KURUCIYAR JUMMAI Complete Hausa Novel
Bayan ya rakasu bakin gate ya dawo ciki tan zaune inda ya barta…zama yayi a hanun kujeran ya rungumo ta ya isa haka menene akayi maki?..bakai bane jiya ka k’i zuwa..shh ya isa haka nan gashi na dawo bazan sake barin ki ba i promise…haka yaci gaba da rarashin ta har aka kira sallah ya wuce masallaci..gyara gidan ta k’ara yi ta shiga wanka tare da yin alwala, sallah ta gabatar..rigar baci ta saka mai laushi har guiwa ta daura hijab mai hannu har k’asa…daya fito daga masallaci ya biya k’asan layin su ya sayo gasasun kaji biyu da exotic,ita ya saya mata hollandia yoghurt…da sallama ya shigo tun daga palour kamshi,dakin da yaji karatun Qur’ani na tashi nan ya shiga,zaune take saman salaya rik’e da Qur’ani tana karatu….hamdala ya k’ara yi cikin zuciyar shi,sai da takai aya ta aje…sannu da shigo wa,yauwa baby na barka ke d’aya ko?ba komi ai.
Kamshin turaren nan na gida yamin dad’i sosai..murmushi tayi,dauko plate muci abinci ina palour…plate ta dauko da cups zuwa palour saman center table ta ajiye..yace yi serving namu mana.
Ta cire kazar saman plate tare da yanyankawa….ki cire hijab din mana..cikin jin konya ta cire,yana ta binta da kallo sai kamshi mai sanyi yare da saka nutsuwa ke fita daga jikinta,haka sukayi feeding na juna har suka k’oshi,ta kwashe kayan.
Ruwa ta hada mashi yayi wanka,tare da zira jalabiya ya dawo palour,nan ya sameta zaune shiru…yadai ko kina kewar umma ne?kaman ka shiga zuciyata uncle..uhm sai dai kiyi hakuri haka aure yake,hira yake ta yanta dashi tana kwance a jikin shi har suka fara jin bacci ya kashe komi tare da rufe kofa….dakin shi suka shiga ya yaba kwarai da tsarin d’akin…alwala ya umurce ta da tayi suyi nafila,haka a kayi raka’a biu suka gabatar,ya kwararu adu’oi na neman tsari da zaman lafiya..bayan sun gama ta suka haye yago ya jawota jikin shi tare da kashe wuta,sai da ya bari ta saki jikinta ya fara wasani da ita cikin natsuwa,bayan wani lokaci yayi adu’ar saduwa da iyali..iya dauriya jummai ta yishi amma taji jiki sosai,bayan komi ya lafa yayi ta sa mata albarka tare da adu’ar Allah basu zuri’a d’ayiba….cikin natsuwa da kwanciyar hankali suke rayuwa jummai bata da matsalar komi sai dan abunda ba a rasa ba har mijinta ya koma bakin aikin shi da kuka suka rabo…
*BAYAN WATA UKU*
Result nasu jummai ya fito yayi kyau sosai,har gida taje ta kwada ma su umma da baba sunyi farin ciki…aysha ma sun fara rubuta final exams yan gidan su abdul sun zo maganar sa ranar aure..aka saka wata biyu bayan ta gama exams.
Jummai takai ziyara gidan hajia kus1n sau biyu,taje gidan anty balki da yake shiya guda suke(london street)sai ta zama uwar d’akin jummai…Ranar da ta kai ma mami ziyara murna sosai tayi domin jummai ta zamma babban mace,ta k’ara kyau da waye wa..tace ma amina ai nayi fushi tun da kika zo gidana sau uku baki sake zuwa ba…haba besty ku d’in ne baku da dama keda mijinki,soyaya kamar ku cinye junan ku,kuma mun fara waec shi yasa..haka ta yini sai yamma ta koma gida…
Matsala na farko da suka fara fuskanta raji yabar zuwa weekend yanzu idan tayi magana yace aiki ya masu yawa,tayi masa maganar komawarta schl da zaman banzan da take yi a gida yace bai abince ba,ko islamiya haka suka yi kaca kaca a waya ta kashe wayarta gaba daya…..
*LEEMA*✍????
*⚜BRILLIANT WRITER’S ASSO…*????
????????????????????????
????????????????????????
*QURUCIYAR JUMMAI*
????????????????????????
????????????????????????
*HALIMATU SADIYA MUHAMMAD*
*LEEMA*✍????
*wanan shafi naku ne;QURUCIYAR JUMMAI FAN’S GROUP*
*kun nuna min k’auna,ina jin dad’in adu’oi’n ku a gare ni,Allah bar zumunci ya had’a fuskokin mu a aljannah fir’dausi amin*????????????????????????
*73-74*
????????????????????????????????
A bangaren raji kuma wani lokaci haka kawai yake jin ya tsani jummai musamman ya tuna da abunda ta yi mashi lokacin”QURUCIYAR TA”sai yaji baya ma ko son ganinta shine dalilin shi na rashin zuwa gida har aka share wata guda”’Idan ya kad’ai ta abun na mugun damun shi sabida yasan yana son matarshi,yana mugun kewar ta,sanan bata masa laifin komi ba,tana iya kacin k’ok’arinta wurin kyautata mashi”’idan hajia ta kira shi sai dai yace aiki ne ya masu yawa.
