NIDA AMARYATA 17-18

1⃣7⃣_1⃣8⃣
_Alhamdillah! nagodewa Allah Daya Kara bani ikon numfashi,tare da yalwatacciyar lfy,Ina dada godiya gareshi Daya Kara bani ikon kara rubutu a rayuwata,Ina matukar godiya gareku masoyana masu amana,NI DA AMARYATA GROUP 1and 2 Ina godiya bisa ga addu’arku gareni nagode nagode Allah yakara zumunci._
_________________________
Kusan sati biyu da haduwar su a asibiti,Sam ta ma Manta da card din Daya Bata,Wanda yakamata ace tun wuri ta kirashi tayi Masa godiya.tunawa tayi da Sam Bata kyauta ba Dan haka ta tashi ta dauko wayarta,inda ta kunna ta, kasancewar dama bawani kiranta akeyi ba shiyasa take kasheta.koda ta duba balance ba kudi a ciki nera Daya ce,Bata koyi tunanin sa Kati ba ta tabbatar da cewa wannan kudin na ciki zaiyi Mata flashing,Dan haka ta dauko katin tare da kwafar nombar ta shigar cikin wayar.batare da Jin ko dar ba ta Danna flashing,irin Wanda ake Kira da kar a kamani,ringing Daya ta kashe,ta tsaya jiran Kiran Amma shuru,haka ta dinga Danna flashing ba ji ba gani,Wanda shi Kuma duk flashing din da takeyi bema San tanayi ba,Dan yasa wayar tasa a silent ne.
Saida yagama abinda yakeyi sannan ya duba wayar,aikuwa yaga missed call kusan goma Kuma da bakuwar number.cike da mamaki yake bin wayar da kallo,Dan haka ya shiga kokarin Kiran number.
Tana zaune tana gogewa Amina baki wannan lokacin taji ‘yar kwaribar ta na tsuwa alamar ana Kira,Saida ta kammala sannan ta mike ta nufi inda ta ajiye wayar,Nan ta taga number Alhaji kabeer ce.cike da nutsuwa ta dauka tare da sallama,”Assalamualaikum,”
“Ameen Alaikissalam,ya amsa mata,Nan ta shiga gaisheshi,ya amsa Mata cikin rashin gane kowacece.Sai zuwa can sannan ya tambayi me maganar,Nan ta shiga sanar dashi wacece ita.Sosai yaji farin cikin Kiran datayi mishi,inda bayan sun sake sabuwar gaisuwa Nan yake tambayar ta me jiki? Amsa Masa tayi “da sauki”inda Nan yake fada Mata Yana uzuri Amma tayi mishi kwatancen inda suke zaizo akwai maganar dayake so suyi, kwatance tayi mishi,sannan ta Kara mishi godiya,Nan ta katse wayar cike da tunanin maganar meye zai kawo shi Kuma,ganin batada amsar tambayar yasata yin shuru taci gaba da sabgar ta.
************************
Tunda yafara wa Aunty Hama maganar take mishi kallon marar hankali,Amma Sam Bata katseshi ba har Saida yakai aya.
Ganin tayi shuru yasata dagowa ya kalleta sai gani yayi tana kallonshi ta tsare shi da ido.murmushi yayi tare da fadin” Ina magana kinyi shuru”!
“Ai dole inyi shuru,domin al’amarin da kazo dashi ya girmi tunanina,taya kake tunanin zanyiwa Nihila aure yanzu,kada kaga jikinta haka,ba fa komai bane domin yanzu take shekara Sha uku inaga,Dan haka bawan Allah na rokeka Dan girman Allah kabar ma wannan maganar,domin Wallahi hankali ma bazai dauka ba”,Nan fa ta shiga masifa.
“To fa! Banda abinki Hajiya nifa bance dole ba,domin wannan abin taimakon ku nake son yi,bawai Dan son Raina bane,ki duba jikin baiwar Allah nan,abar a tausayawa ce,in kina ganin kankantar ta ai kin San dabarun ku na Mata da Zaki Mata,nasan halin abokina baya taimako Dan Allah,sai dai fa muddin tana gidan to zaku iya samun mafitar abinda zaku taimaki wannan baiwar Allar.wallahi da inada abinda Zan taimakeku Wallahi danayi,to arziki na Bai Kai Nan ba,amma kiyi shawara duk abinda Kika yanke Kya sanar Dani idan na dawo”.haka yayi Mata sallama ya tafi ya barta da tunani kala-kala.
