KURUCIYAR JUMMAI Complete Hausa Novel
Mutuwar tsaya m.raji yayi.
Mal.Ahmad yace fadi tsakanin ki da Allah allawiya haka ne.
Tace tabbas anyi haka mal.,hada cewa yayi sirri ne kada a bari kowa ya sani.
Yace haka ne mal.raji.
Ya rasa abin cewa dan imani ya cika shi.
Tace tun ranar dana fara zuwa makaranar nan ya matsa min yana sonna, ai su Margret ne shaida.
Ta fidda book dinta da sauran text buk tace kaga .a abunda yake rubutamin duk ya amshi buk dina””M.raji love Maryam salis””.
Mallamai nata passing suna gani, abun mamaki kuma handwriting nashi ne.
Aka tambayi su Helen, suka bada tabbacin jummai keda gaskia.
Akace ko yana da abin cewa?
Yayi shiru, dan yace Allah dai zai fidda shi, dan cikin gallery akwai pics nashi ga kuma number shi ciki.
Aka cema su jummai kuwa, tazo da babanta gobe akwai meeting da teachers.
Jummai suka fita,tace masu kada wadda tazo da ubanta gobe zata wanke su ko da magana ya tashi.
Suka amsa, sudai sun tausaya mashi dan yanzu tsoro jummai ke basu.
Tace nasan kan ku ya kille da lamari na,sai an gama case din zan warware maku komi.
M.raji kam fargaba yake dan yasan bai da mafita, either ace ya aje aiki Ko ayi masa transfer, daman hukuncin kenan.
Aysha CE tajawo junmai tace wane iron rashin imani kenan da rashin tsoron Allah, wanan qazafi har ina?
Tur da mugun hali irin nakyi, dan wanan ya wuce QURUCIYA,sai rashin imani da mugun zuciya ace mutum ya hukunta ka akan laifin da ka aikata ba daidai ba kace sai ka rama, mallamin ka for that matter? Allah ganar dake gaskia,amma bazan bari kiyi succeeding ba.
Jummai tace dallah mallama dakata, bata fin karfina kikay ba,kuma ba tsoron ki nike jiba,anyi mashi sharrin ahi waye, nida ya Kama ya dirka kamar jakar gidan ubansa ba haihuwata akayi ba,cikin bainar jama’a ya kunyata ni,ya cimin mutunci hadda fadin dan ubana sai na bar makaranta,shi tunda ba ubansa keda makarantar ba ai yanzu dole ya bar ta.
Kazafi kuma walahi wayan nan ta ceceshi,nai mashi mai sauki dan va abunda na yi niyyar laka mashi kenan ba,sai gashi ya amshi waya abun yazo min a sawake.
Walahi idan bakyi cire bakin ki cikin maganan ba,zan manta mun hada jini dake MU samu matsala. Dan kunne yaji jiki ya tsira.
Shi kuma NURA sai ya fadamin hadin shi da M.Rajiiiiiiiiii
*L££MA*????✍????
[17/01, 02:14] +234 812 140 7930: ????????????????????????
????????????????????????
*QURUCIYAR JUMMAI*
????????????????????????
????????????????????????
*HALIMATU SADIYA MUHAMMAD*
*L££MA*????
*@AM££NCI WRITER’S ASSOCIATION*????✍????
*domin samun kayatatun littafan mu a shafukan fcbk tuntube:-AM££NCI WRITERS NOVEL’S GROUP*
*GODIA GARE KU MARA ADADI MASOYA LITTAFIN QURUCIYAR JUMMAI WA YAN DA NA SANI,DA WA YAN DA BAN SANI BA.ALLAH BAR KAUNA DA AMINCI*
*21-22*
Da suka dawo gida ,Aysha taso fada masu umma abinda jummai ta aikata, sai tayi tunanen ai tunda ance su zo da iyayen su idan baba ya je zai ji.
Jummai gidan hajia taje,hajia tace ya makaranta.
Tace lfy lau.
Tace hajia ina nura?
Tace ya tafi kauye kuta rasuwa akai mana, sai gobe zai dawo.
Tace ba matsala,zani gida.
Tace gashi yau ban dafa komi ba.
Tace nagode hajia.
Ki gaida su umman ki.
Tau tace ta wuce.
Da yamma sun je islamiyya,taje biya karatu wurin mallama hadiza.
Tace Mara kunya, kin min tsaye saman kai,, bara ki duqa yadda sauran yan uwan ki sukai ba.
Tace kai na ke ciwo, bari har biyawa yakai kaina zan duka.
Tace tatatar Mara kunya ai sai in ba keba, sai kin bada amsa,idan bakyi dukawa ki tafi bazan biya ba.
Jummai ta juya shike nan ai.
