummai ya cika da hawaye,haka suka mata sallama.