KURUCIYAR JUMMAI Complete Hausa Novel
Har yanzu raji bai koma dai dai ba,ya zama shiru shiru,kullum cikin tunane…an kai kayan barka gidan su jummai da manyan raguna biyu’su anty balki ne yan bakin gado’uwar dakin mai jego’..amina ma nan take yini kafin ta fara schl..Anty khadija ma tazo da baby’n ta ahmad..jummai taji karfin jikinta sosai sabida tana samun kulawa na musamman ‘sati biu da haihuwa aka yanka ma yara ragon su,ba wani taro akayi ba sabida jimamin mutuwar hajia,amma sun samu kyaututuka.
Raji ya koma bakin aikin sa tare da cuku cukun nema masu gida a abuja’a ”cewar sa bazai iya zama a minna ba hajia ‘.
Amina ma ta xuce schl,soyaya sai abunda yayi gaba tsakaninta da farhan,hadda alkawarin aure dadyn farhan yayi masu idan ta maida hankali a karatu.
Bayan wata biyu twins sunyi kwari,raji yazo ya wuce dasu abuja da mai rainon su’jummai ansha gyara sosai’..
Aysha
ma na fama da laulayin ciki,ga aikinsu babu hutu,abdul yaso ta aje aiki ”ta nuna rashin amincewarta domin adashe take yi da zumar biya ma iyayenta kudin kujeran makka su sauke farali.
*BAYAN SHEKARU UKU*
abubuwa da dama sun faru ciki hadda auren amina da farhan bayan ta gama schl”suna zaune lagos.
Aysha ta haifi baby girl taci sunan umma.
aysha ta biya ma umma da baba kudin kujeran makka,abdul ya biya mata itama tare suka tafi suka sauke farali.
koda suka dawo raji yasa an gyara ma su baba gidan ya koma ”2bedroom flat”da toilet ciki.
Jummai ta k’ara haihuwar baby girl mai sunan ta maryam’raji yace a kirata da jummai’amma bai fata tayi irin QURUCIYAR momy’n ta.
Ya gina ma jummai makarantar islamiyya babba a cikin minna kusa da masallacin su hajia…Tare suka je saudiya aikin umra,ga mota daya siya ma jummai tana kai yara schl.
Allawiya ma ta k’ara haihuwa har yara biyu duka mata.
su jummai basu cika zuwa minna yanzu sai lokacin bukin sallah,ko wani abu ya taso ”a gidan su suke sauka..
Ranar sallar laya,umma na gani tayi shar cikin leshi red colour mai daukar ido tana faman fara’a,ga hauren makka ya zauna das a bakinta..palon su yasha tile da manyan ledar set,ga plasma manne a bango..rashida(diyar da umma ke rik’o)tana kwashe abinci a kuloli..sallama suka ji,yara ne kyawawa su hudu suka shigo da gudu’ka’ka oyoyo’ta rungume su,daga ina haka?su jummai da aysha suka shigo cikin shiga ta alfarma sai kamshi ke tashi,sunyi shar dasu kamar wasu matan governor’s’ko wace na fara’a ga hauren makka na zinari na haskawa cikin bakin su.
umma tace daga ina haka yau sallah bara ku tsaya a gidajenku ba ku samu lada!!!kai umma jikokin ki suka tasamu a gaba sai an kawo su wurin ka’ka su amshi happy sallah cewar jummai…aysha tace ai mazajen mu suka ce a kawo su idan sun dawo masallaci mu wuce a bar maku su”rashida ta gaishe su suka ”da fara’a suka amsa”nan aka koma palour a na sabon gaisuwa,yara suka fara tsale saman kushin”umma tace kun gyara gidan ku kunzo ku 6ata nawa kafin mijina ya dawo ko?”’yara suka sheke da dariya”’jummai tace ji palour’n umma kamar na sabuwar amarya sabida tsaruwar shi ga kamshi”murmushi tayi”kuyi ma mazajen ku godia sanuwa suka saya mana na layya..sallama suka ji daga kofar palour.
baba,raji da abdul ne cikin ankon farin shadda da babban riga blue sunsha kyau da alama daga masallaci suka dawo.
Nan aka zauna tare da sabon gaisuwa,yara suka koma wurin baba’yan hamsin hamsin sabbi baba ya raba masu..rashida ta gabatar da abinci ‘suka ci aka sha,bayan komi ya lafa suka masu umma sallama, kowa ya kama hanyar gidan shi’su umma aka bar ma yara’baba yace Allah mai iko yau ni mallam salis d’an koli ne da jikoki har hudu,ga surukai jarumai masu zuciyar yi,umma tace lalai Allah abun Godiya,bamu haifa da yawa ba amma gamu da jikoki ninkin abunda muka haifa,baba yayi murmushi irin nasu na manya dama haka yake’MAHAKUR CI MA WADACI’
a hanyar su jummai na komawa gida ta kalli raji cikin shaukin so’my master’happy sallah’..yayi murmushi ai sai mun isa gida zan amshi happy sallah na,da abunda yafi komi dad’i da muhimmanci a rayuwa ta,kinsan bana gajiya dake kullum sabuwa kike k’ara zama a wuri na’tell me what is the secret?..uhm my master u are the secret”godiya nike.. Allah shine abun godiy daya bani gwarzon miji kamar ka.
suna isa gida yayi horn,gate man ya wangale masu gate,yana parker motar shi ya sungumi matar shi sai bed room nasu……
suhanaka llahuma wa’bihamduka ash’hadu an la’ilaha illah amta astagfiruka wa atubu ilaihi
????????????
[ad_2]