KURUCIYAR JUMMAI Complete Hausa Novel
Tace kai umma walahi ko kudi kinfi baba,sanan ko yar shinkafar nan da miya da yaran kan je makaranta su dawo su iske an dafa,
Babu wanan a gidan MU,daga zazafen tuwo sai yan kame kame.
Umma tace abinda ubanku ya kawo kenan,idan da anbi ta tashi ko kame kame zaku samu…
Ta Mike nidai na tafi ma gidan su Alawiyyah kallon super story.
Da sallama ta shiga, ta iske yaran unguwar abokan wasan ta makil cikin dakin.
Tace me zan gani haka?
Hadda wayan da basa makarantar boko da yan primary sun San kalan super story.
Lalai super story yayi banza.
Ke alawiwi ina mama?
Tace Baku hadu ba,yanzu ta shiga gidan Ku a.
Kenan kina zaune kina kalan yara sun cika daki da warin tsami,ko turanci basa ji?
Alawiyya tace tau ya zanyi duk abokan mune.
Tace yayi, banga laifin ba,ko ke ba turancin kike ji ba.
Oyah duk Ku fita screaning za ayi;- lami,karima da audu Ku zauna,sauran duk waje road.
Suna cikin kalan aka dauke NEPA..
Jummai tace muje bakin titi shagon mai barber yana tadda generator..
Suka ruga a guje, ko da suka isa shagon makil da yarbawa,tace tsinanu,walahi na tsani Yar bawa,shegu kawai…
Ta kutsa can gaba, kodata daga kai angama..
Tace amma Allah ya isa tsakanina da Yar bawa
Da safe da wuri ta isa makaranta domin M.raji keda first period yau.
Su Margret har sun rigata zuwa.
Tace gud mrng friends
Suka amsa mrng dear.
Sai gga M.Raji ya shigo
Suka mike gud mrng sir””muryan jummai yafi na kowa tashi..
Yace mrng how u?
Suka ce fine sir
Yace get sitted.
Ya fara tambayan su abunda yayi last time, jummi ta mike tsam ta bashi amsa dala dala.
Mamaki yayi sosai yadda akayi ta gane, bayan ko zama bata yi ba ranar a class.
During break ne yan ss3 suka shigo sukayi informing nasu akwai””MSS””yau after closing””
Tsaki jummai tayi,tace ko mene MSS kuma oho.
Tace ban tsayawa gida zani.
Jummai kumawa tayi sit din su Alawiyyah domin basu da aiki su kuma yan back sit sai karatun littafan soyaya na hausa.
Tace sannunku su hadiza kawayen Alawiyyah
Suka ce sannu jummai kawar kafurai
jummai tace wai Ku abunda iyayen Ku suka turo kuyi Kenan?
Wai shin ina ma kuke samun littafn nan?
Zaliha tace bashi aka turo MU yiba,amma tunda bamu gane abunda ake koyawa kuma fa,gara mu nemi lahiran mu?
Jummai tace ta INA?
Alawiyya tace cikin littafin mana, yadda ake zaman aure, gyaran jiki,tsafta,yadda zaka zauna da mutane duk akwai ciki, kuma aljannah Mace ai akace tana karkashin kafar mijinta.
Jummai tace lalai alawayyah,ina kuke samun littafan?
Hadixa tace mamata ke karantawa,shine nike sato masu alawiyya su karanta a mayar.
Suna cikin hiran, sai anty Aysha kasim mai””integrated science””ta shigo.
Bayan sun gaishe ta,ta tambaye su Wanda zai iya””differencieting between living things and non living thing”
Wani yaro mai suna mas’ud rilwanu ya bana nashi,
Tace atafa mashi,
Helen ma ta bata nata, haka jemimah
Tace yanzu tafi son amsa daga baya cikin yaran hausawan nan,idan ba haka ba sai tayi punishing nasu.
Duk sukayi tsuru, tsuru, jummai tasan amsan tace walahi tunda aka ci zarafin su bata fadi.
Data Ji shiru,tace Maryam salis I know u know it pls tell us the answer.
Tace shegiya baki kamar I know u know it.da jummai taga embracement din zai yi yawa ta mazze ta bada amsa.
Duk class ya dauki tafi..
Cikin ranta tace nadai bayar ne kawai, amma daga yau nayi alkawari bazan sake amsa was kowa tambaya ba, idan ba M.raji ba.
*tau ko menene dalilin jummai oho*
Da aka tashi, jummai taso guduwa gida amma ina prefect sun tare ko ina dole taje MSS.
Yayar ta Aysha tayi karatun Qur’ani.
M.raji yayi leacture akan muhinmancin Neman ilimi musamman ma na addini.
Jikin jummai da alawiyya duk yayi sanyi.
Jummai cikin ranta tayi alkawarin komawa islamiyya domin nemn lahiran ta.