Finciko hijabin ta mallama hadiza tayi, tace dawo nan bara mutunci, maimaita abinda kika fadi.
Tace ban fadi tunda ba zagin ki nay ba.
Tace Iliya miqo min bulalar nan.
Jummai tace duk kika bugeni zan rama, na fada makyi banda lfy, sanan ba zagin ki nayi ba.
Caula mata bulalar tayi.
Ta rike da Sauri,kada ki sake.
Ta hizge zata sake bugunta, jummai ta ware ta wanke mata fuska da mari mai lafia.
Ta dafe kuncyi LA LA laaa kika mare ni,
Anas, kabiru, Iliya Ku kamo min ita..
Haba kafa mai naci ban baka ba sai gidan Hajia da yake yafi kusa da Islamiyyar.
Ganin mutum Hajia tayi cikin daki sai haqi take yi.
Tace lafia,waya biyo ki.
Taba hajia lbr.
Hajia tace haba jummai, kina girma kina kara shiriricewa,mallamar kice fa, duk abunda tai maki bai kamata ki rama ba,ke kenan babu mai makyi shaidar kwarai?
A haka kike son nura ya aure ki,yanzu fa ko mutuwa kikai ba mai makyi shaidar kwarai.
Tace haba hajia, kenan ko kai keda gaskia sai a tauye ka.
Tace ta ya zaa bakyi gaskia bayan ba ai makyi shaidar kwarai ba.
Idan kina so MU shirya, kuma kina son auren NURA ki koma ki bada hakuri.
Tace walahi bazan bada hakuri ba, kuma nabar islamiyyar nan har abada, NURA kuma ai dama ba sonshi nike yi ba.
Sai Anjima.
Ta wuce fuuuuuu.
Hajia tace Allah shirye ki, dama ai kallan nuran nakye, ina zai kai Mara kunya irin wanan yarinya.
Washe gari, da wuce taje makaranta, tace masu marget ko an tambayi iyayensu suce basu gari duk sunyi tafia,alawiyya tace riqonta ake ba iyayenta bane, ita kuma zata ce babanta yace bai zuwa.
Haka kuwa akai, bayan dogon bincike a cikin wayan da kuma shaidun karya irin su alawiyya, da kuma yadda M.raji yayi shiru, shi bai karyata zancen ba, kuma bai gasgata ba””dan a ganinsa ko teachers yan uwansa sun isa bada shaidan kwarai a kansa,amma suka rufe idanu, suka gasgata zancen yara kamar su jummai.
Management ta rubuta letter aka aika ministry duk abunda ta yanke dai dai ne, sanan an dakatar dashi tukum till fortheer notice.
Principal, mallamai da dalibai sunyi bakin cikin rashin mallami mai kwazo da hazaka kamar M.Raji
Hatta su Margret sai da suka tausaya mashi, tare dayin dana sani.
Ita kam uwar gayya ko a jikinta.
Ranar MSS hadda waazi akai akan M.raji wai yana Neman bata tarbiyar dalibai…
Aysha tayi takaicin hada jini da jummai, yanzu ace kamar jummai Yar shekara goma sha biu tasan ta hada makirci,tuggu da qazafi har a dakatar da mutum a kan aikin sa.
Da umma taji lbr ranta ya baci matuka haka baba, amma ba yadda suka Iya da jummai sai adu’a.
*PLS KUYI HAKURI DA WANAN BAN JIN DADIN JIKI NA NE*
[22/01, 00:56] +234 812 140 7930: ????????????????????????
????????????????????????
*QURUCIYAR JUMMAI*
????????????????????????
????????????????????????
*HALIMATU SADIYA MUHAMMAD*
*L££MA*????
*@AM££NCI WRITER’S ASSOCIATION*????
*domin samun qayatattun littafan mu a shafukan fcbk a tuntube mu @AM££NCI WRITER’S NOVEL GROUP*????✍????
*23-24*
Ranar friday a assembly principal ta sanar dasu anyi M.raji transfer, sanan tayi Kira ga masu hali irin nasa su gyara..
Aka watse assembly kowa na alhinin rashin jarumi,gwarzon mallami irin Muhammad raji.
Haka sukaci gaba da karatu cikin fahimta da natsuwa.
Jummai bata da aiki yanzu sai karatun littafan Hausa na soyaya, kawayen allawiya ke dauko mata da yake tana da saurin karatu tana iya kare 1 & 2 kafin a tashi schl,taje da saura gida tana kai har 2::00am na dare tana karatun novel, amma duk da haka bai hanata mai da hankali kan karatun taba, duk test da assignment da ake basu yana kokari sosai, yanzu shirye shiryen exams suke saboda azumi ya gabato.
Aysha ma baa barta a baya ba,dumin tana da hazaka itama,yanzu shirin Junior leaving suke yi.