Sosai ya barta da tunanin,inda ta mayar da hankalinta ga Nihila dake kwance tana sharar barci,kwallar data kwaranyo mata ta share,tabbas tana cikin tsaka me wuya,bazai taba yiyuwa ba saboda wani dalili kawai ta jefa yarinyar mutane cikin halaka.Kwana tayi tana tufka da warwara,inda abin kamar magani,tun ranar da sukayi maganar jikin Amina ya Kara rikecewa,kullum haka suke fama,cike da rashin mafita ta dinga kallon Ahlin nata,Wanda daga karshe ta amince da abinda zuciyarta ta yanke kawai.Ta Kira Alhaji kabeer ta sanar mishi,inda yazo suka tattauna bawata walwala.Tun daga wannan lokacin ya shiga Kai gwauro da Mari Yana taimaka musu,yayin da Aunty Hama bisa dole ta shiga koyawa Nihila wasu abubuwan.Tun da Alhaji sani yaga hoton Nihila ya rude,Wanda Saida aka kaita gidan hoto aka dauka aka dada taceshi,Dan haka ya Kara rikicewa,barin kudi ya shiga yi musu,yayin da inya bayar sai dai Aunty Hama ta adana,inya Kira waya,Aunty Hama ke make murya taita zuba Masa kalamai,Bai samu zarafin dawowa ba har sai lokacin bikin,Wanda ranar kamu ranar yafara ganin Nihila,Nan yakara rikidewa,Dan ganin tsantsar kyanta,Koda ya Kira wayar yace Yana son ganinta Dan su gaisa, Aunty Hama tace ai ta gaji bacci takeji,Bai wani damu ba Dan yasan nesa ta zo kusa.
_wannan shine dalilin auren Alhaji Sani da Nihila_
*_Back to story_*
Hannunta ya kamo ya shiga murzawa,yayin Daya kafeta da ido,sosai yakejin soyayyarta har cikin zuciyarshi,Dan haka ya Kara damke hannunta da Dan karfi,aikuwa saita saki Kara tare da fadin “wayyo Allah na”!
Da sauri ya shiga tambayar ta meya faru? Ga mamakinsa ganin kwalla yaga tana zubuwo a idanunta.cikin tashin hankali ya shiga tambayar ta meya sameta?
Bata bashi amsa ba sai kawai ta fashe da kuka.”Kinga yi hakuri fadamin meke damunki? Bana son rigima fadamin kinji!
Zumbura Baki tayi gaba tare da fadin “NI gida nake son zuwa ” ta karasa maganar kwalla na dada zubowa.
“Gida Kuma, ya maimaita kalmar.kai ta daga alamar eh!
“Haba ke kuwa yaushe duka Kika bar gidan da har zakice Zaki koma? Kina ji….Bai karasa ba yaga ta kwace hannunta tare da Fara birgima a kasa,Wanda hakan yayi dai-dai da shigowar Hajiya,wadda tazo sanar dashi su Alhaji kabeer zasu tafi suna jiranshi.Aikuwa Nan idonta ya sauka akan Alhaji dayaketa kokarin riko Nihila tana zamewa tare da Kara sautin kuka.
Bakin ciki yasa Hajiyar juyawa batare da ko shi Alhajin yasan da zuwanta ba.tana sauka ta sanar ta dasu cewar Yana wanka,aikuwa Nan suka mike da bazasu tsaya jiransa ba.nan sukawa Hajiya sallama suka tafi ita Kuma ta shige bangaren ta cike da tunanin abinda ta gani .
Shikuwa Alhaji da kyar ya rarrashi Nihila tare da Mata alkawarin zai kaita gobe,amma ta tashi ta shirya yakaita ya siyo Mata ice cream.make kafada tayi tare da fadin” nidai bana son abinda kace sai dai Inka yarda zaka siyamin gyadar gidan Alawiyya da kuli-kuli……
_ku Kara hakuri,ku Kuma tuna da girman alkawari,ki sani in Kika biye ta batun mutane wlh zasu kaiki su baroki,hakki koya yake yanada wahalar dauka,tunda kin amince kin biya danki karanta kisani kin dauki Amana,muyiwa juna adalci,Ina alfahari daku masoya amaryar Alhaji sani._
*Alkalamin khady* ✍