Sai 3:00pm aka gama MSS,a hanyar dawo wa gida ta fara gunguni””yanzu duk yunwar nan da mutum ya kwaso abin takaici yana komawa gida dumamen tuwon jiya zai iske””taja doguwar tsaki.
Da dare taje wurin gashin masarar Aysha tayata hira.
Sai ga wasu samari uku, wayanda kullum sai sun zo sayan masarar.
Sukace amma Aysha wanan yayar kice ko?
Tayi murmushi kanwata dai dan kunga ta fini jikin girma.
Daya yace gaskia ina son kaunan nan tamu da zaki bani ita.
Jummai ta juyo da niyar yin rashin kunya, taga gayen ya mata kwarjini da yawa.
Tace ya sunan ka;yace NURA
Kefa tace; JUMMAI
Bello yace jummai ai ba suna bane
Aysha tace Maryam sunan ta.
Muhammad dai na kalan su.
Nura ya kashe murya kina sona Maryam?
*L££MA*????
[14/01, 21:56] +234 812 140 7930: ????????????????????????
????????????????????????
*QURUCIYAR JUMMAI*
????????????????????????
????????????????????????
*HALIMATU SADIYA MUHAMMAD*
*L££MA*????
*@AM££NCI WRITER’S ASSOCIATION*????✍????
*domin samun kayayatun littafan mu a shafin fcbk a neme MU a:-AMEENCI WRITER’S NOVELS GROUP*
*17-18*
Tace soyaya,tab in ban han mene haka ba,kuma ban taba yi ba.
Yace zan koya miki idan kin amince.
Tace tau ya sunan ka?
Yace muhammadu nura.
Ya sunan mamaka?
Hajia
Halan taje makka?
Yace eh
Baban ka fa?
Yace ya Rasu.
Tace eyah,sannu.
Yace nagode.
Tau kana da kudi,kuna da TV,sanan kuna cin kayan dad?
Yace muna da rufin asiri dai””na gama university ban samu aiki ba,amma inada shagon dunki,muna da TV hadda DVD,sanan abinci Ko wane iri Hajia na dafa wa.
Tace Ashe zan kama zuwa kallo gidan Hajia,sanan zan dinga zuwa duk ranar da kukayi shinkafa in CI.
Yace badai kina sona ba?
Tace oho,nidai kayan dadi nike so.
Yace wane schl kike?
Tace nan bayan PZ,makarantar mugun nan da garda wan maza wai prefect.
Ya kyalkyale da daria.
Yace ajin ki NASA?
Jss1A
Yace so serious, yaushe za muyi aure?
Tace wanan sai su Aysha, ni kam ba yar iska bace.
Yace yayi kyau,zani gida sai gobe
Tace ka kawo min kayan Dadi.
Yace bye take care of yrself for me.
Ta ruufe ido.
Ranar Saturday tunda safe ta shirya ta dauki jakar islamiyyan ta
Tace baba na wuce makaranta.
Umma tace karyan banza, a fake da zuwa islamiyya aje gantali.
Tace walahi islamiyya zani.
Baba yace kyaleta mamata,Allah bada sa’a,a dawo lfy.
Tana isa, mallama HADIZA tace sai yau, ko Jan fada kika zo yi?
Tayi banza ta wuce ajinsu na da.
Mallam babba me ciki, yace daga ina zuwa ina?ko batan hanya kika yi?
Tace ni dai makaranta na dawo kuma saboda Allah.
Yace kin kyauta, amma ba ajin nan ba kuma ajin yara.
Tace tab din,da girma na,ina secondary, in zau na da yan aji daya,wayan nan jariran yaran,aji biu na zan zauna gaskia Mallam.
Yanzu ki bada karatun da aka koya maku na aji daya idan kin iya sai ki zauna aji biu.
Dala dala ta bashi baya ni
Yace masha Allahu barakallah,shiga ki zauna.
Ban da Jan Dada,banda zuwa latti ko fashin zuwa.Allah taimaka
Amin tace,ta shiga ajin,tsit sukay Dan sun San halin jummai sarai.
Da aka tashi ta hadu da NURA
Yace Baby va gaisuwa?
Tace daga ina kake?
Yace shago yanzu gida zani.
Tace mu koma shagon in gani, sai MU wuce gida.
Yace ahhh
Ba gidan Hajia ba, dakina zani
Tace sai me muje kawai.
Yace MU he,shago ne madai daici,keken dunki biu,na designe guda, yaran shagon biu.
Yace kin ga shago na?
Tace eh yayi kyau.
Gidan a bakin titi yake dan madaidaici, dakin nura ne farko da an shiga, sai rum and palour da toilet,a kofar daki take girki.
Yace sannu da aiki Hajia
Tace yauwa, ina ka samo yarinya?