HAUSA NOVELKURUCIYAR JUMMAI Complete Hausa Novel

KURUCIYAR JUMMAI Complete Hausa Novel

Sai da mutane suka rage suka k’ara duba kaya,nan jummai ke tambatan ta kontagora zata zauna ko nan?..tace kontagora yayi gida,amma ya kama masu gidan haya a nan two bedroom flat”tunda nan yake aiki”sosai jummai taji ma yar uawarta dad’i sai dare raji yazo d’auka rta daga hospital”’bayan sun gaisa dasu baba tayi masu sallama suka wuce gida””hada fargaba take dare yai yace zai amshi hakk’in sa”’yau kuka ta saka masa akan ita ya saurara mata haka wanan ta gaji kullum bata jin dad’in komi sai ciwon mara da take k’are wa dashi amma ya matsa mata da abu guda””yace ai shi yana jin dadi kuma idan lafiya ne bata da shi ai sai tayi magana suje hospital ba ”’ta aza masa kuka ba”idan kuma ta gaji dashi ne yak’ara aure”’dama ya fada mata k’arin auren shi na hanunta”haka dai ya lala6ata har ya samu natsuwa ya barta da ciwon mara.

yau suna hospital wurin hajia tana zaune suna hira,wata nurse t shigo dama sun saba da jummai,suna mutunci sosai”’ta canza harshe da turanci tana tambayan nurse din meke kawo ma mace yawan ciwon mara idan mijinta na saduwa da ita?tambayan farko da nurse tay mata shine ko tana da shigan ciki ne?”’tace gaskiya bata sani ba,amma bata yi period nata ba last month gashi har wani wata ya k’are,kuma bata cin abinci””tace ta biyo ta lab suka tafi ta amshi fitsarin jummai tayi pregnancy test”positive ya nuna”tace ma jummai ai k’aramin ciki ke gareta”’murna sosai tayi ta dawo daki””abunda bata sani ba hajia najin turanci sabida mijinta tsohon soja ne har lagos sun zauna”’sai da raji yazo daukar jummai hajia ta juya harshe da gwaranci take fada ma raji ya binciki matar shi kaman tana da shigan ciki”yace tau”da suka dawo gida ranar bai sex da ita ba dad’i sosai taji,kuma yayi noticing nata”da safe daya matsa mata taci abinci hadda kuka ta saka masa”ita lalai coke zata sha”ya hanata sha yaga iya gudun ruwanta amma stil tak’i cin komi.
Da suka zo hospital ne doctor ya kira shi akan ya gama binciken da zai yi”a india ake aikin kuma million goma ne kudin aiki sanan doctor’n dake aikin duk april yake yi”Raji yace zamu shirya ayi mana booking before then” sallama ya rubuta ta koma gida taci gaba da shan mgungunan ta tunda yanzu febury muke before april ta sake dawo wa check up kafin su wuce…nan ya mashi complain akan jummai…daria doctor yayi tare da cewa ya shigo d ita ayi scarning”koda tazo akayi cikinta wata biyu sai dai ba a cikin mahaifa yake ba shi yasa take fada da ciwon mara lokacin da yake saduwa da ita”sabida haka dole ya daga mata kafa har cikin yakai wata biyar,kuma duk wani aiki gida for now ta bar yi,idan ba haka ba ana iya rasa baby’n” an rubuta mata magunguna da zasu taimaka mata sai shawarwari daya basu”godia suka mashi”sosai raji yayi farin cikin samun cikin jummai”ita nata farin cikin da biyu ne zata huta da azabar da take sha idan yana saduwa da ita.
Da ya fada ma hajia murna sosai tayi hadda hawaye wai nura ya mutu,ga sabon nura an sama mata”haka suka tatara kaya zuwa gida yaso kwarai hajia ta koma gidan su da zama,tak’i amincewa’sabida k’anwarta na nan wadda mijinta ya mutu”ta dawo wurin hajia ita ke jin yarta”haka ya hakura ya kaita gida”cikin di’yan kau’nar hajia aka dauko ma jummai guda wada zasu zauna tare tana ta yata aikace aikacen gida”raji kam duk bukatan shi ya tashi haka zai rarashi jummai har ta amince ya biya bukatan shi”sabida gaskiya yanzu alhamdulilah ba kamar da ba ta br jin ciwon maran”amma kam babu abunda ya canza game da rashin cin abincin ta har yanzu coke take sha sosai….

Amina result na waec ya fito”alhamdulilah anyi nasara”yanzu shirye shiryen rubuta jamb take yi.

