HAUSA NOVELKURUCIYAR JUMMAI Complete Hausa Novel

KURUCIYAR JUMMAI Complete Hausa Novel

Ya k’ara rungume ta ”’tun a palour ya fara hot romance da ita”cikin duba ra ta jashi zuwa room nashi”sun kai awa guda ana abu d’aya”tabbas sunyi missing junan su” sun samu natsuwa alhamdulilah”’wanka sukayi ta dafa masu indomie da kwai suka ci”’sai data tabbata ya samu natsuwa take fada mashi hajia na hospital”subhanallah tun yaushe??aysha tace tun jiya hadda k’arin jini aka mata”’tashi ki shirya muje”’nagode sosai da kika tsare min kanki a inda na aje ki,Allah maki albarka amin.

A hanzarce suka isa general hospital minna,aminity ward room 6,tun a waje suka fara haduwa da yan uwa maza na can kuta ana ta gagaisawa,dak’in cike da yan uwa maza da mata,bayan an gagaisa ne yake tambaya wane likita ke duba ta?nurse ta nuna mashi office na likitan”bayan sun gaisa,yace shine yaron mara lafiyar dake aminity word room 6,yau yazo daga wurin aiki”’file nata likita ya dauko tare da mik’a ma raji,ya gama dudubawa bai gane komi ba””yace i need more clearification doctor”’blood cancer ke damun mahaifiyar ka,a bincikin da muka yi ne muka gano ya dad’e a jikinta sosai”what blood cancer hajia how,when???
Be a man” kada ka tadda hankalin ka jiya brother baka abdulrahim ya bada jini anyi mata k’arin jin,sanan mun daurata kan magunguna lasu inganci insha Allahu zai lafa”yanzu doctor u mean bazai warke gaba dayq ba sai lafawa??wanene ni da zan yanke hukunci,Allah kadai yasan gaibu”’amma gaskiya mostly masu fama da irin ciwon basu cika warke wa ba sabida ya riga da ya lalata jini dake cikin cikin su,gradually zai lalata duk wani organ na jikinsu har akai ga rasa mutum”’mostly abunda ake masu suji saukin abun for some years shine a fita dasu k’asashen waje a kwashe jinin da ke jikin su a zuwa wani jinin””amma yanzu doctor kana ganin ita idan aka mata zata warke??i ca’nt predict sai abunda Allah yayi”mutuwa da rayuwa duk tana hanun Allah..ina so ayi making arragement for her zamu fitar da ita waje””doctor ya kali raji up and down zaka iya kashe wayan nan kud’ade kuwa?…me ka dauke ni talaka ko me?bara kaji koda duk abunda na malaka zai k’are sai na nema mata magani”’it ok since u said so,i will make an enquiry,what ever is their i will let u know…

Ko da ya fito ya samu abdulrahim zaune a saman wani beanch yana latse latsen waya”gaisawa suka yi,ya mashi godiya sosai akan taimakon da yayi masu””haba an zama daya ai”nan raji ke fada mashi abunda doctor yace”’hakan ma yayi dai dai,idan ana bukatan wani taimako dai feel free to ask me”insha Allah zamu yi iya kacin kokarin bada duk wata gudun mawa muga an samu ci gaba ta fanin lafiyar ta””nan suka zauna suka tattau nawa sabida tun da aka mata alluran bacci da safe har yanzu bata farfad’o ba..

Cikin d’aki kuma jummai ce raku6e a gefe ta rafka uban tagumi tare da zuba ma hajia idanu”sallaman aysha suka gani tana dauke da basket na abinci,umma da maman allawiya na bayanta”ko kallon jummai bata yiba a dole fushi take da jummai,bayan an gagaisa ne””yan uwan raji keta ma umma godiya akan yadda suka tsaya tsayin daka suna bada gudun mawa yadda ya kamata””tace babu komi ai an zama daya”sai da suka ke6e da jummai umma ke fada mata tunda kwana biyu taki zuwa gida,ga wayanta bai zuwa ana ta faman shirye shiryen auren aysha,karshen wata za a kawo lefe da sadaki”murna sosai tayi,tace insha Allah zata shigo kafin lokacin”ta kali aysha sister don Allah ki yi hakuri idan nayi maki ba dai dai ba,bani da wata yar uwa duk duniya sama bake,kefa kika ce nayi biyaya ga mijina,na zauna inda ya ajeni komin runtsi kuma na 6oye sirrin mijina?ya kamata ki fahimce duk abunda nake yi ya zama min dole ne ko dun kare mutuncin aure na”ta share ma jummai hawaye na fahimce ki,fatan komi ya dai dai ta tsakanin ki da mijin ki?gyada kai tayi”masha Allah,Allah kara rufa asirri ya baku zama lafiya mai daurewa amin”hira suka ci gaba dayi take ba jummai labari ai kud’aden da abdul kan bata 10k duk karshen wata na trasport da kuna wayanda yake bata na kashe wa ta shiga adashe dasu yanzu ta kwashi dubu dari kuma ya bata dubu hamsin ta k’ara idan akwai abunda take son saya har sun je kasuwa da friend nata faiza sun yi sayayan kayan kitchen da wasu tar kace”’tace gaskiya kinyi dubara sister an fara biyan kune?…tau kinsan anyi posting namu ne kafin result ya fito idan yayi kyau za a dauke ka aiki parmanent,amma su na bamu wani abu duk karshen wata.Allah taimaka.

