KURUCIYAR JUMMAI Complete Hausa Novel
Sha una all desame,all of una na hausa ube,how it take worry me?
Jummai tace na me be thief?
I will put zakafi for u now now.
Yace idiot,shege banza,dan iska..
Ta fara waqa;
LA la la lala
La lala
Kwadon ubanka ya tsinke
Saura qashi da dan tsoka.
Yara Ku zo Ku sai nama.
La’anane dan wuta
Suka amsa:
Kafuri
Mai futsari a tsaye
Kafuri…
Hasarare
Kafuri….
Abishi da go ra har wuta…
Ya dauki kata ko ya bisu da gudu
Suka sheka..
Jummai tace kuje gida kuyi bacci,mamar wasa ma yau bacci take Ji.
Audu yace jummai a raba madarar mana
Tace wanan kayan ba namu bane
Allawiya tace na wage?
Jummai tace baquwar mu
Gobe rata zo daga kauye, kunga bai yuwuwa ta baro kunnu can, tazo birni taci gaba da shan kunnu,sai ta rai na ma gidan mu da wayyau.
Suka ce ba matsala.
Tun da safe jummai ta share dan madai dai cin gidan su tayi goge goge””duk da ba wani abuna azo a gani ke gare suba.
Wanka tayi,taci kwaliya
Tea tahada mai kauri, ta rufe a cikin jug.
Tace ina ki ka samu kayan tea?
Tace wurin ubale,kuma babu mai sha domin na baquwa ne.
Umma tace abincin sata raki ba baquwar?
Aysha tace wada zata Taso tun daga kebbi state zuwa niger state(minna) aka hadawa tea tun yanzu?
Babu ruwan ki,kuma yau ban zuwa ko ina sai tata iso tasha tea nan.
Aysha tace umma na wuce islamiyya.
Tace a daw lfy.
Yan wasa sunyita sallama ma jummai, amma ta fau taqi fita.
Sai da la’asar fati ta iso, da yake tasan gida kuma babu nisa da tasha, ta karaso da Yar Ghana most go nta kodade.
Jummai najin sallaman ta, ai a guje tayi hanyar zaure, amsar jakar hanunta tayi sannu fati, shigo ciki.
Umma sai murmushi take yi
Zama tayi saman yagagen Leda carpet dake palour su jummai.
Jug din tea ta kaw mata da cup.
Umma dai kwanu mai marfi ta bata””faten tsakin masara ne na manja, yaji sure da kyada””
Jummai ta jaye kwanun gefe, tace bashi ZAKI Ciba dan shi kika bari kauye, ga dai shayi nan.
Ai ko ta kafa kai sai data shanye shayi tas, ta kuma shanye fate.
Jummai tace taf wayaga na kauye a birni.
Aysha ta daw isllamiyya,tace ah su fatin dai, yasu gwaggo?
Tace lfy lau.
Ina tsaraba?
Jummai tayi caraf, yan kauye kika San suna kaw tsaraba ko son banza sun fiki,umma ce dama idan zata ta daukar ma kanta qalulan wahala,ayi tsaraba niqi niqi.
Fati dai na sauraran cin mutunci da ake masu..
Da safe masa umma ta aika aka saya ma fati, jummai tace alambaran sai dai fati tasha tea,dan akwai masa kauye.
Fati kam a dadin ta duka biu ta hada.
Da yan maa jummai taja fati, wai zata zaga da ita taga gari.
Daga gidan su allawiya aka fara
Tace kin gidan babban aminiyata wadda tazo jiya, duk da gidan haya suke, amma dadi suke ci.
Tace uhm.
Tace nan gidan mai bredi ne,kin san yarbawa qazamai ne, katti kee kwabin flour zindir ba riga duk zufan hammatan su na zuba cikin bredi shi yasa kullum yake kwantai yadda masarar umma ke kwantai..
Tace muje layin baya, in banda kwasar daria babu abinda fati keyi.
Gidajen nan uku na masifafun unguwar nan ne,tsofai tsofai dasu; Hajia ibra, hajia mai dawa da Hajia taya haka suke kamar mayyu.
Fati tace tab.
Nan kuma gidan zuriar duwayu kenan,.manyan su a yara duk babban duwayu ke gare su.
Suka sheqe da daria.
Nan kuma gidan yan’aljannah duk unguwar nan babu Wanda ya kai su kirki,basu fada da kowa zattausayi, bayin Allah.
Ga gidan mamar murtala, tsuyaya ce, sai mugun son kudi.
Wai kamar ruwan rijiya mtar nan sayar wa take lokacin rani duk bokiti naira goma,tsinaniyar har da kirari akai mata
Money ya dey
Money ya kam.lol
Fati tace ban jin turanci ai, tace duk kanwar ja ce inji jummai.
