KURUCIYAR JUMMAI Complete Hausa Novel
Da safe zaza6i ya rufeta,sai daya taimaka mata tayi wanka,tana faman jin kunyan shi..yace ai gara kibar jin kunyata don mun zama hanta da jini,cikin tsadaden leshi ta shirya,bata yi make up ba amma tayi kyau..yan uwa nata zuwa sallamar amarya..haka rayuwa mai dumbin farin ciki ya kasance gidan aysha da abdul,kafin su dawo minna ta saba sosai da sister’s na abdul m,sabida akwai ta da hakuri..wata guda a kontagora suka dawo minna,har gida ya kawota da dare suka gaishe dasu umma…murna sosai baba yayi daya gansu cikin kwanciyar hankali.
Haka ma jummai taje gidan aysha ta yini mata,domin yanzo tabar laulayi tana cin abinci sosai har cikin ya fara tasawa…nantake fada mata ai anty khadija ta k’ara haihuwar baby boy har anyi suna,raji ya hanata zuwa kaduna..sai yamma ta dawo gida
Result na national exams nasu aysha ya fito,kuma tayi passing,yanzu ta zama parmanent worke’r a general hospital minna.
Amina an rubuta jamb,kuma an samu score mai yau.. mami tace daddy’n ki yace ki shirya nxt month zaki wuce schl lagos(university na lagos)…amma mami ba hostel zan zauna ba ko?…eh tunda wan baban ki can yake sai ki zauna wurin su ma,haka daddy’n ku yace… Godia nike mami Allah k’ara girma…amin kada ki damu fatan mu ki samu ingantaciyar ilimi.
Rum nata ta shiga..tayi dialing wani number da naga an rubuta my destiny…hello baby love yadai..lafia lau my destiny ya aiki?..gamu nan muna fama..kasan me daddy yace zan na dawo lagos da karatu…wow gaskiya am very happy for both of us,akwai soyaya kenan…tana kashewa ta kira jummai guest what??..ina jinki..dady ya amince naje karatu lagos gidan su masoyina farhan…gaskiya na tayaki murna Allah taimaka.
Yanzu cikin jummai ya shiga wata bakwai”tuni ta fara zuwa awo”mijinta na bata kulawa na musamman suna zaman lafiya iya gwargwado..ta 6angaren hajia kuma tana samun kulawa na mussaman ga shirye shiryen fita da ita india ya kankama…wurin aiki Raji ya koma yayi report sabida tare dashi za’a india.
Ranar ba bara su ta6a mantawa dashi ba a kundin rayuwar su,ranar da aka wayi gari babu hajia rai yayi halin sa..jummai suma tayi,nan da nan raji ya rud’e ya sungumeta sai hospital,cikin gagawa aka amshe ta sai emergency… kasa ta6uka komi yayi,ga gida ana jiranshi ayi jana’iza..aysha ya kira a waya tare da fata mata halin da ake ciki..cikin gagawa ta iso tare da abdul..shawara ta bayar kada a sanar dasu umma ,gudun tashin hankalin su,ita zata zauna da ita,su tafi wurin jana’iza…haka akayi kuwa suka kama hanyar gidan hajia….koda suka isa an shiryata nan raji ya gurfana a gaban gawan hajia domin yin adu’a..amma ko uffan bai iya furtawa ba,idanun shi sun bushe,ya kasa ta6uka komi ba haka aka sallaci gawan hajia aka kaita gidan ta na gaskia.(Allahu akbar ,dama rai ba a bakin komi yake ba,Allah sa mu cika da kyau da imani.amin)
su umma ke amsan gaisuwa a gidan hajia…aysha na hospital tare da jummai,sabida doctor yace a sanadiyar faduwar da tayi saman cikin lokacin da taji rasuwar hajia,dole a bata agaji na gagawa sabida abunda ke cikinta ya bugu..drip aka saka mata,kafin ta farfado ayi scarning a gani….can gidan rasuwa mutane nata tururuwan zuwa gaisuwar rasuwa ciki hadda su mami,nafisa,anty balki,allawiya,amina da sauran mutanen arziki,ga dangi na nesa dana kusa duk sun iso sabida da asuba ta rasu…..daga gidan gaisuwa hospital suke ta zuwa duba jummai amma har lokacin bata farka ba.
Raji na zaune cikin mutane a kofar gida tare da abdul,ga friends nashi duk sun hallara,amma idan ka ganshi bai cewa k’ala yayi zugum…sai ban baki ake masa,lalai kuka rahama ce ga bawa,raji kam ko kukan Allah bai bashi daman yiba,domin baida kamar hajia suk duniya,ta bashi ingantaciyar ilimi,ta rik’e shi kamar ita ta haife shi,kuma ya’shi ce,sai mutuwar nura ya dawo mashi sabo fil.