Jummai kuwa ta kashe wayarta gaba d’aya”’ta mik’a lamura nta wurin Allah”babu wanda yasan halin da take ciki”’adu’oi take yi sosai da nafilfili.(idan kika rasa gane kan mijin ki,kyautata alwala kiyi nafila raka’a biyu,idan an idar a karanta aya ta goma a cikin suratul khafi( sau 313)haka kuma
Imam Dairabi yana cewa duk wanda ya lazamci wanan nafila raka’a biyu bayan sallar magrib (ana yinsa ne akan ko wace irin buk’ata na alheri); ko wace raka’a ki karanta fatiha da kulhuwallahu kafa bakwai(7)idan anyi sallama a karanta “ya samadu”kafa(104)insha Allahu bukatar sa zata biya.
Haka zalika idan kana so Allah ya yaye maka wani bak’in ciki da kake ciki ”’sai kayi sallar nafila raka’a biyu”bayan fatiha a ko wace raka’a sai a karanta wanan aya kafa(7)Rabbanakashif anna azaba anna mi’uminun”bayan anyi sallama sai ayi adu’i Allah zai yaye.
Sai wanan wanda ya zame ma jummai kamar farilla.
Idan ana son jawo hankalin mutum duk inda yake ya dawo gida(idan ma 6ata yayi,ko asiri,ko sammu aka masa)sai ayi sallah raka’a biyu ko wacce raka’a fatiha da innahu ala rajihila qadir sau(41)bayan ayi sallama sai a karanta innahu ala rajihi laqadir sau(313)idan an gama ayi adu’a abunda ya sawaka insha Allah za a ga abin mamaki”’haka ta ri’k’a kai kukan ta wurin Allah
Rana tsaka Allah maji ruk’un bawa ya amshi adu’ar ta,tana kwance saman three seater a palonta rik’e da chasbaha a hanunta tana lazumin”tuna wa tayi da abunda ya faru jiya tsakanin ta da aysha”’ har gida aysha tazo ta fada mata hajia ba lafiya jiya suman ta uku a general hospital akayi admitting nata hada k’arin jini,abdulrahim ya bada jini,anyi ta kiran raji bai d’aga ba tazo tambayan jummai ko lafiya??…take ce mata lafiya lau,aiki ne ya masa yawa amma insha Allahu zai zo week d’in nan”ta nemi da jummai ta biyota suje hospital”’tace A’a sai ya iso zasu tare”’nan suka rabu baram baram wai jin dad’in aure ya sa jummai ta canza rayuwar ta kwata kwata,bata waya da kowa,bata zuwa gidan kowa yanzu,har yakai da tazo har gida ta fada mata rashin lafiyar surukar ta,tace bara ta ba sai mijinta ya dawo””tayi ta ba aysha hak’uri,amma ina da fushi ta fita daga gidan jummai”’jummai ta shiga rera kuka na bak’in ciki”’ta ya zata fita bada izinin mijinta ba,menene amfanin wayarta tunda kota kira mijinta mai d’aga wa”’Allah take rok’o ya kawo mata karshen wanan jaraba wa da yayi mata.
Alamar tsayuwar moto taji a compound na gidan”’bata damu da ta duba ba tasan bai wuce amina ko allawiya suke yawan kawo mata ziyara,domin Alhaji saddat ya saya ma allawiya k’aramar mota sabida fita anguwa tunda ba zama yake yi ba”’nocking kofar palour taji anayi”da sauri ta share hawayen da ya zubo mata”shigo a b’ude yake”da sallama ya shigo cikin razana ta mik’e tsaye!!!
Sanye yake da suit ash colour,hanunsa dauke da brefcase””daga ganinsa kasan hankkalinshi kwance sabida babu alamar damuwa a tatare dashi””da gudu ta shek’o tayi hugging nashi cikin matsanaiciyar kuka”’tana dukan k’irjin shi da hanuwan ta duka biyu”why why uncle ka manta alkawarin daka dauka akan bara ka taba juya min baya ba,menene nayi maka da zafi haka da kamin irin wanan hukunci,na wahala sosai a dalilin rashinka 2months is not a joke uncle,kwata kwata fa wata na biyar kenan a gidan ka,shekara guda kuma da daurin auren mu,ashe haka aure yake,duk yadda kuke son juna kake kyautata ma mijinka sai shaid’an yasan ta inda zai shiga tsakanin ku yaga ya wargaza farin ciki da jin dad’in ku,yaga ya lalata aure,walahi ba zai tab’a yin gala6a akan mu ba”’tsaye yayi kaman gunki yana sauraren ta domin kam lalai sai shaidan”’a iya saninshi babu abunda tayi mashi na rashin kyautata wa”’ajiyar zuciya yayi yana mai zub da hawaye baby ki yafemin ban kyauta maki ba,nasha yi maki alkawari bana cika wa but insha Allah komi ya koma normal daga yau bazan sake barin ki ba tare zamu koma abuja ””kinga na dauko annual leave na wata uku”’aaba uncle ni baka min laifin komi ba jarabta ce ta ubangiji kuma nayi tawakali a matsayina na musulma,ka dena kuka mana.