Tace nan kuma gidan shehu lalura kenan, duk unguwar nan yafi kowa kiran babu, ga cin bashin tsiya,matan shi kuma badai qazanta ba”kin san halin matan hausa wa musamman sakwatawa”
Yauwa ga islamyyan MU
Azaluman biu ne,mal.Babba da malama hadiza.
Ita mallama hadiza ina mata uzuri sabida bata San zafin haihuwa ba, tunda bata taba haihuwar ba.
Shi kuma Mallam babba ma gemun bunsuru, basamude ne daga Yemen ya gudo nigeria,shine aka danka mai makaranta.
Jifa sukaji na duwatsu ta ko ina…
*L££MA*????
????????????????????????
????????????????????????
*QURUCIYAR JUMMAI*
????????????????????????
????????????????????????
*HALIMATU SADIYA MUHAMMAD*
*L££MA*????
*@AM££NCI WRITERS ASSOCIATION*????✍????
*domin samun littafan mu a Facebook @AM££NCI NOVEL GROUP*
*INA NEMAN AFUWAN KU AKAN JINA DA KUKA YI SHIRU KWANA BIU,I WAS VERY OCCUPIED NE SAI KUN YITA HAKURI DANI YANZU*
*11-12*
Wa zata gani?
Dan lami gwangwanin alala…
Tace MU gudu fati mahukaci ne,zai halaka mu, ai kuwa sheka wa su kai sai gida…
Baba dake zaune bisa tabarma a kofar dakin shi,yace ya ya,lfy kun shigo a guje?
Tace baba dan lami ya biyo MU da jifa.
Umma tace me ya kai Ku har bagadaza.
Tace naje nuna mata gari ne AI.
Tace da ya fashe maku kai taga garin da kyau AI,fati wuce ki huta dama ita bata gajia yawo.
Haka fati tayi hutun ta cikin fari ciki da anashu wa.
Data tashi koma wa sha tara na arziki su umma su kai mata.
Common entrance ya fito.
Jummai ta samu admission a””government technical schl minna””makarantar su Aysha,domin yanzu jss3 take.
School din bai da nisa da gidan su.
Alawiyya ma nan ta samu.
Ranar monday suka fara zuwa,jummai baayi Mata uniform ba,tsohon na Aysha tayi amfani dashi,dan basu da hali.
Alawiyya komi sabo aka yi mata,kuma Baban ta ya kai ta.
Jummai kam ita takai kanta,tana isa an gama Assembly har an fara tsaran latti””prefect””
Fuske wa tayi zata wuce, wani dan ss3 yace ”hey where did think u are going.
Kneel down my Friend.
Murguda baki tayi, tai tafiyar ta.
Class din da aka rubuta jss1A ta shiga, makil yake da students, Layin baya ta zauna sit din da allawiya ke zaune.
Maths teacher ya shigo.
Aka mike
Good morning sir,banda jummai,tace iskan cin banza,primary gud mrng sir, secondary gud mrng sir,aikin wahala.
Yace get sitted..
Let me introduce myself.
Am Muhammad Raji by name””popularly known as M.Raji””, I will be teaching u mathematics.
Ya rubuta topic;-Roman figures
Yace bring out yr writing materials.
Kowa ya fitar da book,calculator and mathematical set,amma banda jummai domin ko book bata dashi.
Baba yace tayi hakuri har second term ta fara zuwa, dan bai da kudi yanzu,tace atafau sai ta fara zuwa.
Ya rubuta example:-Roman figure 1 to 100 ya rubuta, yayi baya sanan yace suyi copying.
Ya fara going round, yana observing student din,jummai ya han go zaune tana faman gyangyadi.
Desk din ta ya buga,firgita tayi,ta mike tsaye.
Yace what’s wrong with u?
Tayi shiru zata zauna.
Yace keep standing.
Why are u not writting?
Tace, takadata na wurin yaya ta.
Yace speak English, u are no more in primary schl.
Where is yr sister?
Tace jss3A
Yace call her for me.
Ya fita sai ajin su Aisha, tace M.Raji na kiran ki.
Sai da gaban ta ya fadi domin duk schl din babu Wanda vai sai halin shi ba.
Suna zuwa, ya tamvayi Aysha ya suke da jummai?
Tace sister tace.
Yace ya sunan ta.
Tace MARYAM SALIS.
JUMMAI tace nima popularly known as JUMMAI.
Yace shut up,who ask u.
Yace Aysha salis she told me that her writting materials are with u?
Tace she did not give me anything sir.
Yace ma jummai why did u lie to me?
Tayi tsuru tsuru dan kuwa karyan ta shirga.