A hospital yan uwa sun cika d’aki cirko cirko,aysha na fad’a masu anyi scarning ance in har ba a cire abunda ke cikin jummai ba ana daf da rasa baby’n…anty balki tace yanzu kam halin da raji ke ciki idan ya rasa baby’n nan abun zai masa yawa,gara ayi aiki..aysha ta kira abdul ta fada mashi..kama hanun raji yayi ya saka shi front sit yayi locking,jan motar yayi sai harabar hospital..raji dai zugum yayi kamar ta6a6e har suka shiga office na likita…bayani ya k’ara masu,ya nemi da mijinta ya saka hannu doming ayi booking nata for C/S..bayani abdul yayi mashi raji ne miji amma ga matsalar da yake ciki,abdul yasa hannu…dakin suka shiga,raji na ganinta ya rungume ta tare fashe da kuka mai tsuma zuciya..abdul yace kada a rarashe shi gara yayi ko zai ji sauk’i a ranshi..fita sukayi suka basu wuri…haka yayi mai isar’shi..baby ki tashi,hajia ta tafi ta barmu,bani da kowa sai ke,kada ki barni baby,ki taimaka min..haka yayi ta sambatu har ya gaji dan kanshi,yace su aysha suje gida shi zai kwana da ita”babu yadda basu yi dashi ba akan ya koma wurin amsan gaisuwa”’yace a’a..haka suka wuce.
sai cikin dare ta farka,dama doctor yace kada a bata abinci ”ceiling take kallo,hawaye ya zuba a idanunta,rarashinta ya shiga yi da ban baki,tayi shiru amma bata ce komi ba,haka suka kwana rungume da juna.
da safe aysha tayi abinci kula biyu, sai da suka biya gidan jummai suka dauki duk abunda za a bukata a hospital…. kula guda gidan rasuwa ta aje,cikin hanzari suka biya gida ta gaya ma baba halin da jummai ke ciki..yace ta fada ma umman su Allah ba jummai lafiya shi zai wuce wurin amsan gaisuwa…tare da umma suka wuce hospital jummai na zaune saman bed tayi tagumi,raji ma haka,bayan gaishe gaishe aysha ta hada masu tea cup biyu,umma tace daure ka amsa ko k’adan ne kasha ”haka ya amsa yana sepping kamar mai shan magani..haka aka matsa ma jummai tasha kadan,umma tace ya kamata raji ya koma wurin amsan gaisuwa tunda sun iso,badan yaso ba ya wuce gidan hajia…zuwa 10am doctor ya iso”nurses ya umurta dasu shirya jummai su shigo da ita theater room ….Bayan minti talatin aka ce su umma su bada kaya”aysha ta bayar”yara biyu aka fito dasu(baby girl da baby boy)yan bakwai ni(7month)yaran kyawawa,amma k’ana na ne sosai…sai da aka k’ara awa guda, aka fito da ita tana sharar baccin ta…nan aysha tayi ta kiran yan uwa tana fada masu labari mai dad’i before u know hospital ya cika da yan uwa,kowa sai fad’i yake nura da hajia sun tafi kuma sun dawo….haka anty balki ta kwashe su zuwa wqni gidan friend nata kusa da hospital,tai masu wanka fes ta shirya su..sai da yamma jummai ta farka”hadda kukan ta wai ciwo ya dame ta,ga yunwa da k’ishin ruwa”umma tace don ma baki d’an d’a na azabar da mata keji ba wurin nak’uda da haihuwa..suna cikin haka ne Raji ya shigo da abokan shi,haka suka ta daukan babies domin sunyi kama da baban su sak banban cin yaran launin fata”macen fara,namijin b’aki”
Raji na zub da hawaye yayi masu huduba macen aisha’sunan hajia’namijin nura..yace daga yau yarana sunci sunan aysha da nura,ban yadda a 6oye sunansu ba..kabara akayi gaba da’ya,abokanshi suka mashi sallama,nan ya zauna har dare yana rarasin matar shi’umma da taga haka ta wuce gida.
Bayan sati guda aka sallami jummai,gidan umma ta koma”gidan hajia kuma anyi ad’uar kwana bakwai” mutune sun watse’saura na gida,koda aka tambayi raji menene yake so cikin kayan hajia?.ya nuna babu abunda yake bukata’haka yan uwa suka rabe kayan hajia..gidan da take ciki dama gadon nura ne kuma ya rasu bai bar kowa ba..shawara aka yanke da asa gidan a kasuwa a gina masu masallaci ladan yakai kabarin su.