Shirye shiryen buki ya kankama gidan su jummai,da raji ya labarta masu tana da ciki sosai baba yayi murna,haka umma da ma duk yan uwa baki daya,anty balki sai tsokana rta take ”wai daga shiga sai daukar ciki”da anty khadija taji labari sosai ta taya jummai murna”ta basu hakuri akan bara ta samu zuwa auren aysha ba sabida cikin ta ya shiga watan haihuwa.
Sosai raji ya bude bakin aljihun shi a kan bukin aysha”’domin yana matuk’ar tausaya ma su baba halin rashi da suke ciki kusan rabin kayan d’aki shi yayi ”’haka ya faranta ran jummai sosai”ta k’ara gode ma Allah da ya bata gurzon miji mai zuciyar yi,duk da rufin asirrin Allah ne kawai,amma raji akwai zuciyar yi.
Satin buki ya zagawo yanzu gida take yini sai dare yake zuwa daukan ta.
Ango ma ba a barshi a vaya ba sosai ya gyara gidan daya gina a kontagora da abubuwan more rayuwa”yace duk kayan da aka mata a saka a nan minna inda ya kama haya”kudi sosai ya sakar ma aysha domin fitar da iyayenta kunya sabida yasan halin yan wanshi akwai karyar arziki.
Haka kuwa akayi a bosso lowcot gidan yake madaidaici mai d’akuna biyu da palour,su nafisa,allawiya da jummai suka gyara gidan tsaf.

Amarya ansha gyara jiki har ta gaji”dama nafisa mutumiyar ta ne”su anty balki ma ba’a barsu a baya ba ”sun bata tasu gudun mawar”’yayin da k’awayen aysha watau faiza da sadiya suka tsaya tsayin daka domin ganin komi ya tafi yadda suka tsara”ranar alhamis aka yi kunshi da safe,da yamma kuma kamu duk a gidan nafisa.

Juma’a akayi walima na mata zalla a ”Lebo kutigi conference center”yan uwan ango sunyi ranmwar gani,yayin da jummai ta wadata wurin walima da kalolin girke girken ta mai dad’i da kayan shaye shaye,sai savonier’s da sukayi rabo.

Ranar saturday da karfe goma sha biyu n rana dumbin jama’a suka shaida daurin auren
*Aysha salis*
&
*Abdulrahim mamman king*
Daurin auren da ya samu hallartan manyan yan kasuwa,manyan yan siyasa,manyan banker’s da sauran mutane”bakin ango bai rufuwa sai fatan alheri ake mashi”sai da komi ya lafa ne aka bude masa dakin baba ya shiga da abokanshi,suka ci abinci”sanan amarya ta shigo da abokanta biyu aka gagaisa tare da fatan alheri”suka basu wuri su zanta.
Hugging nata yayi sosai yana zub da hawaye”’aysha nafi kowa farin ciki,nafi kowa sa’an mace ta gari,ina kara gode ma Allah daya bani ke a matsayin uwar ya’ya na”haba dear kada ka sani kuka nima nafika farin ciki da sa’a fatana Allah bar mu tare amin”’ki fada ma su faiza sai ku shirya idan ayi sallah zamu wuce kontagora”ta amsa sanan ya fita.
Haka amarya tayi wanka,ta shirya cikin atamfa super wax blue”abunka da farar mace ta haska sosai duk da kana hanko tashin hankali da jimamin rabuwa da iyaye akwayar idanunta haka take dauri ya”wurin baba aka kaita tasha nasiha sosai mai ratsa jiki”haka ma umma taja mata kunne sosai duk da sun san halin aysha bata da matsala kuma akwai hakuri da kau da kai”’da kyar aka rabata da jummai suna faman kuka”raji ya jaye matarshi zuwa gida sabida halin da take ciki kada ta ja ma baby’n su matsala.
Ba’a kwashi mutane da yawa ba,daga amarya da abokanta biyu,sai gwagwanin amarya uku suka kama hanyar kontagora.
Umma sosai taji kewar diyan nata gidan yayi mata fadi”ta rok’i kaunan baba data bar mata d’yarta rashida ta zauna wurin su” gwamma ta amince sabida taga diyan umma duk masu hali suka aura”haka aka watse aka bar umma da rashida yar shekara goma sha biyu.

Amarya sun isa kontagora lafiya”a mutunce yan uwan ango suka amshi su”bayan an damka amanarta wurin su, aka wuce da ita gidan ta dake federal lowcost”fadin tsaruwan gidan 6ata baki ne”’amarya sai kuka take,haka suka lala6ata ta tsagaita kukan”akayi sallah tare da cin abinci”ango ya bugu mata waya akan su shirya zuwa takwas na dare akwai dinner da antie’s nashi suka shirya masu”haka akayi anko amarya da ango sukayi na gizna shadda milk colour sunsha kyau har sun gaji”’a safara hotel kontagora akayi dinner,an ci,an sha,an zuba kudi sosai ”sai lokacin ta k’ara tabbatar lalai abdul d’an dangi ne ”sai sha biyun dare aka watse.
Washe gari yan uwa ango nata zuwa ganin amarya kuma sun yaba da za6in abdul”sai da rana bayan sun ci abinci,sunyi sallah mota tazo daukan yan gidan amarya zuwa minna”da kuka ta rabu da friends nata”sister’s na ango nata bata hakuri su suka zauna da ita har yamma”suka k’ara gyara gidan suka wuce.
Da dare ango ya shigo da abokanshi”bayn adu’oi da fatan alheri suka wuce”kaji ya shigo dasu da hollandia yughourt,bayan sun ci,sun sha,yayi wanka itama ya umurce ta da tayi wanka tare da dauro alwala”’nafila suka gabatar tare da dau’oi’n neman zama lafiya”’cikin natsuwa ango ya amshi budurcin matarsa,sai sam barka dasa Albarka.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button