Har suka wuce hajiya bata farfado ba,su jummai na nan dai sallah ke tadasu ita da raji domin mutane sun rage sosai,allawiya ma tazo har da abinci ta kawo”sai da yamma ta farfado,doctor ya kira ya duduba ta,yace taji dama sosai ana iya bata abinci ko wane iri taci,nan jummai ta zuba mata abincin da allawiya ta kawo,kuma alhamdulilah taci sosai”haka suka yita hira da ita sai da dare ya raba tace su wuce gida domin akwai mai kwana da ita””a hanya ya tsaya ya masu take away”domin ya lura da jummai taki cin komi a hospital sai coke data sha”suna iya gida tare suka yi wanka”ta zuba mashi abincin da yayo take away”ke bara kici bane??no coke kawai zansha bana jin yunwa”na you sabi”ya cika cikin shi,ta kwace kayan basu tsaya dogon hira ba suka shige domin a gajiye suke”jummai kam ta murzu hanun mijinta cikin daren nan,ta jigata sosai amma yaki sarara mata gashi maranta sai mugun ciwo yake mata”haka ta hakura har ya samu natsuwa.
Da safe a dadafe ta gyara gidan ta hada break fast mai yawa hada na hospital”babu yadda bai yi da ita ba taci abinci” tace ai taci kafin ya tashi daga bacci,haka ya hakura ya cika cikin sa da abincin matar sa mai dad’i
wayanta ta kuna ta kira anty balki ta fada mata hajiya na hospital”’ta kira amina ma ta fada mata”tace insha Allah zan shigo yau sabida jiya mukayi sendforth party namu”’jummai tace iye yan mata su graduate manya,ina ruwan amindago an gama secondary schl”dariya abun yaba amina sosai,mami tace keda wa?jummai ce ke tsokana ta ””mami ta amshi wayan suka gaisa da jummai,tayi mata ya mai jiki?.tace taji dama sosai”nan tace sai sun zo”haka suka shirya zuwa hospital”hajia taji sauki garau sai d’an abunda ba’a rasa ba”yan dubi ya sai zuwa suke yi ciki hadda baban su jummai”anty balki hadda abinci ta kawo”su mami ma kayan fruits suka kawo.
yanzu kullum a hospital suke yini sai dare yayi su koma gida”Raji na lak’e da jummai baya raga mata kullum sai ya amshi hakk’in sa na aure”tun tana hakuri har abun ya fara damunta,domin ta gane shi mutum ne mabuk’aci sosai,gashi yanzu bata cin abincu kwata kwata ta tsani abinci sai coke take yini sha”ga ciwon mara dake matsa mata kullum idan suna kwanciyar aure”haka dai ta barshi akan period din ta ke son zuwa,amma kuma abun yak’i zuwa har lokaci ya wuce sai ciwon mara ta barshi akan maybe canji yanayi ne..

Ranar kawo lefe jummai ta kira amina gidan ta suka soya kaji goma da katon na drinks biyar suka wuto gida dasu” allawiya ta zo itama da fried rice kula guda sabida daga kontagora za a wuto da lefen”baby rahma tayi wayau sosai”gida ya cika da yan uwa da abokan arziki”jummai ta cire kaji biyar da katon na fanta taba umma nasu ne.
Sai zuwa karfe uku suka iso cikin sharon”mata uku,maza biyu”’sallah suka fara yi aka gabatar masu da fried rice na allawiya”sun ci sosai tare da yabawa da karamci irin na iyayen aysha”set guda na akwatuna da kayan lalle”maza kuma suka gana da su baba aka bada sadaki naira dubu hamsin.
Barakallah kaya sun dama na jummai a kyau da tsada sun shanye””sabida bank manager ne”ga family nasu akwai y’ayan bank””’sai da suka yi sallar la’asar suka juya da kajin su da drinks sai 10k da jummai ta basu.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button